Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC ya hana ministoci da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa halartar tarukan yaƙin neman zaɓe a jihohin da ba nasu na asali ba.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin takardar umarnin da Babban Daraktan Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, ya sanya wa hannu a ranar Talata, 3 ga Nuwamba, 2026.
Takardar ta ce ministoci da sauran masu muƙaman siyasa za su mayar da hankali kan neman goyon bayan jama’a a rumfunan zaɓe, mazabu da ƙananan hukumomin jihohinsu, yayin da mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen su ma za su halarci tarukan jihohinsu kawai.
Kwamitin ya kuma umarci mambobin Kwamitin Gudanarwar na ƙasa APC su mayar da hankali kan ayyukan jam’iyya a jihohi da shiyyoyinsu, amma ya ware Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Sakatare, Shugabar Mata ta Ƙasa, Shugaban Matasa na Ƙasa da Sakataren Tsare-tsare na Ƙasa daga wannan ƙa’ida.
Takardar ta ƙara da cewa, sassan kwamitin da ba su da takamaiman aiki a tarukan za su ci gaba da gudanar da ayyukansu, tare da umartar daraktoci su sanar da jami’ansu sabbin ƙa’idojin domin tabbatar da bin su.
