‘Yan bindiga sun kashe mutane huɗu sun sace kayayyaki da yawa na miliyoyin naira a wani hari da suka kai a Gandi da Maikujera a karamar hukumar Rabah a jihar Sakkwato.
Mazauna garinn sun ce harin ya faru ne a ranar Juma’a da marece har zuwa ranar Assabar da safe, in da ‘yan bindigar suka kwashi dabbobi da yawa da kayan shaguna da Man fetur, abin da ya cilasta da yawan magidanta barin gidajensu.
Wata majiyar a Gandi ta ce maharan sun shiga garinsu ne karfe (7am) na safe Assabar bayan sun sace dabbobi da yawa a makwabtan garuruwansu.Ya ce ‘yan ta’addan sun so shiga cikin gidan man fetur domin su sata suka samu yana rufe.
“Sun nuna fushinsu in da suka lalata komai a gidan, sai suka je in da wani dan bunburutu suka saci mai da yawa,” a cewarsa
Ya ce daga nan maharan suka tafi rukunin gidaje da Qatar ta gina inda ‘yan gudun hijira ke zaune anan sun kashe mutum biyu kafin sojoji su zo wurin su kore su.
A garin Maikujera majiyar ta ce ‘yan bindigar sun shiga garin karfe 6(pm) na marecen Jumu’a sun yi yanda suke so tsawon awowi sun sace dabbobi da kayan shaguna masu yawa.Sun kashe mutu biyu a hain Lauwali Mika’ilu wanda aka sani da Aloko da Asma’u Nanuwa wadda aka fi sani da Bodi.Ya ce mutum uku suka yi wa rani da yawa yanzu haka suna asibiti don karbar magani.Majiyar ta ce akwai shagon da suka saci man fetur da Injin oyil da tsabar kudi za su kai dubu 500, a ranar an yi hasarar da za ta kai ta miliyan 250.
“Maharan sun sace shanu kusan 150 bayan kayan shaguna da kudi tsaba da lemun kwalba da gora(kayan sanyi)Ya ce ‘yan bindigar sun sato shanu daga ƙananan hukumomin Shagari da Boɗinga da Yabo da Tureta kafin su zo Maikujera, mutane garin suna cikin tsoro har wasu masu shagunan sun fara tunanin daina sa’ar su bari gaba ɗaya don gudun wata hasara a gaba.
Mutanen yankin sun nemi gwamnati da ta ƙaro masu jami’an tsaro yanda ake kai masu hari ba ƙaƙƙautawa an yi Narba da Alhamis da Jumu’a.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda DSP Ahmad Rufa’i bai kusa a lokacin da waƙilinmu ya kira shi don samun bayani daga wurinsu.






