Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alkawarin soke tsarin biyan kuɗin wutar lantarki na rukuni biyar da ake amfani da shi a Najeriya, tare da maye gurbinsa da tsarin da zai kasance mai sauƙi, gaskiya da sauƙin biya.
Atiku ya kuma zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da gaza cika alkawarin samar da wutar lantarki a kai a kai da kuma kawo ƙarshen cajin kuɗin lantarki bisa ƙiyasi.
A cikin wata sanarwa da kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar ranar Lahadi, Atiku ya ce har yanzu ‘yan Najeriya na biyan kuɗin wutar lantarki duk da rashin samun ingantaccen lantarki.
Ya bayyana cewa zai yi aiki tare da gwamnatocin jihohi da hukumomin da abin ya shafa domin samar da sabon tsarin da zai kare masu amfani da wutar lantarki tare da ɗora wa kamfanonin rarraba wuta alhakin ingancin ayyukan su.
Atiku ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan mayar da hankali wajen biyan tsoffin basussukan kamfanonin samar da wuta maimakon gina sabbin cibiyoyin samar da lantarki.
Sai dai gwamnatin APC ta kare ayyukan da ta gudanar a ɓangaren wutar lantarki, ciki har da dokar samar da lantarki ta 2023, shirin samar da mitoci da kuma shirin biyan basussukan kamfanonin samar da wuta.





