Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce ba zai janye daga takarar shugaban ƙasa ba, duk da hukuncin kotu na baya-bayan nan da ya shafi shugabancin jam’iyyar.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Jumma’a, inda ya ce babu wata dabara ko matsin lamba da za ta iya hana shi fitowa takara ko hana ’yan Najeriya zaɓen wanda suke so.
Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da hanyoyi daban-daban wajen raunana ’yan adawa, ciki har da matsin lambar siyasa da kuma amfani da kotuna, yana mai cewa hakan na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam’iyya ɗaya.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan cire tallafin man fetur ba tare da wani shiri na kare al’umma ba, da kuma tabarbarewar darajar Naira, tashin farashin abinci da ƙaruwar matsalolin tsaro.
Atiku ya ce waɗannan matsaloli sun jefa ’yan Najeriya cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu, su kasance cikin haɗin kai, kuma kada su karaya.
Ya jaddada cewa zai ci gaba da takararsa, yana mai cewa jam’iyyarsa za ta kasance a takardar zaɓe, kuma ba zai bari barazana, cin zarafi ko hukuncin kotu su hana shi ba.
Atiku ya kuma ce Najeriya mallakin dukkan ’yan ƙasa ne, don haka dole ne a kare dimokuraɗiyyar ƙasar daga duk wani yunƙuri na mayar da ita tsarin jam’iyya ɗaya.
A ƙarshe, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba zai yi amfani da kotuna wajen kauce wa hukuncin da ’yan Najeriya za su yanke masa a zaɓe ba.
