Gamayyar Malaman Musulunci sama da 1,000 sun gudanar da taron nuna rashin goyon bayansu ga yadda gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da ƙasar.
Arewa Updates ta rawaito cewa, Malam Kabir Bashir Abdulhamid ne ya gabatar da jawabin bayan taron a madadin malaman, yayin taron da ƙungiyar Ko Da Naka ta shirya a birnin Kano tare da haɗin gwiwar AFAQ Educational Foundation a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.
Takardar bayan taron ta ce mahalarta sun nuna rashin amincewa da manufofin tattalin arziki da suka haɗa da janye tallafin man fetur, sauya tsarin canjin Naira, ƙarin kuɗin wutar lantarki da sauye-sauyen haraji, waɗanda suka ce sun ƙara wa jama’a wahalar rayuwa.
Sun kuma nuna damuwa kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro, musamman a Arewa maso Yamma.
Mahalarta sun kuma nuna damuwa kan ficewar likitoci, malamai, injiniyoyi da sauran ƙwararrun ’yan Najeriya zuwa ƙasashen waje, inda suka danganta hakan da rashin aikin yi, ƙarancin kayan aiki, yanayin aiki da matsin tattalin arziki, tare da buƙatar gwamnati ta inganta albashi da yanayin aiki.
A matsayarsu kan zaɓen 2027, mahalarta taron sun ce bai dace a sake zaɓen gwamnatin ba idan ba ta sauya manufofin tattalin arzikin da suka soka ba, tare da kira ga malaman addini su faɗa wa masu mulki gaskiya, sannan ’yan Najeriya su tantance ’yan takara bisa ƙwarewa, gaskiya, cancanta da manufofinsu.






