Home Siyasa Tun farko zuciyar Obi ba ta kwanta da ADC ba – Babachir...

Tun farko zuciyar Obi ba ta kwanta da ADC ba – Babachir Lawal

2
0

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, ya ce Peter Obi bai taba nuna cikakken goyon baya ga jam’iyyar ADC ba tun bayan shigarsa cikinta.

Lawal ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise, kwanaki biyu bayan Obi da Rabiu Musa Kwankwaso sun fice daga ADC zuwa sabuwar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC), inda suka danganta matakin nasu da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’in da ke addabar jam’iyyar.

Ya ce Obi ya shiga haɗakar jam’iyyar ne a makare kuma tun daga farko ana shakkar jajircewarsa, duk da cewa an ba shi damar zaben sakataren tsare-tsare domin a tabbatar masa da gaskiya a harkokin jam’iyyar.

Lawal ya kuma zargi Obi da tsoron fafatawa a zaben fidda gwani, yana mai cewa yana son zama ɗan takarar maslaha ne kawai. Ya jaddada cewa ADC na ƙoƙarin tabbatar da adalci ga dukkan ‘yan takara a jam’iyyar.

Haka kuma, ya ce goyon bayan da ya bai wa Obi a zaben 2023 ba yana nufin dole ya ci gaba da binsa ba, yana mai cewa siyasar sa ba ta ta’allaka da mutum guda ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here