Home Daga Marubutanmu ME YA SA WASU IYAYE SUKE NUNA BAMBANCI TSAKANIN ‘YA’YANSU?

ME YA SA WASU IYAYE SUKE NUNA BAMBANCI TSAKANIN ‘YA’YANSU?

8
0

ME YA SA WASU IYAYE SUKE NUNA BAMBANCI TSAKANIN ‘YA’YANSU?

Iyaye suna da matsayi mai girma wajen gina tarbiyya, tunani da halayen ‘ya’yansu. Amma abin takaici, a wasu gidaje ana samun iyayen da suke nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu, ta hanyar fifita wani a kan wani, ko ba wa wani kulawa da gata fiye da sauran ‘ya’yan.

Wasu iyaye suna fifita ɗan da ya fi biyayya, wasu kuma wanda ya fi samun nasara a karatu ko sana’a. Akwai kuma waɗanda suke nuna ƙauna da kulawa ga ɗan da ya fi kawo musu kuɗi, yayin da suke wulaƙanta ko nuna halin ko-in-kula ga wanda ba shi da wannan damar.

Amma shin iyaye sun taɓa tunanin irin illar da wannan hali yake haifarwa a zukatan ‘ya’yansu?

Yaron da yake ganin ana fifita ɗan’uwansa a kansa zai iya fara jin kamar ba a ƙaunarsa, ba shi da amfani ko kuma ba shi da wani matsayi a cikin iyalinsa. Wannan na iya haifar da kishi, ƙiyayya, rashin yarda da kai da kuma rashin kyakkyawar alaƙa tsakanin ‘yan’uwa.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, wani lokaci iyaye ba sa fahimtar cewa suna haifar da gaba tsakanin ‘ya’yansu ne da hannuwansu. Yau za su fifita wani, gobe kuma su yi mamakin dalilin da ya sa ‘ya’yansu ba sa zaman lafiya da juna.

Ya kamata iyaye su fahimci cewa kowanne ɗa yana da irin baiwarsa, halinsa da ƙwarewarsa. Ba dole ba ne duk ‘ya’ya su kasance iri ɗaya kafin a nuna musu ƙauna da kulawa.

Idan ɗanka ya fi wani wayo, ba yana nufin ɗayan ba shi da amfani ba ne. Idan wani ya fi kawo maka kuɗi, ba yana nufin shi ne ya fi cancantar kulawa ba. Idan kuma wani ya fi biyayya, hakan bai kamata ya zama dalilin wulaƙanta sauran ba.

Ƙaunar iyaye bai kamata ta zama gasa tsakanin ‘ya’ya ba.

Iyaye su tuna cewa duk wani bambanci da suke nunawa a lokacin yarinta na iya zama abin tunawa da raɗaɗi a zukatan ‘ya’yansu har zuwa lokacin da za su girma.

A wannan gaɓar; ina kira ga iyaye da su yi ƙoƙarin yin adalci tsakanin ‘ya’yansu, su guji kwatanta su, su guji nuna wa wani cewa shi ne abin so fiye da sauran.

Domin ba dukiyar da za ka bar wa ‘ya’yanka ce za ta fi muhimmanci ba, zaman lafiya, soyayya da haɗin kan da ka gina a tsakaninsu ma babban gado ne.

Tambaya ga iyaye: Shin kun taɓa tunanin cewa yadda kuke mu’amala da ‘ya’yanku a yau na iya shafar dangantakarsu da juna a nan gaba?

#Managarciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here