Mutane Tara ‘yan asalin ƙaramar hukumar Yabo a jihar Sakkwato sun rasa rayukansu a hatsarin mota suna kan hanyar zuwa Lagos in da suke kasuwancinsu daban daban.
Ɗan majalisar dokokin jihar Sakkwato da yake waƙiltar ƙaramar hukumar Yabo Honarabul Abubakar Shamaki Yabo ya nuna baƙincikinsa kan faruwar lamarin da ya faru da matasa Tara a ƙarƙashin mazaɓarsa kuma ‘yan uwansa.
Mutanen sun haɗu da hatsarin ne a ƙudirinsu na neman halal a kasuwanci daban daban da suke yi a jihar Lagos du.
A saƙon ta’aziya da ya rabawa manema labarai a ranar Assabar Honarabul Shamaki Yabo ya bayyana hatsarin abu ne da ya taɓa zukatan mutane, ba Yabo kaɗai ba har da mazaɓar Yabo da Shagari da Sakkwato gaba ɗaya.
“Na yi alhini bayan da na samu wannan labarin na baƙinciki mun rasa matasanmu har guda Tara daga Yabo, wannan rashi ne ba ga dangi da iyalai ba har da mazaɓa baki ɗaya,” a cewarsa.
Ɗan majalisan ya fahimci yanda margayan ke son nema da ƙwazo, al’umma na baƙinciki rabuwa da su.
“Waɗan nan matasan sun bar gida da buri mai kyau na gina rayuwarsu ta inganta, a ƙoƙarinsu na nema muka rasa su gaba ɗaya kan hanyar zuwa Lagos daga Sakkwato,” ya ƙara da cewa.
Ɗan majalisar ya yi kira ga hukumomi da su kula da hanyoyi, haka ma akwai buƙatar matasa su riƙa neman aiki da sana’a a wuraren da suke rayuwa waton jihohinsu.






