Hukumar zaɓen Nijeriya (INEC) ta tabbatar cewa ba za a sake samun jinkirin kai kayayyakin zaɓe da aka fuskanta a zaɓukan baya ba a babban zaɓen 2027, tare da gargaɗin cewa duk wanda ya yi barazana ko ya kai hari ga ma’aikatan hukumar zai fuskanci hukuncin doka.
Arise News ta rawaito cewa Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin rangadi shirye-shiryen zaɓe a yankin Kudu maso Kudu, wanda ya kai shi jihar Rivers, inda ya kuma sanar da rage adadin masu zaɓe da ake buƙata kafin a tura ƙarin na’urorin BVAS daga 1,250 zuwa 850 a kowace rumfar zaɓe.






