Home Labarai Jama’atul Nasril Islam ta nisanta kanta ga kalaman Shaikh Jingir 

Jama’atul Nasril Islam ta nisanta kanta ga kalaman Shaikh Jingir 

28
0

Jama’atul Nasril Islam reshen jihar Filato ta nisanta kanta da wani bayani da yake yawo cewa kungiyar ta mara baya ga kalaman da shaikh Sani Yahaya Jingir da ya yi kan kiristoci.

Kungiyar ta nuna bayanin  ba gaskiya ba ne a hukumance bai fito daga wurinsu ba an yi haka ne domin a samar da fargaba a tsakanin mabiya addinai a jiha Filato da wasu bangarori a kasa.

Bayanin wanda Sakataren yada labarai Gambo Hamza ya sanyawa hannu, kungiyar ta yi tir da rahoton in da aka ce “muna tare da Shaikh Jingir 100 bisa 100, JNI Filato jami’in yada labarai ya kare malamin musulunci kan kalamansa na sukar kiristoci.”

JNI ta ce bayanin bai fito daga wurinta ba don haka mutane da mambobinta sun fita batun zancen

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here