Home Rahoto Tinubu ya yi alwashin cire tallafin wutar lantarki a 2027

Tinubu ya yi alwashin cire tallafin wutar lantarki a 2027

15
0

Shugaba Bola Tinubu Yasha Alwashin cire tallafin wutar lantarki kamar yadda Ya cire tallafin man fetur idan Ya lashe zaɓen 2027

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta bayyana cewa za ta kawo ƙarshen tallafin wutar lantarki daga shekarar 2027, a wani sabon shiri da ake sa ran zai sauya tsarin biyan kuɗin lantarki a faɗin ƙasar.

Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauki matakin ne domin kawo ƙarshen tarin bashin da ke cikin ɓangaren wutar lantarki tare da tabbatar da tsarin da zai kasance mai ɗorewa.

A cewarsa, daga shekarar 2027 gwamnati za ta daina biyan tallafin wutar lantarki, amma ta ce hakan ba yana nufin za a hana ‘yan Najeriya samun wuta ba, sai dai za a mayar da hankali wajen inganta samar da ita.

Me hakan ke nufi ga ‘yan Najeriya?

Idan aka aiwatar da wannan shiri, ana sa ran masu amfani da wutar lantarki za su riƙa biyan kuɗi bisa cikakken farashin lantarki, lamarin da zai iya ƙara kuɗin wuta ga gidaje da ‘yan Najeriya

Wannan sanarwa ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman ganin yadda cire tallafin man fetur ya ƙara tsadar rayuwa a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here