‘Yan bindiga sun yi ajalin mutane uku ciki har da mai taɓin hankali a Sokoto, sun tafi da 28 daji
‘Yan bindiga sun kai hari a garin Kagara da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto a daren Asabar, inda suka yi ajalin mutum uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 28.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba, yayin da ake ci gaba da neman mutanen da aka sace kawo yanzu.
