Ɗan takarar shugabancin Nijeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana adadin ’yan Nijeriya da gwamnatinsa ta fitar daga kangin talauci tun bayan hawanta mulki.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Obi ya kuma ƙalubalanci shugaban ƙasar da ya bayyana yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da aka mayar da su makarantu, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da gwamnatinsa ta gina masu cikakken aiki.