Gwamnatin jihar Sakkwato ta amince da za ta sayi babura 1000 kan kudi naira biliyan 1,759,250 domin rabawa hukumomin tsaro a jiha wani yunƙuri na ganin an yaƙi ‘yan bindigar daji.
Majalisa zartawa ta jiha zamanta karo na shidda a shekarar 2026 ne ta aminta da sayen babura ƙirara Bajaj guda 1000 domin cike giɓin da ake iya samu bayan motocin yaƙi 62 da aka sawo da kudinsu yakai biliyan 27 da aka rabawa jami’an tsaro domin yaƙar ‘yan baindiga a yankin da suke addabar mutane.
A bayanin da yake ƙasa kowane babur Gwamnati za ta saye shi kan kuɗi miliyan 1,759.25.Haka ma Majalisar ta amince da gyara makarantar gwamnati ta fasaha dake unguwar Runjin Sambo kan kuɗi miliyan N723,171,671.23, da makarantar kurame ta AA Raji N498,995,000, sai gyara kwalejin koyon aikin jinya ta jiha mataki na farko N489,319,380, za a kuma gyara wurin kwanan mata da maza na kwalejin gyaran jarabawar sikandare ta jiha N229,363,455.Gwamnati ta aminta da sayo kayan koyarwa a cibiyoyin koyon sana’a na mata guda 46 a ƙananan hukumomi 23 na jiha kan kuɗi N93,880,000.





