Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 40

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 40

14
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 40📑

__📖 Dr Alƙali yaji daɗin al’amarin ba kaɗan ba, dama yana zaune a office ne, kawai sai yaji kaman yayi tsuntsuwa ya koma gida, haka ya daure ya gama duba patients ɗin da suke gaban shi, yana gama ganin su ya kamo hanyar gida.

A parlour ya samu Aunty hauwa tare da Aunty uwani suna cin abinci suna kallo kuma, yana murmushi yace, “ƴan mata sai yanzu kuke cin abinci? Laillai kuna jin daɗi fah”, ya nemi wuri gefen matar shi ya zauna.

Bayan sun gaishe shi ne, suka cigaba da cin abincin sun hankali kwance, shidai sai duba abu yake a wayan shi batare da yace uffan ba kuma, suna gama ci Aunty hauwa ta miƙe zata bar wurin domin mata da mijin su samu sakewa, ganin haka yasa ya ɗago da manyan idanunshi yana murmushi yace, “amaryah dawo ki zauna, tafowan da nayi ae duk don ke ne”.

Wurin data tashi ta koma ta zauna tana kallon shi, “yauwa Hauwa ɗazu Bappah ya ƙirani yake gaya mun cewa na gaya miki yau ya ɗaura miki aure da ƙanin mijinkin nan Abdallah”…….. Wani irin miƙewa tayi da murya mai ƙarfin gaske tace, “a wani hujjan za’a ɗaura mun aure da mutumin da bana so” wallahi auren nan bai ɗauro ba, ko sama da ƙasa zasu haɗu toh aure bai haɗu ba”, ta faɗa tana zare ido kaman zata kai duka wa Dr.

“Saboda ke kin isa da kanki ko? toh ki sani bawai barinki ake yi ba kike abinda kika gan dama hauwa, kuma baki isa kija da iyayen mu ba, aure an riga da an ɗaura ya rage naki kiyi biyayyah wa mijinki ko akasin hakan”, yana gama faɗa ya miƙe yayi ɗakinshi, ita dai Aunty uwani sai juya kanta take tayi alaman bata so hakan ba, tafi so abi komai a hankali, hakan yasa ta fara rarrashin Aunty hauwa, ita kuma bata sararara ba kawai ihu da kuka ta fara, daga baya ta fita da gudu zuwa ɗakinta, inda suke tare da yaran Aunty uwani, kwanciya tayi ta fara rera kuka mai azabar taɓa zuciya.

Har akayi magrib Aunty hauwa kuka ta keyi bata saurari kowa ba, bayan tayi sallah ne ta shiga wanka domin tayi shirin tafiya night duty da ta keyi, wanda yau idan tayi zata shiga up na 1week, tana wanka ta shirya, lokacin aka ƙira ishaa, babu ɓata lokaci tayi sallan ta miƙe ta ɗauki jakanta ta fito domin tafiya, a parlourn ta samu Dr da Aunty suna cin abinci, yana dubanta yace, “amaryah kinci abinci kuwa”?.

Hararan shi tayi bata ce mishi komai ba tayi hanyar waje, tana fita yayi murmushi ya dubi bayanta yace, “zama ki ɗame ae”, suka cigaba da cin abincin su shida matar shi, wanda ta ke ta mitan ya dinga bin ta a hankali da lallaɓi, bawai yayita ɓata mata rai ba, shidai dariya kawai ya keyi bai ce mata ƙala ba.

Tana shiga office ta samu wanda zasu karɓe su suna shirin tafiya, gefe ta samu ta zauna, bayan sun gaisa taji wayanta yana ringing, da sauri ta fito da shi kawai sai taga Baban Narabi ne, jikinta yana rawa ta ɗauka sannan ta miƙe ta bar office ɗin tayi waje.

Bayan ta gaishe shi ne ya fara mata maganan yadda auren ya taso sannan ya bata haƙuri na gaggawan da aka mata, Aunty hauwa ce mishi tayi babu komai ae sun isa da ita ne, amma tana maganan tana kuka, jin haka yasa Baba yayita saka mata albarka daga baya yayi mata nasiha sosai, wanda har saida sautin kukanta ya dinga fitowa, suna gama wayan ta ƙira Ummi har lokacin kuka ta keyi, itama Ummin haƙuri tayita bata tana rarrashinta da kalamai masu daɗin gaske, wanda Aunty hauwa ita kuma tayita mitan yayah zata iya zama da Abdallah bayan ya raina ta, itafa matar yayan shine kawai don raini yazo ya aureta?

Ita dai Ummi haƙuri ta ke bata chan ƙasa-ƙasa kuma tana dariyan hauwan da taji tana maganan wai ya rainata, haka suka gama maganan Aunty hauwa ta koma ciki, nan kuma an kawo masu haihuwa har mutum uku, dole ta zage ta fara aiki.

Tunda Abdallah yaji an ɗaura mishi aure da hauwa, farin ciki ya taso shi gaba, jiki na rawa ya ƙaraso gida wurin Baban shi, inda shi kuma Baban ya fara mishi nasiha da yayi adalci a tsakanin matan na shi, kuma ya gaggauta gayawa fadilah abinda ya faru, sannan ya mishi nasiha sosai.

Abdallah yana fita a parlourn Baba ya ƙira fadila, cikin nutsuwa ya mata bayanin komai, amma abin mamaki bata nuna mishi damuwarta ba, kawai fatan Allah ya basu zaman lafiya tayi, daga baya ta tambaye shi yaushe zai dawo zaria? Jiki a sanyaye yagaya mata zuwa gobe ko jibi, haka sukayi sallama ya shige motar shi yayi cikin garin jos gidan Aunty Amina.

Washegari da safe Abdallah ko karyawa bai yiba ya kama hanyar garin bauchi, amarya tayi ƙira, tunda yaje yake ƙiran wayarta amma firr taƙi ɗagawa, yananan ƙofar gidan saiga Dr ya fito wurin 9:00am zai wuce office, mamakin ganin Abdallah yayi a kofar gidan, cikin mamaki yace, “Hauwan bata san kazo bane?” ya tambaye shi da sauri, yana murmushi kanshi a ƙasa yace, “yanzu na iso ina shirin ƙiranta kenan”, Abdallah ya faɗa yana ɗaga wayan shi alaman zai ƙirata.

Da sauri Dr ya koma ciki, inda ya tarar da Aunty Uwani a tsaye gaban dinning tana tattare kayan da yayi breakfast da su, “mantuwa kayi Dr”? “babu wallahi, kawai na fita sai naga mijin yarinyar nan Abdallah tsaye a ƙofar gidan, daga dukkan alama ya nemeta taƙi fitowane, don daga gani ya daɗe a ƙofar gidan”, ya faɗa yana wucewa zuwa ɗakin su Aunty hauwa, daga ƙofar ɗakin ya tsaya yana ƙiran sunan ta, amma firr tayi shiru kamar mai bacci taƙi amsawa, ganin haka Aunty uwani ta shiga.

Ganin bazata fitoba yasaka shi shiga ɗakin ranshi a ɓace, kaman zai wanka mata mari yake mata masifah, “ke hauwa wa kika ɗauka yaronki ne a gidan nan? Kinsan Allah idan raina ya gama ɓaci bansan me zan miki ba, banzar yarinya mai masifar tsiya, ke har kin isa iyayen mu su zartar da abu kidawo kina nuna basu isa ba? Ke wacece? Wuce kifita kije wurin mijinki kafin na nuna miki ɗayan halina ɗin”.

Fuska a ɗaure ta fita wurin Abdallan, shi kuma Dr yazo ya mishi tasss akan kada ya fara sakewan da Hauwa zata raina shi, gara ya rage nuna mata damuwan shi akanta kafin raini ya biyo baya.

Tsayawa tayi a gaban motan sai cin magani ta keyi tana harare-harare, tsayawa yayi na wani lokaci yana dubanta, chan ya koma Abdallan shi yana dubanta fuska a murtuƙe yace, “nifa bana son rashin hankali, hakan yayi miki mutunci kizo gabana kina wani juye-juyen jiki kamar ke kaɗaice mace a duniya? Ko kuma haka aka ce miki ana taryan baƙo? Toh ni bazan ɗauki rainin hankali ba”, ya faɗa mata fuskan shi a murtuƙe, da sauri ta juyo da nufin ta maida mishi martani, amma ganin fuskar shi ya sakata juya da fuskarta gefe tace, “toh ni nace maka kada ka shigo ne,? Ni ae jira nakeyi ka shigo”, ta faɗa tana ta murguɗa bakinta ta gefen shi.

“Nidai koda wasan wasa kada ki nemi raina mun hankali, maganar auren nan nayi ne don samun kwanciyar hankalinmu gaba ɗaya, amma kina ta wani nuna isan ke wata ce, bayan na samu Baba nace mishi bana son maganan abarki ki auri wanda ki ke ganin kun dace amma firr ya tafi akan maganan, ni bana son nunawa iyayena ban haihu ba a wurinsu shiyasa na amshi buƙatun su da hannu bibbiyu, amma hakan bazai saka ki raina mun hankali ba don ina da wacce ta fiki komai a gida”, ya faɗa yana tafiya hanyar shiga parlourn.

Baki a buɗe ta bishi da kallo cike da mamakin shi, tana tambayar kanta dama ba wai sonta yake ba? Har yana nufin matar shin tafita komai da komai, kodai don ita matar shi yana sonta ne yake ganin ta haɗu? amma ita dai taga photon matar da ta je gidan Umaima, kuma bataga ta fita komai ba, banda ma wani bleaching da ya ɓata mata fuska gata gajeruwa lukuta sosai, tsaki taja ta bi bayan shi zuwa parlourn.

Gaisawa ta samu su nayi da Aunty uwani, itama ta nemi gefe ɗaya ta zauna, har Aunty uwani ta fita bata ɗaga kai ta dube shi ba, shi kuma babu abinda yakeyi sai kallonta, domin ba ƙaramin shiga ranshi tayiba, shiru zuwa wani lokaci yace, “ke kam Hauwa baki ɗauki halin kirki irin na ƴan gidanku da iyayenki ba, amma har yaushe baki san yadda ake mutunta baƙo ba, ballantana kuma ina da ƙarin darajar matsayin miji a gare ki, kina son albarka kuwa”? Ɗago kai tayi tana duban shi, murya cike da sonyin kuka tace, “ba kai bane kace dole aka maka ka aureni, kuma wai ban kai matar ka komai ba, kuma wallahi na gani na fita kyau, kawai faɗa ne baza kayi ba don ita kana sonta”, ta ƙarasa faɗi kaman zatayi kuka.

Dariya yayi yana dubanta cike da nishaɗi a ranshi yace, ” kin taɓa ganin inda aka fi son wata mace sama da uwargidan ka? Toh ki daina ruɗin kanki matar farko baka ganin wacce ta fita a komai, ballantana wanda kukayi soyayyah kana sonta tana sonka”, ya ƙarasa yana gyara zaman shi.

Turo baki tayi gaba, ” hmmm nidai nasan Hero duk da a ta biyu ya aure ni yafi sona akan Aunty suwaiba, kuma kullum ce mun ya keyi ina da kyau, saboda haka nasan ni mai kyauce, don muna secondry school Hauwa golden girl ake cemun”, ta faɗa tana jujjuya idonta.

Kallonta ya tsaya yanayi a cikin zuciyar shi yace, “wato duk matar mamaci magana ɗaya sai ta kwatanta da mijinta ko? toh yanzu don Allah idan da ba don ɗan’uwan shi bane da yaya zaiji a ranshi?” a fili kuma yace, “shiɗin ae ya aure ki yana sonki ne duk da ma ance Abba ne ya tura mishi ke, shi kuma yayi biyayyah ya karɓa kaman yadda nima nayi yanzu, shi kuma bansan dalilinshi na ganin kyaunki ba? nikan bana gani gaskiya, ko dan banji ina sonki bane ohoo”, ya faɗa yana wani ya mutsa fuska.

“Wallahi baka isa kace mijina baya sona ba, don ni nafi kowa sanin irin son da yake mun, kaidai da baka sona kai ka sani, don ni ban maka dole ba, idan baka so akwai mai so kabar mishi ni kawai zai fi mana zaman lafiya”, ta faɗa tana share hawayenta.

Dariya yayi yace, “nima haƙuri zanyi don kada iyayena suga ban mutunta su ba, amma ke idan kinga zaki nunawa duniya iyayenki basu isa da ke ba, toh kiyi gaggawan taimaka mana ki gaya musu baki sona, ko nima zan samu kwanciyar hankali”.

Shiru tayi na zuwa wani lokacin, sannan ta dube shi baki ta murguɗa mishi tace, “da yake nice wanda akace jeki kya gani ko? wanda bansan darajan iyaye na ba, toh bazan faɗan ba, kai da baka son kaje ka faɗa”.

Miƙewa yayi yana zurma hannun shi cikin aljihun shi yace, “nidai babu ruwana ban iya jayayyah da yayuna bama ballantana iyaye na ba, ke kuma na barki lafiya da halinki na rashin mutunta baƙo, zanje gidan umaimah nayi breakfast na wuce, domin gobe da safe xan wuce Zaria wurin my luv ɗita”, yana dariya ya ajiye mata kuɗin da yakai 20k a cinyarta yace, “ki dinga transport kafin na dawo ko”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here