Home Rahoto ‘Yan bindiga sun saki Alƙali da suka yi Garkuwa da shi bayan...

‘Yan bindiga sun saki Alƙali da suka yi Garkuwa da shi bayan biyan kuɗin fansa a Kebbi

2
0

Rundunar ‘yan sandan Kebbi ta tabbatar da sakin Alƙalin babbar kotun jihar Kebbi Alƙali Faruk Hassan Bunza wanda aka sace a gidansa ranar 26 ga watan da ya gabata ƙaramar hukumar Bunza a Kebbi.

An sako shi yau Litinin 3 ga Agusta 2026 kamar yadda iyali da ma’aikatar Shari’a ta tabbatar da sakinsa, sai dai ba su faɗi yawan kuɗin fansar da suka biya ba.

‘Yan sanda sun nuna rashin gamsuwa da da tsayawa kan matsayarsu kan ƙin  biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga a duk sanda suka nema bayan garkuwa da mutum.

Bayan Alƙali ya koma gida ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro na ƙoƙarin ganin sun gano masu hannu a lamarin domin hukunta su.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar SP Bashir Usman ya fitar ya ce hukumar ‘yan sanda ta yi kira ga mutane su riƙa ba ta bayanai masu inganci, duk rahoton da mutum ya kawo sirri ne ba wanda zai sani shi ya kawo shi.

Hukumar ta gode kan haɗin kan da ake ba su a koyaushe, sun tabbatar da cewa za su cigaba da kare rayuwa da dukiyoyin jama’a a jihar Kebbi.

Hukumar ta bayar nambobi ga duk wanda ke son ba da bayani da zai taimakawa harkar tsaro ga su kamar haka: 09039911876 and 07081074395.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here