Home Daga Marubutanmu Maunin Rayuwa: Fita Ta Biyu

Maunin Rayuwa: Fita Ta Biyu

5
0

Page 2

ƁANGAREN SURAYYAH

Da misalin ƙarfe goma da minti arba’in da biyar na dare suna baje a kan shimfiɗun da aka malala tsakar faffaɗan gidan, kowa yana gurbin kwanciyarsa kawai ta ji an hankaɗe ta ta mulmulo daga gefen katifar zuwa ƙasa bakinta ya ƙumu da wani ɗan dutse da yake kafe a cikin ƙasa.

Ah! Ta saka ƙara tana yunƙurin tashi zaune da shafa gun. Ta haska da fitilar hannunta ta ga jini, ai ko ba ta ɓata lokaci ba ta miƙe ta haura kan katifar ta sakarwa Minal da ta lafe a kai kamar ba ta yi komai ba dundu a gadon baya.

Ba shiri ta wartsake daga baccin munafuncin da take ta dafe gun tare da sake ƙara “Wa! Kai! Ka kai! Me na miki kika daken?”

Surayyah ta banka mata harara a cikin duhun, aikuwa ta sauko daga kan katifar tana shirin ramawa. Surayyah ta ƙanƙance ido cikin alamun jin masifa “Ai wallahi kina kai hannunki jikina zan tsinke ki da mari…”

Daidai lokacin baaba Hannatu ta fito daga ɗakinta da ba shi da nisa da inda shimfiɗun nasu suke ta ce “Amma ke dai Surayyah an yi babbar kwabo, me ya sa ke kullum ba ki da aiki sai neman rigima da ƙannenki?” 

“Baaba ita ce fa ta fara hankaɗo ni ƙasa na fasa baki, kuma wallahi da gangan ta yi da ma duk kwanakin nan nemana take da masifa ina sani shiru na mata.” Ta faɗa da hasalalliyar murya.

Tsayawa ta yi gefen ƙofar ɗakinta ta dallowa Surayyah fitilar hannu a ido. Surayyar ta yi saurin kauda kanta gefe. 

“To laifin wa? Na ce wa ya ja a raina shi Surayyah? Dube ki fa goɗai-goɗai dake kina kwanciya a cikin ƙannen ƙannen bayanki. Shekara 30 kenan da ‘yanwatanni da haihuwarki, amma har yanzu kin gagara yin aure. Sa’o’inki daga mai ‘ya’ya uku sai mai huɗu amma ke dube ki, ga ki nan ƙyamus-ƙyamus a cikin ƙannenki. A lalace kin ba wa Minal shekara goma don ko da na haife ta kin kusa gama primary. Shekara dai ba ta faɗuwa sai a jiki, idan ba ki kama jiki ba kina zaune tsufa za ta zo, ahtoh!”

Surayyah ba ta iya cewa komai ba amma jin maganganun take kamar ana watsa mata ruwan zafi. Shin ita kam sai yaushe ne za a daina yi mata gorin aure a gidan nan? Ita ba mai son fitina ba ce amma ya kamata yau ta tauna tsakuwa ko don aya ta ji tsoro kamar yadda take yi lokaci zuwa lokaci idan buƙatar hakan ta taso.

Ita kuwa Minal ganin an shigar mata rigima sai ta hau bakinta da faɗen “Ai ba za ta yi auren ba, wani hamshaƙi take jira, kodayake ma wa zai ɗauki kayan baƙin hali ya ajiye a gidansa?” 

Raɗaɗin ƙunar maganganun Minal da ta ji ya ninka na baaba sau biyar don haka ido a rufe ta falle Minal da wani gigitaccen mari cikin jin masifa da tunzurarriyar zuciya ta fara magana.

“Idan ke jahila ce Minal ni ba ita ba ce, na san aure lokaci ne, kamar dai mutuwa da haihuwa ba wanda yake faruwa sai wa’adin da aka ɗiba masa ya cika. Baƙin hali kuwa yana nan ƙunshe a jikinki, ke ma ki jira ki ga yadda ƙaddara za ta yi da rayuwarki kafin ki zagi rayuwar wani.”

Waigawar da za ta yi haka tana huci ita ma ta jiyo saukar tafi a kuncinta, baaba ta wanke ta da mari mai kyau sannan cikin masifa ta ɗora da.

“Bisa kanki! Bakinki kuma sai dai ya sari ɗanyen kashi in sha Allahu, wannan baƙin jinin dai irin naki ba da ‘ya’yana ba. In kin ji makwanci bai miki ba za ki iya nemar wani, daga jinƙai sai ya koma jinƙice?”

Wasu hawaye masu zafi ne suka fara sirnanowa daga idanunta ta miƙe daga kan katifar zuciya cike da ƙuna ta ja hijabinta da yake kan igiya ta saɓa a kafaɗa ta nufi ƙofar Baffa Bashir.

Daidai lokacin tuni wasu daga cikin ‘yanmata da ƙananun yara da ke kwance gun sun farka, waɗanda dama ba su yi bacci ba suna gefe suna kallo ba halin tamkawa saboda kowa yana shakkar baaba Hanne shi ya sa ko sabgar ‘ya’yanta ba a shiga a gidan. Farida da komai ya faru a kan idonta ita ce ta yi ƙunar baƙin waƙe ta miƙe tsaye ta durƙusa ta ɗauki buta tana faɗar “Gaskiya dai baaba ba ki kyauta ba, ke kike ɗaurewa yaran nan ƙugu suna zuba wa anty Surayyah rashin mutuncin da suke so a gidan nan, jinkirin aure ba kanta farau ba, ba kuma za a ƙare a kanta ba. Wani zubin ma hakan shi ya fi alkhairi, ni da na yi auren wurin me ya tsinana mana, daga ni har ku ban da shiga baƙinciki da takaicin rayuwa? Yanzu ga ni nan ina zawarci da tsohon ciki da ƙananun shekaruna.”

Ta fara takawa da ƙyar tana tura ciki tana nufar banɗaki.

“In yeah! Lallai Faridatu wuyanki ya isa yanka. Ni kike faɗawa magana haka?”

“Ai gaskiya ne baaba, korar ta ma da kika yi ba daidai ba ne don ita ma tana da haƙƙi a gidan nan.” Tana gama faɗa ta shige ciki abinta ta bar baaba Hanne tana kumfar baki.

Surayyah kuwa ko da ta isa ƙofar Baffa Bashir da ke can hanyar fita daga gidan ganin ƙofar a rufe sai ta ja ta tsaya, wata zuciyar na yi mata huɗubar tsiya tana nuna mata kawai ta nufi gidansu a wannan daren. Sai dai ta san cewa ko gidan nasu ta je ba za ta samu maraba ba ballantana wurin kwanciya. Gidan nasu ya yi matsatsi da yawa wannan ya sa idan dare ya yi ake rarraba su a gidajen ‘yan’uwa. A bar shi ma akwai wurin kwanciya amma ta sani nufar can ganganci ne don idan ba a yi sa’a ba ma har gara kalaman da ta ji a nan a kan waɗan da za ta iya ji daga bakin mahaifiyarta. 

Za ma ta yi a gun ta haɗa bayanta da jikin bango tana kuka a hankali, a ranta tana karanto addu’o’in samun sauƙi a zuciya tare da addu’ar Allah ya gaggauta koro mata mijin aure, amma duk da haka ba ta fatan ta maimaita rashin sa’ar zaɓen wanda take fata ya zame mata abokin rayuwa kamar dai yadda ta yi har sau biyu a baya. Ta ɗauki tsawon mintuna talatin zaune a haka cikin ƙunci, kwatsam ba tsammani ta ji wani ƙwaro ya yi mata mugun harbin da ba shiri ta ƙwallara ƙarar da sai da ta farkar da matar Baffa Bashir. Ta miƙe a gigice ta jefar da hijabin jikinta tana yunƙurin cire riga mama Salame ta fito a ruɗe tana haska fitila ta rirriƙe ta tana faɗar “Subhanallah! Surayyah me kike yi a nan? Me ya same ki?”

Yi take kamar za ta shiɗe tana fisge-fisge duk gumi ya karye mata da ƙyar ta iya buɗar baki. “Wani ƙwaro ne ya cije ni.” 

Mama Salame ta fara haska fitila a ko ina tana neman ƙwaron, can nesa ta hango kunama baƙa wuluk ta tada ƙarinta sama tana wucewa da hanzari. Kalmar shahada ta ja a take kunamar ta ƙame a gun ta cire takalmin ƙafarta da sauri ta isa gun da take ta fyaɗe ta da ƙarfi sai ga shi ta dare gida biyu.

Ta yi hanzarin komawa gun Surayyah da take a gigice ta kama ta ta shigar da ita ƙofarta. Daidai za su shiga ta tarar da mijinta a ƙofa yana shirin fitowa don duba meke faruwa.

“Subhanallahi! Salame ke da waye? Me ya faru?” Ba ta dakata da yunƙurin shigar da Surayyah ciki ba sai shi ne ya raɓe ya ba su hanya.

Ta ce “Wallahi malam kunama ce ta harbe ta, Surayyah ce, ban san me ya fito da ita a daren nan ba.”

“Assha ko! Yi sauri ki zaunar da ita a ɗaure gun kafin dafin ya haura sama.”

Tambayarta aka yi ina ne harbin yake? Amma tsabar gigicewa ta kasa tantancewa, sai shi ne ya haska ya gano wurin a ƙwabrinta na ƙafar dama kusa da idon sawu, don haka cikin hanzari ya ja mayafin ɗaya daga cikin yaransa mata da yake kan igiya ya ɗage doguwar rigar tata ya ɗaure can sama kusa da gwuiwarta.

Samo mafici ki firfita mata bari na yi hanzarin na kirawo baba Maitawada, Allah ya sa bai riga ya kwanta ba.” Ya ja rigarsa da ke kan igiyar ya yi hanyar waje buzum-buzum yana ƙoƙarin zura kansa a rigar.

Can bayan mintuna goma sai ga sallamarsu a ƙofa sun shigo tare da baban. Bayan gajeruwar gaisuwa da ta shiga tsakaninsa da matar gidan ya kama ƙafar Surayyah ya yi mata tawada ya ƙara da ‘yan addu’o’in neman lafiya ya tofa a ruwa ya ba ta. Duk ƙyanƙyami irin na Surayyah sai ga ta ta shanye ruwan tas, azaba mai sa arne shiga masallaci. Wani garin magani ya ɗauko a cikin jakar fatar da ya ratayo a kafaɗa, ya ƙarbi ruwa ya kwaɓa ya saka mata daidai gun harbin.

Sannu a hankali ta ji sauƙi yana samuwa, nan Baffa ya yi wa matarsa umurni ta yi wa Surayyah shimfiɗar katifa a tsakar gidan su kwana tare a ga yanayin jikin nata kafin safe a garzaya da ita asibiti.

Haka ya sallami baba mai tawada bayan ya tabbatar masa da cewa in sha Allahu nan kusa za ta faɗi ya koma gida, ita kuma ta kwanta lamo ta rasa abin yi tana ta sauraren raɗaɗin ciwon yadda yake ratsa ta tana sakin salati haɗe da hawaye.

Sai can bayan mintuna 40 nutsuwa ta shige ta ta dawo hayyacinta sai a lokacin ne kuma ɗatatan zantukan Minal da na baabarta suka dinga dawo mata, zafin ne ya haɗe mata biyu ga tiririn ƙunar zuci ga na gangar jiki, wani ƙarin abin haushin ma da ta tuna cewa wannan hatsarin da ya same ta ma su ne sila.

Ƙwafa ta yi a ranta tana faɗar ‘Kun yi kashi gonar fara, da ni kuke zancen.’

Duk da cewa ba ta cika saurin ɗaukar zafi ba amma akwai riƙo, idan ka mata abu musamman na sharri ba ta mantawa amma tana yafiya wasu lokutan.

Washegari

Sai wuraren ƙarfe 7 na safe Baffa ya dawo daga masallacin da ya fita. Ya kalli Surayyah da ta yi ɗai-ɗai tana baccin wahala ya durƙusa yana tashinta a hankali yake bubbuga gefen filon da take kai. “Ke Surayyah! Surayyah!! Tashi.”

Idonta ta fara buɗewa a hankali ta sauke su a kansa. “Kin yi sallah kuwa?”

Ta gyaɗa masa kai alamar eh, sannan ta miƙe zaune tana murtsike ido da faɗar “Ina kwana Baffa?” 

“Lafiya qlau, ya jikin naki?” Ya tambaya yana ƙoƙarin duba ƙafar daidai wurin da ya ɗauren.

“Da sauƙi, sai dai zazzaɓi da na kwana da shi.”

“Allah ya ƙara afuwa. Ai kin yi sa’a ma abar ta faɗi da wuri. Yanzu ki tashi ki lallaɓa ki je gida, kafin ki ƙarasa zan kira babanku na sanar masa ya sa a raka ki asibiti. Ni kin gan ni nan haka na kwana ba ko sisi a jikina ai da na ba ki kin je tun da da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne.”

Murmushin yaƙe kawai ta yi ta yunƙura ta miƙe ta sanya hijabinta tana faɗar “To Baffa na gode, idan mama ta tashi a mini godiya.”

Tana gama faɗa ta bi hanyar barin gidan gandun nasu gaba ɗaya ba tare da ta komai can cikin gidan ba ma ballantana su san halin da take ciki, sanin komawar tata ba ta da wani amfani don ba wanda zai iya taimaka mata da ko ƙwandala a cikinsu. Shi ma Baffa Bashir ya yi taimakon ne a babin dole don kar labari ya tashi a ce a ƙofarsa abin ya faru amma bai taimaki ‘yar ɗan’uwansa ba.

 Kodayake wannan karon ta ga alamun tausayi a idonsa amma ta sani cewa ba wani tausayin da zai saka ya iya kashe kuɗinsa a wannan jinyar tata, hannun ‘yan dambe ne da shi ba ya ɓanɓaruwa, ba wai don ba shi da kuɗin ba ne kamar yadda ya faɗa.

A haka ta durfafi unguwarsu da ke maƙwabtaka da wannan cikin zafin zazzaɓi tana tafe tana tunanin yadda rayuwa take gwara mata kai da bango har ta isa ƙofar gidan nasu.

Da sallamarta ta tura ƙofar ta faɗa jiki ba ƙwari. Da mamanta ta fara cin karo ta fito daga madafa, maman ta zubo mata ido.

“Lafiya dai kika dako mana sakko haka?” Wuri ta samu a jikin bango ta raɓe tana mai kai wa zaune.

Ba abin da ta rage a abin da ya faru duk ta kwashe ta labartawa mamanta. Ashe duk a kunnen Abbansu da ke kwance a kujerar falon da take raɓe a bangonsa.

Wuf ya yi ya fito waje yana mata kallon sama da ƙasa, “Ina miki kallon mai hankali ashe ke ma sha ka tafi ce? Habah Surayyah! Minal ɗin duk nawa take da za ki kula ta bayan ke kin san komai lokaci ne, shi ne har za ki zuciya ki fito inda za ki cutu?”

Ita dai ba ta ce komai ba sai sunkuyar da kanta ƙasa da ta yi. Mamanta tana son yin magana amma sanin komai a kunnen maigidan ake yi sai ta yi shiru ta tamawa lokaci.

 “Shiga ciki ki buɗe loka ki ɗauki farasitamal ki sha zai kashe miki zogi, bari na karya na fita nemo kuɗin asibitin na ga ko za a samu daga nan zuwa yamma. In ba a samu ba ki fawwalawa Allah lamurranki…”

Ba ta iya cewa komai ba sai dai ta aiwatar da umurninsa, amma har a lokacin tana jin matuƙar ɗaci a ranta, ta sani wannan ba komai ba ne a cikin kalolin gorin da ake yi mata kan rashin aure, amma har yanzu ta kasa sabawa da yanayin. Sau tari ta yi ta ƙokarin hana wa kanta damuwa da hakan sai dai ta kasa, kodayaushe ɗacin dabam ne.

BANGAREN HALISA 

Tafe suke a cikin adaidaita sahu, ‘yanmata ne kusan su goma a ciki wata kan wata, wasu a cikin but sai shi ɗan sahun da yake tuƙi tafiya yake ya miƙi babban titi sosai Halisa da take zaune a gaba kusa da ɗan sahun ta hango wasu matasa guda uku a gefen titi suna tahowa ta gefen dama saitin inda take. Haka kawai ta kalle su sai da ta tabbatar sun gan ta ta ɗaga murya.

 “Ku masu tafiya uwaku!” Ta yi musu dawo-dawo da hannunta na dama, ai kuwa nan take ta hango fusata a fuskar na tsakiyar ta juyo da hanzari ta kalli ɗan sahun “Ƙara sauri, ƙara sauri malam.” Bai kula ta ba ya ci gaba da tafiyarsa kamar yadda yake yi.

Sauran ‘yanmatan da ke zaune a baya ne wasu daga cikinsu suka bushe da dariya “Gaskiya Apsara ba ki da mutunci, haka kawai ki kai zagi?”

Dariyarta ta ci gaba da yi bayan ta leƙa ta tabbatar ɗan sahun ya yi wa waɗanda ta tsokana nisa. Ganin shi fusataccen ya juyo zuwa direction ɗin da zai hango ɗansahun nasu ta ga kuma yana kallon gun, ta sake buɗe yatsu biyar ta aika masa da wani zagin tare da turo harshenta waje tana mai yi masa gwalo. Ganin ya duƙa da nufin lalubo dutse ta yi saurin mayar da kanta cikin adaidaitar tana dariya da riƙe ciki “Wallahi ya tunzura, shegiya ni.” Ta ƙara ƙyalƙyalewa da dariya.

Hannah da Shema’u da suka kasance matsorata a cikin tawagar su ne suka haɗa baki wurin faɗar “Wallahi idan kika tsokano wanda suka fi ƙarfinmu sauke ki za mu sa a yi mu yi gaba.” 

Shema’u ta ɗora da faɗar “Ba za ki ja mana salalan tsiya ba wallahi. Ko mu daina tafiya tare da ke.”

“Dallah can! Baƙaƙen matsorata, ba abin da zai faru, na ci dubu sai ceto.” Ta faɗa ta juya tana ci gaba da kalle-kallen gefen titi.

Har zuwa lokacin matuƙin bai ce musu komai ba. Can sun shiga wani titi mara hayaniya sosai ta sake hango wata matashiyar kirista da za ta kai shekaru 35, ta tsuƙe cikin riga da wando ta sha jan attach a kanta, ga wani uban gilashin kariyar rana (sunglass) baƙi da ta maka a ido tana tafe tana karairaya da rangwaɗa, ga wasu uban takalmi masu tsini da ta sanya.

Ai kuwa ta dinga nuna ta da yatsa tana dariya har da riƙe ciki ba tare da ta ɗauke idonta ba ta ce “Chau! Wannan wanka ya baje Hinda sai ina? Ah! Gaskiya kin haɗu kamar murfin masai.”

Hinda da ke zaune kan cinyar Hannah ta ce “Ah! Lallai kam wannan wanka da na zuba ba shi da ƙasa, bari! bari!!” 

Aka sake bushewa da dariya ana matsawa gaba kaɗan Aziza ta ce “Mai adaidaita idan ka samu wuri sauke mu. Ke kuma Apsara Allah ya shirye ki.”

Wasu suka firfito suka ba ma Aziza da Hadiza wuri suka sauka, suka ciro kuɗin su biyu suka haɗa masa naira ɗari suka miƙa masa.

Sai a lokacin ya samu zarafin yin magana “Gaskiya ɗaukar ‘yan makaranta ba riba. Wai yanzu a ce duk yawan nan naku hamsin-hamsin ce har unguwanninku?”

Halisa ta yi caraf ta amshe zancen “Ah! Zauna nan! Ai ma mun taimaka maka da muka iya ba ka hamsin-hamsin, kai ba ka san kuɗin ɗalibai kuɗin cizo ba ne ba sa ciyuwa?” 

Ya kalle ta kawai, can kuma ta marairaice “Ai ni yayana da za ka taimake ni da na ba ka talatin, ka gan ta ita kaɗai ta rage mini gaba da baya. Ka taimaka ka ji ɗan’uwana.”

 Harara ya so aika mata sai dai suna haɗa ido yanayin yadda ya ga ta yi wa fuskar ya ba shi dariya ya ma kasa magana sai washe haƙora kawai ya yi.

Ummu Intisar ce 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here