Ƙungiyar Ansaru ta ɗauki alhakin kashe Sheikh Yahaya Masussuka
Ƙungiyar ƴan ta’adda ta Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki alhakin kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, a gidansa da ke Dutsin-Ma, Jihar Katsina kamar yadda mai sharhi kan al’amuran tsaro, Barista Audu Bulama Bukarti ya wallafa.
Acewarsa, kungiyar ta tabbatar da hakan ne a wani saƙon murya da ta fitar a ranar Talata, inda ta zargi malamin da kasancewa kafiri, ba tare da bayyana takamaiman laifin da take zargin ya aikata ba.
A cikin saƙon, Ansaru ta ce ta kai harin ne da misalin ƙarfe 8:30 na dare, duk da cewa ta ambaci ranar Talata a matsayin ranar da lamarin ya faru, alhali rahotanni sun nuna cewa kisan ya faru ne ranar Litinin.
Ƙungiyar ta kuma zargi Sheikh Masussuka da adawa da abin da ta kira koyarwar Musulunci. Sai dai, ana hasashen cewa matsayinsa na ƙarfafa zaman lafiya da tattaunawa tsakanin mabiya addinai daban-daban na iya kasancewa cikin abubuwan da suka sa aka kai masa hari.
A cewar Barista Audu Bulama Bukarti, malamin na shirin gudanar da wani babban taron zaman lafiya, lamarin da ka iya kasancewa cikin dalilan da suka sa ƙungiyar ta ɗauke shi a matsayin abin hari.
Ansaru ta balle daga ƙungiyar Boko Haram a shekarar 2012, sakamakon rashin jituwa da shugabancin Abubakar Shekau. Tun daga lokacin, ƙungiyar ta fi gudanar da ayyukanta a yankunan Arewa maso Yamma, musamman jihohin Zamfara, Kaduna da Neja.
Rahoton ya nuna cewa ikirarin ɗaukar alhakin kisan da Ansaru ta yi ya ƙara jefa haske kan barazanar da masu fafutukar zaman lafiya da tattaunawar addinai ke fuskanta a wasu yankuna na ƙasar.






