Home Labarai Masarautar Katsina ta baiwa Gwamna Kebbi Sarautar Garkuwan Katsina Babba

Masarautar Katsina ta baiwa Gwamna Kebbi Sarautar Garkuwan Katsina Babba

16
0


Masarautar Katsina ta amince da naɗa Gwamnan  Kebbi, Nasir Idris, sarautar Garkuwan Katsina Babba, wato babban mai kare mutunci da martabar Masarautar Katsina.
An bayyana cewa an baiwa Gwamnan wannan sarauta ne saboda irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban ƙasa, da kuma wasu manufofi da shirye-shiryen da gwamnatinsa ke aiwatarwa waɗanda ake ganin suna da fa’ida mai yaɗuwa a faɗin Najeriya.
Wata tawaga da ke wakiltar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ce ta isar da sanarwar ga Gwamnan a ranar Juma’a. Tawagar ta ƙunshi Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Isa Alikankiya, da Yarima Abdulmumin Kabir Usman.
Yayin miƙa wasiƙar da ke ɗauke da amincewar Masarautar, Sakataren Sarkin Katsina, Alhaji Isa Alikankiya, ya ce Sarkin ya yi la’akari da gudunmawar Gwamna Nasir Idris ga ci gaban ƙasa, da irin manufofin jagoranci da yake aiwatarwa, da kuma rahotannin ayyukansa da hidimar da yake yi wa jama’a kafin ya amince da ba shi sarautar.
Da yake mayar da martani, Gwamna Nasir Idris ya bayyana wannan karramawa a matsayin babban abin alfahari, ba gare shi kaɗai ba, har ma da gwamnatin Jihar Kebbi da al’ummar jihar baki ɗaya.
Gwamnan ya ce kasancewar wata daga cikin manyan masarautun gargajiya masu tarihi da mutunci a Najeriya ta ga ya cancanci irin wannan babbar sarauta, abu ne da ya sanya shi matuƙar farin ciki, tare da bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki da ba zai manta da shi ba a tarihin aikinsa na hidimar jama’a.Gwamnan ya ba da tabbacin zuwa fadar ta Sarkin Katsina da kansa domin godiya da karamcin da aka yi masa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here