Home Rahoto ‘Yan sanda sun kuɓutar da mutane 32, sun daƙile harin ‘yan bindiga...

‘Yan sanda sun kuɓutar da mutane 32, sun daƙile harin ‘yan bindiga a Sakkwato

39
0

‘Yan sanda sun kuɓutar da mutane 32, sun daƙile harin ‘yan bindiga a Sakkwato

Rundunar ‘yan sandan Sakkwato ta yi nasarar kuɓutar da mutane 32 da aka yi garkuwa da su bayan an kawo ɗauki a harin da ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Maikujera ƙaramar hukumar Raɓah.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar DSP Ahmad Rufa’i ya fitar ya ce a ranar Talata da misalin karfe 8:30 na safe DPO na Raɓah ya samu bayanin ‘yan bindigar da suka  kai farmaki a wuraren Maikujera sun nufi gefen Zamfara tare da dabbobin da suka sace da mutanen da suka yi garkuwa da su, suna harbi kan mai uwa da wabi ga mutanen gari, bai yi wata-wata ba ya haɗa jami’ansa suka rufe duk wata hanya da ‘yan bindigar za su gudu da waɗanda suka ɗauko.

Jami’an tsaro sun yi bata kashi da ɓatagarin da suka fi ƙarfinsu sun gudu a daji sun bar dabbobi da mutanen da suka sato.

“Bayan sun gudu jami’an sun shiga daji in da suka ceto mutane 32 da aka yi garkuwa da su, maza manya shidda da mata 26 mafi yawansu yara ne ƙanana.”

Ya ce dukkan wadanda aka ceton suna karɓar kulawa ta magani kafin daga baya a miƙa su ga danginsu.

Ya ƙara cewa ‘yan bindiga sun kashe mutane huɗu kafin jami’an tsaro su kawo ɗauki a wurin, kan haka Kwamishinan ‘yan sanda CP Hayatu Hassan Shaffa ya yin ta’aziya ga iyalan margayan tare da ba da  tabbacin cigaba da ƙoƙari don ganin bayan ɓatagarin.

Rundunar ta ƙara bayar da tabbacin sai ta kawar da ɓarayin dajin da masu garkuwa da mutane, kan haka suke kira ga mutane su zama a faɗake da ba da bayanin duk wani motsi da ba su gamsu da shi ba ga jami’an tsaron mafi kusa da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here