Home Labarai  Sokoto: Kwamiti kan rikicin Shaikh Lukuwa sun kammala aikinsu

 Sokoto: Kwamiti kan rikicin Shaikh Lukuwa sun kammala aikinsu

16
0

Sarkin Malaman Sakkwato Malam Yahaya Na Malam Ɓoyi shi ne shugaban kwamitin da gwamnatin jihar Sakkwato ƙarƙashin Dakta Ahmad Aliyu ta kafa sun kammala aikinsu kamar yadda ya tabbatar a hirarsa da Managarciya.

“Sai gwamna ya ba da lokaci sannan a je a miƙa  masa  rahoto, ba za mu faɗawa kafofin yaɗa labarai komai ba, har sai an miƙa rahoton ga gwamnati, ita ce za ta ba su bayani.

“A  halin da ake ciki kowa ba mu yi wa bayani ba gaskiya, sai gwamna ya ba da lokaci sannan za mu miƙa masa rahoto anan kowa zai ji abin da aka yi,” kalaman Sarkin Malamai.

Malam Murtala Bello Ɗa’a ɗaya daga cikin malamai a jiha ya ce “a bayanan dana samu masu inganci kwamiti ya kammala aikin shi a daidai sati biyu da aka ba shi, sai dai a lokacin da suka kammala aiki Gwamna baya gari shi ne dalilin da ya aka jira sai ya dawo a gabatar masa, da dukkan alama tun da ya dawo ya kwana biyu a gari, da alama saƙon an kammala aiki ya isa wurinsa.

“Yanzu al’ummar Sakkwato da kwamiti za su zuba ido su ga matakin da Gwamna zai ɗauka kan rahoton, a cikin adalci  tsakanin kowane ɓangare da shi wanda ake tuhuma da masu tuhumarsa.

“A fahimtar da nake da ita bayan mambobin kwamitin ba wanda ya san abin da suka zartar komai alaƙarka da su, domin faɗar za ta haifar da rashin sirri, da sanin matakin da gwamnati za ta ɗauka, zai iya haifar da wasu abubuwan da ba dole su kasance masu daɗi ba, abin da kawai za a jira gwamnati bayan ta gama nazari ta ɗauki shawara daga cikin wadda aka ba ta.

“Ina da kyakkwan zato gwamnati ba za ta yi saɓanin abin da kwamiti ya ba ta shawara ba, domin da zaɓinta ta yi kwamitin ta kuma amince da shi ta kuma ba su amana su yi abu tsakani da Allah, ba a tsammanin ta yi sanyi ko lungu kan abin da aka bata shawara,” a cewar Malam Ɗa’a.

Ɗaya daga ɗalibban Malam Musa Lukuwa waaton Malam Murtala Asada ya faɗi matsayarsu kan kwamitin ya ce “an yi kwamiti an ba shi sati biyu, yau sati uku ba labarin kaomai, ana son a ja abin ne a ce an hana su yin karatu da buɗe masallaci sai an ƙare siyasa, siyasa ta shiga cikin lamarin.” 

Sama da sati uku Gwamnatin Sakkwato ta ba da sanarwar kafa kwamitin a wata takarda da daraktan yaɗa labarai a fadar gwamnati Abubakar Bawa ya sanyawa hannu ya ce Sarkin Malaman Sakkwato Malam Yahaya Na Malam Ɓoyi ne shugaban kwamitin in da Barista Gandi Umar Muhammad ne Sakatare.

Sauran Mambobin kwamitin sun haɗa da Malam Muhammad Isa Talatar Mafara da Farfesa Mansur Ibrahim da Farfesa Mansur Ibrahim Sa’id da Malam Lawal Maidoki da Malam Bello Na Malam Ɓoyi da waƙili daga Izala Jos da Izala Kaduna da waƙili a Jama’atu Nasril Islam da waƙili a majalisar Sarkin Musulmi da waƙili a Tijjaniya da Ƙadiriyya da Kwamishinan ma’aikatar harkokin addinin musulunci.

 “An baiwa Kwamitin kwana 14 ya gabatar da rahotonsa.”

Ya ce Gwamnati ta buƙaci kwamitin ya gabatar da bayani mai zurfi kan matsayar Shari’a a bayanan da Malam Musa Lukuwa ya bijiro da su, a kuma baiwa gwamnati shawara kan abin da yakamata ta yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here