Home Rahoto ‘Yan sanda sun kama hatsabiban ‘yan bindiga biyu, sun kuɓutar da yaro...

‘Yan sanda sun kama hatsabiban ‘yan bindiga biyu, sun kuɓutar da yaro ɗan shekara 10 a Sakkwato

12
0

Rundunar ‘yan sandan Sakkwato a yinƙurin ta na kawar da ɓatagari sun yi amfani da wani bayanin sirri da suka samu kan wasu ɓatagarin da ke addabar jiha sun yi nasarar kama waɗanda ake zargi ciki har da wasu hatsabiban  ‘yan bindiga guda biyu, sun kuma kuɓutar da yaro mai shekaru 10.
‘Yan sanda sun tafi maɓoyar ɓatagarin a ƙauyen Tudun Doki a ƙaramar hukumar Gwadabawa in da suka yi nasarar kama  Abdullahi Buba, wanda aka fi sani da  “Osho,”

 A binciken da aka yi wa Buba ya sanar yana cikin ‘yan bindigar da suka addabi mutanen ƙananan hukumomin Gwadabawa da Kware da Gada, wanda ake zargin ya taimaki hukuma ta hannunsa aka samu kama wasu tare da tarwatsa gungun ‘yan bindigar gefensu.

A bayanin da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan DSP Ahmad Rufa’i ya fitar ya ce hukumar su ta karɓi koke hannun Sani Ibrahim dake garin Gidan Madi a ƙaramar hukumar Tangaza, cewar ɗan ɗan uwansa Sufiyanu Muhammad mai shekaru 10 ya ɓata sun neme shi ba su ganshi ba.

“Bayan saka idanu ‘yan sanda suka tuhumi wasu mutum biyu da aka gani saman babur ɗauke da wani buhu a ƙulle, da suka fahimci an biyo su ne suka bar buhun suka tsare da aka buɗe aka samu yaron ne aka yi garkuwa da shi an yi nasarar bai rasa ransa ba.”

Ya ce an gaggauta kai yaron asibiti  an duba shi har an sallame shi, bayan ya samu sauƙi ya ba da bayanin ɗaya daga cikin ɓatagarin ne ya tafi da shi ɗaki suka yi masa allura da ƙarfi suka sanya shi a buhu.”

An kama mutum ɗaya ya kuma karɓa laifinsa ana cigaba da bincike kan laifin”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here