Home Siyasa Dalilin da ya sa ‘yan majalisar dokokin Zamfara suka bar APC

Dalilin da ya sa ‘yan majalisar dokokin Zamfara suka bar APC

13
0

Dalilin da ya sa ‘yan majalisar dokokin Zamfara suka bar APC
‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara su  7 sun fice daga jam‘iyyar APC a cikin wata sanarwa da suka aika a mazaɓunsu daban-daban da manema labarai suka samu a ranar Lahadi.
Cikin wadanda suka fice ɗin har da na ƙaramar hukumar Talatar Marafa Honarabul Aliyu Ango Kagara, mahaifar daraktan janar na yaƙin neman sake  zaɓen Shugaban ƙasa Bola Tinubu a 2027, waton Sanata Abdul’aziz Yari.
Sauran ‘yan majalisun dokokin sun haɗa da Honarabul Bashar Aliyu a ƙaramar hukumar Gummi da Honarabul Nasiru Abdullahi a Maru da Honarabul Basiru Bello a Bunguɗu.Sai Mukhtaru Nasiru daga Ƙaurar Namoda ta Arewa da Ibrahim T. Tukur daga Bakura da Barista Bashir Abubakar Masama a Bukuyum da Faruk Musa Dosara daga ƙaramar hukumar Maradun.
Dalilansu da suka bayana a takardun da suka aikawa jam’iya a mazaɓunsu sun nuna kan matsalar tsaro da rashin haɗin kan da APC ke fama da shi a jihar da rashin adalci ya sanya suka yanke hukuncin barin jam’iyyar bayan sun yi  nazari da tuntuɓa a tsakanin magoya bayansu da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here