Mutane biyu sun rasu, yayin da wasu mutane 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a hanyarsu ta zuwa halartar taron yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da aka yi a birnin Maiduguri na Jihar Borno.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Mai Bai wa Gwamnan Jihar Borno Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Dauda Iliya, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kan hanyar Biu zuwa Damaturu, inda Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya miƙa ta’aziyya ga al’ummar Biu da iyalan mamatan, tare da yi wa waɗanda suka jikkata addu’ar samun sauƙi.
Gwamnan ya kuma jajanta wa al’ummar Damboa sakamakon wani lamari da ya faru a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, sai dai sanarwar ba ta fayyace adadin mutanen da lamarin ya shafa ba.
Sakamakon aukuwar lamuran biyu, gwamnan ya bayar da umarnin ɗage taron yaƙin neman zaɓen APC na yankin kudancin Borno, wanda aka shirya gudanarwa a ranar Asabar, 28 ga Nuwamba, zuwa ranar Laraba, 2 ga Disamba, 2026.