Home Labarai Sojoji sun kama dan leken asiri na ƙungiyar ISWAP a Borno

Sojoji sun kama dan leken asiri na ƙungiyar ISWAP a Borno

2
0

Dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun kama wani mutum da ake zargi dan leken asirin kungiyar ISWAP ne bisa zargin shirya kai hari kan sansanonin sojoji biyu a Jihar Borno kamar yadda jaridar TheCable ta rawaito.

An kama mutumin mai suna Muhammad Shuaibu ne a sansanin sojoji na Chabbol da ke karkashin Bataliya ta 212 bayan bayanan sirri sun nuna cewa ana shirin kai hari kan wasu sansanonin sojoji.

Rahotanni sun ce an kama wanda ake zargin ne yayin sintiri da sojoji ke yi a kusa da katangar kariya da ke kewaye da sansanin.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutumin da hannu a shirin kai hari kan Bataliya ta 199 ta rundunar musamman, wadda aka fi sani da Mosquito Camp, da kuma sansanin sojoji da ke Chabbol.

Majiyoyin soji sun ce wanda ake zargin ya amsa yayin tambayoyi cewa an shirya kai harin, tare da ikirarin cewa maharan na da niyyar ci gaba da shirin duk da kama shi.

Sojoji sun bayyana cewa kama wanda ake zargin ya bai wa jami’an tsaro damar kara tsaurara matakan tsaro a sansanonin da ake zargin za a kai wa hari.

Daga bisani an mika wanda ake zargin ga rundunar leken asirin soji ta 7 domin ci gaba da bincike, yayin da Operation Hadin Kai ke ci gaba da gudanar da ayyukan tattara bayanan sirri domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here