Home Labarai Kotu ta bada belin Sowore kan Naira miliyan 200 da wasu sharuɗɗa...

Kotu ta bada belin Sowore kan Naira miliyan 200 da wasu sharuɗɗa biyu masu tsauri

13
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC Omoyele Sowore, kan kuɗin Naira miliyan 200.

Mai shari’a Mohammed Umar ya yanke hukuncin cewa dole ne Sowore ya gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa. Daya daga cikinsu ya kasance sarkin gargajiya daga al’ummarsa, yayin da ɗayan kuma zai mallaki kadara a Abuja.

Kotun ta kuma umarci cewa masu tsaya masa su kasance sun samu tantancewa daga masu gabatar da ƙara.

Haka kuma, kotun ta umurci Sowore da ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiya ƙasashen waje ga mataimakin babban magatakardar kotun.

Sai dai kotun ta ce zai ci gaba da zama a tsare har sai ya cika dukkan sharuɗɗan belin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here