Shugaban ƙaramar hukumar Zaki ta Jihar Bauchi, Mas’ud Aliyu Umar, ya rasu a wani hatsarin mota a lokacin da ya ke dawowa daga taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar Allied Peoples Movement (APM) da aka gudanar a birnin Bauchi.
Jaridar VANGUARD ta rawaito cewa Umar ya rasu ne a daren jiya Lahadi, bayan motar da ya ke ciki ta yi hatsari a ƙauyen Konkiyal da ke ƙaramar hukumar Darazo, mai tazarar kusan kilomita 100 daga cikin birnin Bauchi.
Marigayin shugaban ƙaramar hukumar na kan hanyarsa ta komawa Zaki ne bayan halartar taron, lokacin da hatsarin ya afku.
Da ya ke magana akan rasuwarsa, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana matuƙar kaduwarsa, inda ya bayyana marigayin a matsayin ma’aikacin gwamnati mai kishin aiki, ɗan siyasa mai kusanci da talakawa, kuma shugaba mai tausayi.
Gwamnan ya ce gudummawar da marigayin ya bayar wajen hidimar jama’a da ci gaban al’umma za ta ci gaba da kasancewa a tarihi.
A cikin saƙon ta’aziyyar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa lokacin da Umar ya jagoranci hukumar SEMA, ya nuna ƙwazo wajen rage wa al’umma masu rauni wahalhalu, tare da gaggauta kai ɗauki ga al’ummomin da ibtila’i da matsalolin jin ƙai suka shafa.
Mohammed ya ƙara da cewa a matsayinsa na shugaban ƙaramar hukumar Zaki, marigayin ya nuna jajircewa wajen bunƙasa ƙananan hukumomi ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa matasa da mata, inganta rayuwar al’umma da kuma samar da ci gaba mai haɗa kowa da kowa.






