Home Siyasa ‘Wa ke mulkin Nijeriya a yanzu da Tinubu da Shettima ke ƙasar...

‘Wa ke mulkin Nijeriya a yanzu da Tinubu da Shettima ke ƙasar waje?’ — Atiku ya tambayi fadar shugaban kasa bayan cikar kwanaki 21 Tinubu na hutu

15
0

‘Wa ke mulkin Nijeriya a yanzu da Tinubu da Shettima ke ƙasar waje?’ — Atiku ya tambayi fadar shugaban kasa bayan cikar kwanaki 21 Tinubu na hutu

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa da majalisar dokokin ƙasa su bayyana wa ’yan Nijeriya wanda ke riƙe da madafun ikon ƙasar, biyo bayan cikar kwanaki 21 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tafi hutu ba tare da miƙa mulki a hukumance ba.

Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce tafiyar shugaban ƙasa da mataimakinsa Kashim Shettima zuwa ƙetare a lokaci guda ya jefa ƙasar cikin rashin tabbas na shugabanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here