Home Siyasa Babu wani dalilin ci-gaba da tsare Nnamdi Kanu – Peter Obi

Babu wani dalilin ci-gaba da tsare Nnamdi Kanu – Peter Obi

5
0

Peter Obi ya sake nanata kiran a saki Nnamdi Kanu, yana mai cewa babu hujjar da ci-gaba da tsare shi, yana mai bayyana cewa ya kamata a bi hanyar tattaunawa wajen warware matsalolin ƙasar.

Obi ya bayyana haka ne a Washington, D.C., inda ya ce kalaman siyasa ko zagin shugabanni bai kamata a ɗauke su a matsayin laifi ba, yana mai jaddada cewa tattaunawa da masu korafi ita ce hanya mafi dacewa wajen warware rikice-rikice.

Ya kuma ce idan ya samu dama a mulki zai fi mayar da hankali kan tattaunawa da masu fafutuka domin fahimtar dalilansu da samar da mafita mai ɗorewa ga matsalolin da ke haifar da rashin jituwa a ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here