Jam’iyyar ADC ta tabbatar da cewa za ta gudanar da gangamin fara yakin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar Sokoto ranar Laraba, 4 ga watan Nuwamba, 2026, duk da zargin barazana da ƙoƙarin hana ta gudanar da harkokinta na siyasa.
Daraktan yaƙin neman zaɓen gwamnan jam’iyyar a jihar, Bello Goronyo, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a sakatariyar jam’iyyar da ke Sokoto.
Jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar Sokoto da matsa wa masu otal lamba domin su soke ajiyar dakunan da aka yi wa wakilai da magoya bayanta.
A cewar ADC, wasu otal na gwamnati sun ƙi karɓar baƙi, yayin da aka yi barazanar rushe gine-ginen masu otal masu zaman kansu idan ba su soke ajiyar ba. Sai dai gwamnatin jihar ta musanta zargin, tana mai cewa ba ta bayar da irin wannan umarni ba.
ADC ta kuma zargi jami’an wasu hukumomin tsaro na jihar da hannu a hare-haren da aka kai wa mambobinta, ciki har da wanda ake zargin an kai wa ɗan takararta na gwamna, Manir Dan’iya, a filin jirgin saman Sultan Abubakar III ranar 30 ga Oktoba.



