Home Rahoto ‘Yan bindiga sun kashe jami’in ɗan sanda guda da ƙona mota biyu

‘Yan bindiga sun kashe jami’in ɗan sanda guda da ƙona mota biyu

6
0

‘Yan bindiga sun kashe ɗan sanda ASP Bala Waƙili a wurin musayar wuta tsakaninsu a ƙaramar hukumar Keɓɓe jihar Sakkwato.

Ɗan sandan yana aiki ne da ofishinsu dake ƙaramar hukumar.

Majiya ta ce maharan sun tafi garin Girkau da Zugu ne da ƙarfe huɗu na daren Litinin inda suka sace dabbobi masu yawa.

Ya ce jami’an tsaro da ke yankin sun tunkari ɓatagarin inda suka kore su a Zugu bayan shafe sama da awa ɗaya ana bata kashi.

“Jami’an tsaro sun farmaki ‘yan bindigar an yi musayar wuta domin ‘yan bindigar suna da yawa hakan ya sa suka samu nasarar kashe ɗan sanda ɗaya suka ƙone motar aiki biyu, ɗaya ta ‘yan sanda, ɗaya ta jami’an tsaron jiha,” a cewar majiyar 

Wani jami’in tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin har an yi jana’izar Marigayin a Talatar nan.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Ahmad Rufa’i ya tabbatar da harin ya ce jami’in ‘yandan da ya rasu kan aikin sa ne abin da ya same shi.

Ya ce an ƙara tura jami’ai a ƙauyukkan da lamarin ya shafa domin tabbatar da dawo da yanayin zaman lafiya.

Ahmad ya ƙara da faɗin hukumomi na aiki don ganin sun kamo maharan da kare aukuwar hakan a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here