Jam’iyyar ADC ta musanta hannu a zargin jifan ayarin motocin Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a birnin Abuja.
Jam’iyyar ta zargi jam’iyyar APC da ƙoƙarin ɗora wa ’yan adawa laifin fushin da jama’a ke nunawa sakamakon halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, cikin wata sanarwa da ya fitar, yayin da yake mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi wa jam’iyyar ADC.
