Home Rahoto Uban Kasar Gwandu ya rasu a jihar Kebbi 

Uban Kasar Gwandu ya rasu a jihar Kebbi 

15
0

Uban kasar garin  Gwandu dake cikin qaramar hukumar Gwandu a jihar Kebbi Alhaji Muhammadu Rasheed da aka fi sani da Sarkin Gabas ya rasu yana da shekara 61.

Sakataren yaxa labarai na Gwamnan Kebbi Ahmad Idris ne ya tabbatar da mutuwar ga manema labarai a Kebbi.

Ya ce basaraken ya rasu a ranar Laraba in da za a yi masa janaza a fadar Sarkin Gwandu dake birnin Kebbi.

“Mai martaba ya rasu yau za a yi masa janaza a fadar Sarkin Gwandu da qarfe uku na rana, Allah ya jiqansa da rahama.”

“Shi ne ya gadi mahaifinsa margayi Alhaji Muhammadu Bashar Mai-Wurno, wanda yake babban xan Sarkin Gwandu Alhaji Haruna Rasheed.”

Ya bayyana rasuwar rashi ne ga mutanen jihar Kebbi musamman gefen sarakuna.

Ya ce Gwamnan Kebbi yana Amerika wajen taron majalisar xunkin duniya suna cikin tawagar mataimakin shugaban qasa Kashim Shattima duk da haka ya bayyana kaxuwarsa da rashin da aka samu a jihar. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here