Home Labarai Kotu ta soke takarar Atiku a jam’iyar ADC

Kotu ta soke takarar Atiku a jam’iyar ADC

11
0

Kotu ta rushe shugabancin jam’iyyar ADC tsagin su Atiku Abubakar da Devid Mark, An tabbatar da Tsagin Nafi’u Bala Gombe.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kori shugabancin jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da suka ɗauka a madadin jam’iyyar.

Matakan da kotun ta soke sun haɗa da zaɓen fidda gwani da ya samar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, bayan kotun ta amince da ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa mai kula da Arewa maso Gabas, Nafiu Bala Gombe, ya shigar.

Nafiu Bala ya kalubalanci yadda kwamitin riƙon ƙwarya na David Mark ya karɓi shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa bayan murabus ɗin tsohon shugaban ADC na ƙasa, Ralph Nwosu, shi ne ya cancanci jagorantar jam’iyyar.

Kotun ta amince da buƙatunsa, tare da bayyana shugabancin kwamitin David Mark a matsayin wanda bai dace da doka ba. Ta kuma soke matakan da kwamitin ya ɗauka, ciki har da na zaɓen fidda gwani.

Sai dai jam’iyyar ADC ta bayyana cewa za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin a babbar kotun ɗaukaka ƙara.

Hukuncin ya zo ne kwana guda bayan Atiku Abubakar ya gudanar da babban gangamin yaƙin neman zaɓensa a Jihar Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here