Home Rahoto Mutane sun mutu a wata sabuwar Annoba a Sokoto

Mutane sun mutu a wata sabuwar Annoba a Sokoto

7
0

Gwamnatin jihar Sakkwato ta tura jami’an lafiya na gaggawa, magunguna da sauran kayayyakin aikin lafiya zuwa ƙaramar hukumar Bodinga, biyo bayan rahotannin mutuwar mutane da kuma bullar wasu cututtuka da ake zargin na da alaƙa da wata annobar zazzabi a yankin.

Matakin ya biyo bayan rahotannin da aka samu mutane da dama da abin ya shafa, musamman a garin Sifawa, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Faruk Wurno, shi ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da jaridar PUNCH a ranar Asabar.

Ya ce an tura ƙarin jami’an lafiya da muhimman kayayyakin aikin jinya zuwa ga al’ummomin da abin ya shafa domin kula da marasa lafiyar da kuma hana ƙarin asarar rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here