Home Rahoto Annobar Sanƙarau Ta kashe mutum 33 a Sokoto

Annobar Sanƙarau Ta kashe mutum 33 a Sokoto

3
0


Gwamnatin jihar Sakkwato ta tabbatar da rasuwar yara 33 kan cutar Sankarau da ta bulla a wani yanki na jihar.

Kwamishinan Lafiya na jiha Dakta Faruk Abubakar ya yi magana a ranar Laraba a lokacin tattanawa da uwayen kasa da hukumomin bayar da agaji ga yara don kaucewa cutar.

A ta bakin Kwamishina an samu zargin kamuwa da cutar guda 256 a kananan hukumomi Takwas tun sanda aka samu bular cutar a wata daya da ya wuce, Manema labarai sun rahoto kauyen Kurawa a karamar hukumar Sabon Birni an samu annobar bullar cutar Sankarau da mafiyawan wadanda suka kamu da ita yara ne kanana.Majiyar daga kauyen dake gefen lafiya ya sanar da wakilinmu cewa lamarin ya kazanta a ƙalla kullum mutum biyu ko uku suna rasa rayuwarsu, mafiyawansu daga shekara biyu ne zuwa 20.

Mafiyawan wadanda cutar ke samu suna rasa ransu ne kafin daukar matakin kiyon lafiya, don haka ake bayar da shawara ga magidanta su daina kwana a dakunan da ke rufe don kaucewa matsalar zafi.

An bayyana alamun cutar Sankarau jin ciyon gabobin jiki, yin amai(haraswa), masassara, da sauransu suna cikin alamar cutar Sankarau.

Dakta Abubakar ya tabbatar annobar cutar Sabon Birni ke da mutane da yawa 63 sai Wamakko mai mutum 60, Shagari 51 Tambuwal 33 sai Dange shuni 26 Kebbe 16, in da kananan hukumomin Bodinga da Gada da Kware nada biyu da daya da biyu. 

Kwamishinan ya fahimci mutane suna barin marar lafiya sai ya jikata a kawo shi wurin kiyon lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here