Home Labarai Hisbah ta haramta mata zama gefen Keke napep a Zamfara

Hisbah ta haramta mata zama gefen Keke napep a Zamfara

7
0

Hukumar Hisba ta Jihar Zamfara ta sanar da haramta wa mata zama a gefen baburin adaidaita sahu, a wani mataki da ta ce an ɗauka domin ƙarfafa tarbiyya da bin koyarwar addinin Musulunci.

Arewa Updates ta rawaito cewa, Shugaban Hukumar, Sheikh Imam Umar Hassan Gusau, ne ya bayyana hakan a yayin hirarsa da gidan Rediyon Lead.

Ya ce hukumar ta gudanar da zama da shugabannin ƙungiyar direbobin adaidaita sahu domin wayar da kan mambobinsu kan sabon matakin, tare da tabbatar da sun bi dokar.

Shugaban ya ce, hukumar ta kuma tuntubi Majalisar Malamai domin samun shawarwari da goyon baya kan aiwatar da dokar.

Ya ce, za a ci gaba da wayar da kan direbobi da fasinjoji game da sabon tsarin, yana mai jaddada cewa mata ba za su riƙa zama a gefen adaidaita sahu ba.

Hisba ta ce, za ta haɗa hannu da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da bin wannan umarni a faɗin Jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here