Home Siyasa Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Kebbi Don Gudanar Da Yekuwar Zaɓensa—-Gwamna Idiris

Shugaba Tinubu Zai Ziyarci Kebbi Don Gudanar Da Yekuwar Zaɓensa—-Gwamna Idiris

9
0

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci jihar domin gudanar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Birnin Kebbi, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC na shekarar 2027 a jihar.

Nasir Idris ya ce ziyarar Shugaba Tinubu za ta kasance wani ɓangare na ayyukan yaƙin neman zaɓen jam’iyyar gabanin zaɓukan da ke tafe.

Ya buƙaci mambobin kwamitin da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma da gudanar da gangamin neman goyon baya daga matakin ƙananan hukumomi har zuwa matakin jiha, domin tabbatar da nasarar APC a faɗin jihar.

Haka kuma, gwamnan ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da su tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya a tsakaninsu gabanin zaɓen.

A nasa jawabin, Shugaban APC na Jihar Kebbi, Abubakar Kana-Zuru, ya ce kwamitin zai jagoranci daidaita ayyukan wayar da kan al’umma da tattara magoya bayan jam’iyyar daga matakin ƙasa har zuwa matakin jiha.

Ya kuma buƙaci masu rajistar zaɓe da su tabbatar sun mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC), tare da fitowa domin kaɗa ƙuri’a a zaɓen 2027.

Taron ƙaddamar da kwamitin ya samu halartar shugabannin APC, tsofaffi da masu riƙe da muƙaman siyasa a yanzu, ’yan majalisun tarayya da na jiha, da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here