Da ɗumi-ɗumi: Gwamna Zullum Yace Bai taɓa cewa da wani Ya kama ‘Yan Tinubu Must Go ba
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce bai taba ba da umarnin kama wani mutum saboda kasancewarsa ɗan adawa ko kuma mai sukar gwamnatinsa ba.
Zulum ya bayyana hakan ne a Maiduguri ranar Juma’a, yana martani kan kamen wasu mutane da aka ce suna sanye da rigunan da ke ɗauke da rubutun “Tinubu Must Go”.
Gwamnan ya ce ya yi mamakin yadda aka danganta kamen mutanen da gwamnatinsa, yana mai cewa hankalinsa ya fi karkata wajen tabbatar da zaman lafiya da sake gina Borno bayan tashe-tashen hankulan Boko Haram.
Ya ce Borno ta kasance karkashin APC sama da shekaru goma, don haka ba ya ganin dalilin da zai sa ya bayar da umarnin kama magoya bayan wata jam’iyyar adawa saboda siyasa.
Sai dai rundunar ’yan sandan Borno ta ce mutanen biyar da aka kama ba wai saboda sanya rigunan “Tinubu Must Go” kadai aka gurfanar da su ba, tana zargin su da tayar da zaune tsaye, karya zaman lafiya, daba da kuma mallakar wasu abubuwan da ake zargin miyagun kwayoyi ne.






