Home Labarai Sokoto ta sanarda ranar da Rukunin Farko da Alhazzanta za su tafi...

Sokoto ta sanarda ranar da Rukunin Farko da Alhazzanta za su tafi Saudiyya

7
0


Hukumar jindadin Alhazzai ta jiha ta sanar da cewa a ranar Litinin 11 ga watan Mayu rukuni na farko na Maniyatan aikin Hajjin Bana za su fara tashi daga sakkwato zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin

Bana.Babban sakatare a hukumar Alhaji Ibrahim Umar ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a jiha.

Alhaji Ibrahim ya ce hukumar ta yi nasara karbo Biza ta mutum 2404 da suke da niyar zuwa aikin hajji da suka biya ga hukumar a Sakkwato.Haka ma ya ce dukkan maniyatan sun kamma binciken lafiya na wajibi da kasar Saudiya ta bukaci dukkan Mahajjata sai sun yi kafin shiga kasar.

Gwamnan Sakkwato Dakta Ahmad Aliyu ya nada Ministan Kwadago na Nijeriya Alhaji Muhammad Maigari Dingyadi matsayin Amiru Hajji  tare da wasu mutum 12 su ne  za su jagorancin tawagar Alhazan jiha a kasa mai tsarki.

Kwamitin an daura masu su yi shiri da tsari da kula don tabbatar da samun nasara aikin hajjin shekarar 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here