NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE✍🏼
@wattpad AuntyNice.
SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI
SHAFI NA 39📑
__📖 Bata daɗe ba ta fito daga cikin gidan, hannunta ɗauke da tray, har inda yake ta ja table ta ɗaura akai, juq ne cike da zoɓo mai ƙamshin gaske, sannan cooler kuma cike yake da jaloop rice, wanda yaji kayan haɗi har da hanta, bayan ta zuba mishi ne ta koma cikin gidan ta barshi a wurin.
Busmillah yayi ya fara cin abuncin yana ɗan sipping zoɓon kaɗan-kaɗan, sai wani lumshe ido yakeyi na jin daɗin zoɓon, haka yayita ci har yaji ya ƙoshi, bayan ya gama ne ya ɗauki jug ɗin ya cika shi da zoɓo, sannan ya ɗauki wayan shi ya danna ƙiran Aunty hauwa, tana ɗauka yace, “ki fito nagama”.
Zama tayi a kan kujeran sannan ta fara gaishe shi, bayan sun gaisa ta ce, “naganka kwatsam ina fatan ba wani abu mukayi maka ba ko”? ta ƙarasa faɗi tana duban shi, murmushi yayi mai kyaun gaske yana kurɓan zoɓon yana kallon ta har cikin idonta, sannan yace, “nazo tafiya da ke ne”.
Hararan shi tayi, “ni kayace da zaka zo kace zaka ɗauke ni ne”? Murmushi yayi yace, “zanje na aurar da ke ne, don naji ance baki iya zaɓe ba kin zaɓo mana wani sunduƙi”, ya ƙarasa faɗa yana ajiye cup ɗin zoɓon.
“Hmmm batun yau ba na ke zaɓo sunduƙan ba kenan, tunda bashi kaɗai na fara zaɓa ba”, fuskan ta a murtuƙe ta faɗa masa.
Zuba mata ido yayi batare da yace komai ba, hakan yasa ta kasa cigaba da maganan ta ta sunkuyar da idonta ƙasa.
“Hauwa bana son wannan auren da kike shirin yi, domin ina kishin wani ya aure matar ɗan’uwa na, saboda haka ni nan zan aure ki domin kada ki haɗa mana zuri’a da wasu irin kuma daban”.
Tashi tayi tsaye tana bin shi da wani irin kallon mai cike da raini a ciki, “lallai Abdallah idonka baya cike da kunya, ni matar yayankan zaka duba kace wai ni zaka aura? Toh a wani hujjan? Ina ce ana wannan auren idan da akwai yara a tsakani ne? Toh ni babu wani sauran abu a tsakanina da kai, yarinya kuma ko nayi aure ba wurina zata zauna ba ballantana kace zataje gidan wani baka so, saboda haka gara ka farka daga baccin da kakeyi, ni Hauwa nafi ƙarfin na auri yaro mai raina mutane irin ka, kaje chan ka ƙarita da tsohuwar matarka ni bana so”, tana faɗa ta juya cikin gidan ta bar shi zaune a parlourn yana murmushi mai cike da ɓacin rai.
Kuka ta keyi mai ƙarfin gaske inda taje ta samu Aunty Uwani ta zube tana ta kuka, Aunty uwani duk ta ruɗe sai tambayarta ta keyi mai ya faru amma taƙi faɗa mata komai sai kuka da ta keyi, ganin bazata kula ta ba yasa, ta wuce parlour wurin Abddallah, inda ta samu ya miƙe yana shirin tafiya.
Bayan sun gaisane ta tambayeshi abin da ya faru, cikin girmamawa ya gaya mata komai, yana kuma ƙasƙantar da kai alaman yana neman ta tsaya mishi akai, Aunty uwani ta yaba da Abdallah shiyasa ta bashi tabbacin zata samu ɗan’uwanta da maganan, shi kuma godiya yayi mata ya kama hanyar shi sai misau.
Tunda ya isa Bappah yake ta nannan da shi, bayan kuma ya gaya mishi abinda ya kawo shi, Bappah ba ƙaramin jin daɗi yayi ba, ƙiran Uncle Auwal yayi a waya yazo ya same shi, bayanin komai Bappah yayi mishi, shima abun yayi mishi daɗi, domin sanin kirki da karancin iyayen Baba Umar.
Bappah ya ƙira Abba ya gaya mishi duk abinda ake ciki, Abba ya nuna farin cikin shi amma yace a haƙura har sai ita Hauwan ta amince, sannan Bappah ya ƙira Baban Narabi ya zayyana mishi komai, shidai Baban Narabi murmushi yayi, a zuciyar shi yace dama yasan za’a rina wai an saci zani mahaukaciya.
Uncle Abdallah a misau ya kwana, da safe ya kama hanyar bauchi, lokacin da yaje yayi dai-dai da dawowar Aunty hauwa daga duty, tana ganin shi ta wuce bata kula shi ba, ko damuwa baiyi ba, wucewa kai tsaye yayi har parlour yayi sallama, inda Aunty uwani da yayan su Aunty hauwa suke zaune, wurin zama suka bashi cike da kulawa, bayan sun gaisa aka haɗa mishi breakfast, amma yace musu yayi a misau.
Zama sukayi shida dr Alƙali, yayan su Aunty hauwa sukayi magana mai muhimmanci, amma firr Aunty hauwa da aka mata maganan taƙi basu haɗin kai, da yake Dr Alƙali ba mai yawan magana bane sai yabawa Abdallah haƙuri akan ya tafi zai shawo kanta daga baya, babu yadda ya iya haka yayi musu sallama ya tafi, Abdallah irin mutanen nanne masu ƙin yadda suga sun faɗi a neman abu, kuma shi idan yaso abu nacin shi yana dayawa, ballanta wannan da yake ganin idan ya rasata toh zai sha kunya, a ransa ya saka duk abinda zatayi zai daure, don shi Allah kaɗai yasan irin son da yake yi mata kawai ƙarfin hali ne da kuma kada a gane ya damu da ita shiyasa bai nuna ba, kuma a tunanin shi ae Hauwa yarinya ce, dole zata koma tayi karatu ne bawai maganan aure ba, hakan da yayi niyyah ya saka shi wucewa Narabi.
A parlourn Baban Narabi ya zauna ya dinga sauƙe mishi rikicin shikan aje a nema mishi auren hauwa, inda hali ma a tafi da sadaki, Baban Narabi ƙura mishi ido yayi har na tsawon lokaci, saida ya karanci ehh tabbas Abdallah da gaske ya keyi son Hauwa ya keyi tsakani da Allah, sai yayi gyaran murya yace, “toh in banda abinka Abdullahi tun yaushe aka bika akan ka aureta kaƙi, sai yanzu da yarinya ta haɗu da wanda ta keso zamuje muce ga zance ga magana? Ina ce Aishan ko ka aureta ba baka ita za ayi ba, toh meye dalilinka na auren Hauwa?”
Kallon Baban yayi sannan ya sunkuyar da kanshi ƙasa, “nidai Baba ina sonta ne, ae nima zata haifa mun irin Aishan, ko basu bani riƙon Aishan ba hala ta haifa mun mai kama da Aishan”.
Dariya baba yayi yana duban Abdallah cike da ƙaunan ɗan na shi yace, “Abdallah wato kaima sake zakayi hauwa ta sake haifan me kama da ita ba mai kama damu nan ba ko? Wani irin so kukeyiwa Hauwa ne kam”? Baba ya ƙarasa yana murmushi mai cike da jin daɗin al’amarin.
Sunkuyar da kai Abdallah yayi ƙasa, “Baba don Allah kuje ko gobe nema, naga hauwan so ta keyi ta mun yarinta, gara aje da wuri kada ta auri wancan ɗayan, ni bana son zamanta a bauchi ma wallahi don zasuna haɗuwa”.
Wannan lokacin dariya mai ɗan ƙarfi Baba yayi, yana duban Abdallan cike da mamakin irin nashi kishin, “toh ka gayawa ita maiɗakin kane zaka ƙara aure”? Baba ya jefa mishi tambaya.
Abdallah ya dubi Baba yace, “Banida matsalah da Fadilah nidai damuwata a fara zuwa gidan su hauwan”.
Babu ɓata lokaci Baban Narabi washe gari da ƴan’uwanshi mutum biyu, sai uncle sabo ƙanin uncle Abdallah dayaja zuwa misau. Bappah ba ƙaramin karɓa ya musu ba, bayan sun gaisa sun sha ruwa Baban Narabi yayiwa Bappah bayanin abinda ya kawosu, Bappah tashi yayi ya ƙira ɗan’uwanshi wanda yake mahaifi wa Aunty Ummi da Dr Alƙali, da yake shi bamai son wargi bane yace su tsaya ana sallan azahar a ɗaura aure kawai, babu maganan jeka ka dawo a tsakanin su, Bappah ma yayi na’am da batun ɗan’uwan shin, suma su Babam Narabi sunji daɗi ba kaɗan ba da irin dattakun da aka musu.
Ana sallan azahar aka ɗaura auren Aunty hauwa da Uncle Abdallah a masallacin ƙofan fada da yake garin misau, hattah su Mama dasu Addagana sunji daɗin wannan auren ba kaɗan ba, domin farin cikin yaxama musu biyu, inda Uncle Auwal yazo musu da labarin aikin shi daya samu da NNPC, inda Baban Misau, kuma ɗan Mutanen Misau, Dr maikanti baro Allah yajiƙanshi da rahma ya sama mishi aiki a wancan lokacin. ALLAH KAJIƘAN DR MAIKANTI BARU, ALLAH KASA YANA CIKIN RAHMAR UBANGIJI, ALLAH KA DUBA BAYAN SHI KASHIGA AL’AMURAN SU YADDA SHIMA YA SHIGA NA MUTANE, ALLAH YA HASKAKA RAYUWAR IYALANSHI
Lokacin da aka gama ɗaura aure Baban Narabi da kanshi ya ɗaga waya ya ƙira Abdallah yana murmushi yace, “Albishir Abdallah!” cikin zaƙuwa ya amsawa Baban nashi da “goro”.
“Toh yau dai Allah ya nufa an ɗaura aurenku da Hauwa, sai ka shiryah mana goron Albishir ɗinmu”, Baban ya faɗa mishi cike da murna, ae babu shiri Abdallah yace, “Baba nabaka kujeran zuwa umrah kaida su Bappah, insha Allahu ku uku ku shiryah tafiya zuwa nan da sati biyu”, murmushi mai cike da dattaku Baban ya amsa mishi da sun gode, tukun yace ya bar maganan tarewar har sai ita hauwan ta shiryah, daga nan sukayi sallama ya kashe wayan.
Saida akayi sallan La’asar tukun su Baban Narabi da bappanun Abdallah suka dawo Narabi cike da murnan abinda ya faru, suma mutanen gidan kowa ka ganshi cike da murna a fuskar shi.
Bappah ne ya ƙira Dr Alƙali yagaya mishi an ɗaura auren Aunty Hauwa, sannan kuma yace ya sanar mata, sannan ya ƙira su Ummi ya sanar musu, ita dai Ummi taji daɗin wannan haɗin, don ko baɓu komai, baza’a rabawa Aisha hankali yadda zata fahimci wani abuba, duk ranan da taje wurin Aunty hauwa zataje ne a matsayin gidan Ummanta, Abdallah kuwa Mijin Ummanta, kenan komai zai zo mata cikin sauƙi, gaskiya Ummi taji daɗin abun ba kaɗan ba.




