Home Rahoto Masarautar Daura Ta Yi Magana Kan Bidiyon Sarkin Daura Da Baturiya

Masarautar Daura Ta Yi Magana Kan Bidiyon Sarkin Daura Da Baturiya

8
0

Masarautar Daura ta ce tana nazarin wani bidiyo da wata mata ’yar ƙasar waje ta wallafa a shafin Instagram, inda ta yi zargin cewa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya tattaba ta a wuraren da ba su dace ba a lokacin da ta kai ziyara fadarsa.

Matar, mai suna Mirka, wadda ke amfani da sunan @beduinqa a Instagram, ta wallafa bidiyon ne bayan kammala rangadin kwanaki 30 da ta yi a sassan Najeriya.

A cikin saƙon da ta haɗa da bidiyon, Mirka ta ce ta ji daɗin ziyarar da ta kai wurare daban-daban a Najeriya, inda ta haɗu da mutane da dama, amma ta fuskanci abin da ta bayyana a matsayin mummunan lamari a Daura, Jihar Katsina.

Ta yi zargin cewa a lokacin ziyararta fadar Sarkin Daura, an kai ta wani babban ɗaki inda suka zauna suna tattaunawa. A cewarta, sarkin ya riƙe hannunta, daga baya ya rungume ta, ya sumbaci kumatunta, sannan ya taɓa ƙirjinta ba tare da yardarta ba.

Matar ta kuma yi iƙirarin cewa ta nuna rashin amincewarta da abin da ke faruwa, amma sarkin ya yi dariya. Ta ce ta ɗauki bidiyon ne ta amfani da tabarau masu ɗaukar bidiyo na Ray-Ban Meta Glasses.

Mirka ta bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, 2026, amma ta jira har sai da ta bar Najeriya kafin ta wallafa bidiyon.

Da yake martani kan lamarin, Sarkin Labaran Daura, Usman Ibrahim, ya tabbatar da cewa masarautar na sane da bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilin Alfijir Radio, Usman Ibrahim ya ce suna nazarin bidiyon domin tantance sahihancinsa da kuma tabbatar da cewa ba a yi amfani da wata fasaha wajen ƙirƙira ko sauya shi ba.

Ya ƙara da cewa masarautar za ta fitar da sanarwa a hukumance bayan kammala nazarin lamarin.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani daga masarautar kan zargin da matar ta gabatar, kuma ba a samu wani ƙarin martani kai tsaye daga Sarkin Daura ba.

Alfijir Radio ta lura cewa, bai kamata a dauki zargin da matar ta gabatar a matsayin tabbataccen abu ba, har sai an samu cikakken bayani da martanin ɓangarorin da abin ya shafa. Haka kuma, yana da muhimmanci a saurari dukkan ɓangarori domin tabbatar da gaskiyar lamarin da kare mutuncin waɗanda abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here