Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tambayi dalilin ci gaba da tsare tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na tsawon watanni bakwai ba tare da an ba shi beli ba.
Sanusi ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels TV, inda ya ce akwai hukumomi da kotuna da aka kafa domin bincike, gurfanarwa da hukunta masu aikata cin hanci da rashawa.
Sai dai ya ce yadda ake tafiyar da wasu shari’o’in na iya sa mutane su fara tambayar ko ana yaƙi da cin hanci ne kawai ko kuma akwai batun siyasa.
Sanusi ya ce: “Misali shi ne ɗan’uwana Nasir El-Rufai. Ya shafe watanni bakwai a tsare, an hana shi beli. Yanzu mutane suna tambaya, shin wannan yaƙi ne da cin hanci ko kuma yaƙin siyasa?”
A halin yanzu, El-Rufai na hannun ICPC yayin da ake ci gaba da shari’ar da ta shafe shi.
A wani sabon ƙalubale, El-Rufai ya maka ICPC a kotu yana neman Naira biliyan 10, inda ya ƙalubalanci yadda ake gudanar da tsare shi tare da zargin cewa an hana matarsa da ɗansa damar ganinsa.
Sanusi ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da bangaren shari’a da su bar hukumomin da aka kafa domin yaƙi da cin hanci su gudanar da ayyukansu yadda doka ta tanada.
—Mikiya
