Home Siyasa 2027: ’Yan takarar gwamna 6 na NDC sun yi fatali da miƙa...

2027: ’Yan takarar gwamna 6 na NDC sun yi fatali da miƙa jagorancin jam’iyyar ga Babachir Lawal a Arewa maso Gabas

12
0

’Yan takarar gwamna shida na jam’iyyar NDC a jihohin Arewa maso Gabas sun yi adawa da naɗin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a matsayin jagoran jam’iyyar a yankin.

’Yan takarar daga Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe sun ce ba za su amince da Lawal a matsayin jagoran NDC na yankin ba, saboda an yi naɗin ba tare da tuntubar manyan jiga-jigan jam’iyyar a yankin ba.

A wata sanarwa da suka aikewa shugabannin ƙasa na NDC, sun ce matakan siyasa da suka shafi Arewa maso Gabas ya kamata su yi la’akari da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki da waɗanda ke aiki a matakin ƙasa.

Sun kuma bayyana damuwa cewa naɗin na iya shafar ayyukan jam’iyyar da shirye-shiryenta gabanin zaɓen 2027, tare da cewa ba su ga ƙarin tasirin siyasa da Lawal zai kawo wa jam’iyyar a yankin ba.

’Yan takarar sun bukaci jagoran ƙasa na NDC, Sanata Henry Seriake Dickson, da sauran shugabannin jam’iyyar su sake duba matakin tare da tuntubar su domin warware sabanin da ya taso.

Sun jaddada cewa matsayinsu na bai ɗaya ne kuma ba za su amince da Lawal a matsayin jagoran NDC na Arewa maso Gabas ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here