Raunin Rayuwa
Raunin Rayuwa
Raunin Rayuwa
PP 21
Shan gabansa Musa ya yi yana faɗar “To ba ta nan ai sai ka juya.”
Sororo ya yi yana kallonsa yana ta mamakin ɗaukar zafin na yayansa, shi dai bai ga abun fushi ba a duk cikin maganganunsa amma ba shi da zaɓi da ya fi ya juya salun-alun ya bar gidan tun da sauran mutuncinsa saboda haka ya bi shawarar zuciyarsa ya fice.
Bayan ya karɓi abincin ya je kitchen don ɗauko kwano ya juye abincin sai dai yana taka cikin ya dinga jin ƙarni yana bugo hancinsa ba shiri ya mayar da ƙafarsa ta cikin waje yana jan kakkauran tsaki “Mtsw!!”
Duk sai ya ji ƙyanƙyanin kwanukan gidan ya kama shi ya dawo cikin baranda ya shimfiɗa tabarma ya zauna yana cin sakwarar a cikin robar take-away ɗin da take yana daddana wayarsa.
Wata lamba ya kirawo aka ɗaga bayan gajeruwar gaisuwa ya sassauta murya sosai yana faɗar “An sake samun matsala fa a gidana, matsalar wannan karon ma har ta fi ta koyaushe, zan zo an jima ki sake raka ni gun nan mu karɓo abin da muka saba, amma ina so aba mu wanda ya fi duk na baya ƙarfi. Idan za ka sha giya gara ka sha ta dubu.”
Daga can ɓangaren matar ta fara magana “Sai ka zo, tun da ita ba ta jin magana za mu yi maganinta, wannan karon idan ta yi wasa mahaifar za mu lalata duka sai mu ga ta faɗi wai ƙwarƙwata ta kayar da ƙudan cizo.”
Daga haka ya kashe wayar ya ci gaba da tallafawa cikinsa bayan ya gama ya shiga ciki ya fesa wanka ya shirya tsaf cikin yadi mara nauyi kalar ruwan hoda ya fito hannunsa riƙe da makullin mota.
Har a lokacin bai bi ta kanta ba ballantana ya san halin da take ciki sai dai da wutsiyar ido ya hango ta tana gyara falon daidai inda ta ɓata ya wuce abinsa ba tare da ya ce mata ci kanki ba.
Bayan ta gama gyara ko’ina tsaf-tsaf ta kunna turaren wuta ta fesa turaren ɗaki wai duk don ɗakin ya dawo hayyacinsa, sai a lokacin kuma ta koma ciki ta yi wanka sosai ta darji fatar jikinta ta zuba ruwa har cikin gashin kanta da ta gama ta fito ta nemi ƙananun kaya riga da wando ta saka ta kishingiɗa kan gado tana neman mafita saboda azababbiyar yunwar da take ji ga ma ya sanya ta haras da duka taliyar da ta samu ta zauna a cikinta.
Can ta tuna ai suna ajiye maltina da madara a firij da hanzari ta miƙe ta je ta buɗe shi cikin sa’a akwai ragowar gwangwani uku na kowanne. Ai ba jira ta ɗauko guda bib-biyu ta je ta ɗauko dogon jug ta juye su a ciki sun yi sanyi har sun gaji ta juya da cokali ta kafa kai tana fatan Allah ya sa su zauna a cikin.
Tas ta zuƙe haɗin kafin ta janye kofin daga bakinta.
Tun da ya fita gidan bai dawo ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi na dare lokacin ta jima da yin bacci ga ba waya a hannunta ga shi kuma ta rufe gidan da makulli ta ciki.
Juyawa ya yi da sauri ya buɗe motarsa ya ɗauko makullan gareji ya buɗe ya sanya motarsa, a ta cikin ya rufe kasancewar akwai ƙofar ciki wacce za ta sadaka da zauren gidan, ta nan ya shiga gidan ya janyo ƙyauran ya rufe ya wuce ciki.
Sannu a hankali ya leƙa ɗakinta ya hango ta tana bacci ta bararraje kan gado iskar fankar chaji da ta kunna tana ratsa ta da kyau. Ya fi mintina biyu yana kallon fuskarta yadda take bacci cikin kwanciyar hankali sai ya ji hakan ya burge shi.
A zahiri komai nata burge shi yake tun daga fasalin fuskar, kalar fatar da yanayin dirinta can kuma ya ja dogon tsaki ya ɗauke kansa ya fice yana janyo mata ƙofar.
Ba komai ba ne ya sanya shi yin hakan sai don tuna yadda take ƙoƙarin lallai sai ta gusar da duk waɗannan abubuwan da yake ƙauna a tare da ita ta hanyar ɗaukar ciki da renonsa.
Babban dalilin da ya ƙara saka shi jin tsanar haihuwa kenan saboda yana gani tun a kan matan yayyensa da na abokansa da zarar mace ta samu ciki shi kenan sai ta fara lalacewa halittunta su fara sauyawa daga asalinsu, wata da ta samu ciki jikinta zai buɗe hancinta ya yi girma kamar an hura baloon wata sai ƙurajen fuska wata kumburin jiki wata kuma daga ranar da ta samu ciki ta ɗaura aure da ƙazanta sai kuma ta haife.
Tadodin ciki da nau’ukan laulayinsa da suka bambanta daga wata macen zuwa wata duk abubuwa ne da yake ƙyama kuma ba ya iya jure su.
Wata matar ma idan ba a yi sa’a ba da zarar ta fara haihuwa shi kenan asalin siffarta da ƙuruciyarta za su tafi ƙarfinta zai fara raguwa. Idan kuma aka haihu yayin reno za ta raba kulawarta gida biyu, ɗaya a kan jaririn ragowar miji, a ma fi yawan lokutan ma hankalinta sai ya fi karkata a kan ɗanta fiye da shi mijin.
To shi duka waɗannan abubuwan bai shirya musu ba a yanzu, ya yi aure ne domin ya more ƙuruciyarsa ba dalilin da zai saka ya yi wannan gangancin tun yanzu da bai haura shekaru 33 ba a duniya.
Shi mutum ne mai buƙatar cikakkiyar kulawa ba rabi da rabi ba, a hakan ma yana matuƙar cutuwa da zamansu to ina ga kuma ya ƙara ba ta waccan damar ta haihuwa?
Waɗannan su ne ire-iren tunanin da suke yawo a ƙwaƙwalwar Musa suka sa ya ƙara ɗaura ɗambar yaƙi da haihuwa a gidansa kuma har yanzu bai fara tunanin zubar da makaman yaƙinsa ba a ganinsa me aka yi da maza?
Aljihunsa ya laluba ya ciro maganin ya kalle shi da kyau yana murmushin mugunta ya mayar da shi ya koma waje ya tada inji sannan ya isa ɗakinsa ya rage tufafin jikinsa tare da watsa ruwa ya kwanta. Bai ma yi tunanin komawa ɗakinta ba sam ballantana ya kashe fankar chajin da ta kunna.
Washe gari ta tashi da zazzaɓi mai zafi da ciwon ƙasusuwa wanda hakan ba ya rasa nasaba da kayan sanyin da ta sha da kuma wankan da ta yi a jiyan duk da tana sane da cutarta ba ta son sanyi to sai dai a lokacin ba za ta iya haƙura da aikata waɗannan abubuwan ba saboda sun zama dole a gare ta.
Sai can ƙarfe takwas na safiya ya buɗe ɗakinsa ya fito fuskarsa washar-washar tana fitar da annuri.
Bai same ta a falo ba don haka ya kutsa kai cikin ɗakinta, can ya hango ta kan gado tana rawar sanyi da hanzari ya haura kan gadon yana rungumo ta zuwa jikinsa da faɗar “Subhanallah! Sweetheart ba ki da lafiya ne?”
Ba ta iya furuci ba sai gyaɗa masa kai da ta yi, cikin mayaudariyar murya ya fara magana “Sannu Sweetheart! Allah ya sawwaƙe, ko dai rashin lafiyarki ce ta motsa?”
Nan ma da kai ta ba shi amsa ya ajiye ta a hankali yana shirin sauka daga gadon ya ce “Bari na je ɗakina na kawo miki maganin, da ma a jiyan na biya ta chemist ɗin Ubaid na amso miki maganin amai saboda na ga jiyan kin wahala sosai, duka zan haɗo na kawo miki. A lokacin haushi kika ban shi ya sa na yi abin da na yi, amma ki yi haƙuri.”
Yana gama faɗa ya juya ya tafi ta harari bayan ƙeyarsa a ranta tana faɗar ‘Yaudara! Wato ka amso maganin da zai kashe ni. Ai yanzu kan mage ya waye.’
Can bayan mintuna biyar sai ga shi ya sake shigowa ɗakin hannunsa riƙe da sachet ɗin magani kala biyu da kofin ruwa a hannunsa ya ɓallo pracitamol guda biyu da wata ƙwaya ɗaya da take zargin ita ce mai cutarwar ya zuba mata a tafin hannunta ya miƙa mata kofi ta karɓa da ɗaya hannun, ya ƙure ta da ido yana faɗar “Oya madam Sha, kin san bana son ganinki a yanayi mara daɗi.”
Ba ta iya cewa komai ba sai kafe da ido da ta yi kamar mai karantar wani abu a kyakkyawar fuskar tasa.
ƁANGAREN SURAYYAH
Sannu a hankali kulawar Ahmad a kanta ta ragu saboda shi ma ba ya samun yadda yake so a gare ta, sai dai har a lokacin bai daina fafutukar nema mata magani da ɓatar da kuɗinsa a kan hakan ba bai kuma fasa ɗabi’arsa ta hirar banza ba duk da a yanzu ba da kowanne lokaci ba ne yake yin hakan sai jefi-jefi.
Ta yi iya ƙoƙarinta wurin ganin ta jure ta lallaɓa zama da shi a haka har zuwa wani lokaci, amma sai zuciyarta take tunzurata a kan ta rabu da shi kar ya lalata mata tarbiyya domin a mafiya yawan lokuta tana jin sheɗan ɗin da yake cikin zuciyarta yana zugata a kan ta biyewa Ahmad a yadda yake so tun da da alƙawarin aure a tsakaninsu kuma tana matuƙar ƙaunarsa fiye da zaton mai zato, to sai dai tsoron Allahn da ke zuciyarta ya taka rawar gani wurin hana ta amincewa da wannan sheɗaniyar shawarar.
Lokuta da dama takan zauna ta zurfafa cikin kogin tunani a kan halayen maza da yadda suke kallon mata a mahangarsu, so take lallai sai ta gano shin duka mazan duniya haka suke da sheɗaniyar zuciya? Haka suke kallon mata a matsayin kayan alatu kawai, shin irin waɗannan maganganun baɗala da ayyukan baɗala su ne soyayya a mahangar mazan zamani ko kuwa ita ce dai take rashin sa’ar haɗuwa da masu irin wannan ƙazamin tunanin?
Abin da ya fi komai ɗaga mata hankali shi ne wai har da Ahmad da ahalinsa suka yi wa shaidar kirki da nutsuwa har ake iƙirarin ya fi duka yara mazan danginsu kirki da nutsuwa, shi ma a baɗini yana da halin banza irin wannan ashe lulluɓin biri ya yi musu? Idan ire-irensu Ahmad da ake yi wa shaidar taƙawa da kiyaye haƙƙoƙin ubangiji za su faɗa tarkon zamani irin wannan to ina ga sauran mazajen da ba su kamo shi a komai ba?
Idan ta ji ta matsawa ƙwaƙwalwarta da tambayoyin da ba za ta samu amsarsu ba sai kawai ta miƙe ta ɗoro arwala idan lokacin nafila ne ta gabatar da ita sannan ta yi addu’o’i idan ba irin lokacin ba ne sai ta yi karatun Alqur’ani, waɗannan abubuwan ne ke samar mata da nutsuwa a duk lokacin da ta shiga irin wannan damuwar, haka ta ci gaba da lallaɓa rayuwa da Ahmad wani lokacin su yi daɗi wani zubin akasin haka, tana dai ci gaba da neman zaɓin Ubangiji.
A ɓangaren mama kuwa abubuwan suna nan kadaran-kadahan wani lokacin ta goyi bayan Aishatu wani sa’in kuma ta bi bayan Surayyah. Sai dai har a lokacin halin Aishatu yana nan bai sauya ba yanzu ma ta ƙaro wulaƙanci domin ba ta yin aikin komai a gidan sai dai ta kwanta ta shaƙi baccinta fiye da na awa shida idan ta tashi ta yi wanka ta ci abinci sai ta yi kallo a ranakun da ba ta da lecture domin tun a farkon wannan watan da ta fara zuwa polytechnic shi kenan ta tsame hannunta daga duk wani aikin gidan, mama kuwa ta goya mata baya da uzurin zuwa makaranta. Tun daga lokacin sai dai ta wanke goma ta tsoma ashirin.
Da yammacin ranar wata Alhamis Surayyah da ƙawayenta na kwaleji suka haɗu a wurin partyn auren ɗaya daga cikin coursemate ɗinsu, bayan sun fito daga wurin partyn Basira ɗaya daga cikinsu ta dube su. “Ai kuwa a nan unguwar gidan Halima yake fa.”
Dukansu idan ka ɗauke Surayya suka haɗa baki wurin furta “Ah haba! Da gaske?”
“Eh fa ana shiga nan bayan layin an zo gidan…” Ta nuna ƙarshen layin da suke hannun riga da shi tana ci gaba da faɗar
“Da ma kun zo mun biya mu samu ladar zumunci.”
Dukansu suka amince Surayyah ce kaɗai ta girgiza kai tana faɗar “A’a gaskiya ni dai bana son zuwa, kun san fa ba wani gaisawa muke da ita ba, ku ne kuka fi kusa da ita.”
Abin da ta faɗa ɗin gaskiya ne don kuwa ita Surayyar ba mace ba ce mai son hayaniya sosai, ko a lokacin da suke kwaleji ba da kowa take mu’amalarta ba duk da ba ta da wata tawaga ta musamman, kawai tana girmama masu girmama ta sauran kuwa sai dai gaisuwar nesa ba ta shiga sabgar da babu ita a ciki, Basira kuwa ita da Halima da Bahijja ‘yan team ɗaya ne. Su suna zumunci da Surayyah shi ya sa ma koda aka haɗa fitar gaba ɗaya suka biyo mata har gida don su tafi sawu ɗaya.
“Haƙuri za ki yi Surayyah ba jimawa za mu yi ba, kin ga ke ma kya samu ladar zumuncin.”
Ba a ƙin ga mutane wai an ce da ɓarawo gudu, tuno wannan azancin ya saka ta amince ba don ran ta ya yi daɗi ba ta bi bayansu suka rankaya gidan Haliman.
Tafiyar da suka yi ba ta fi ta mintuna biyar ba a ƙafa sai ga su a ƙofar gidan suka yi knocking aka buɗe musu, da farincikinta ta tarbe su suka gaisa. A falonta suka yi mazauni ta kawo musu ruwa, sai dai tun shigowarsu Surayyah take lura da kallon wulaƙanci da Haliman ke auna mata shi ya sa ko ruwan da ta ajiye musu ba ta kurɓa ba, jin ta take kamar kan ƙaya take zaune.
Ɗaya bayan ɗaya ta tambaye su yaransu da mazajensu da ke su duka biyar ɗin matan aure ne ita kaɗai ce budurwa a cikinsu.
“Hajiya Sury ke fa ya maigidan ko har yanzu ana ta zaman gwauranci?” Kamar daga sama ta tsinto muryan Haliman cike da isgili ta yaɓo mata tambayar.
Fuskokinsu ta bi da kallo sai ta lura duk sun yi diri-diri suna ji kamar a tula ƙasa a kansu don kunya.
Duk da alƙawarin da ta ɗauka na cewa duk wanda ya sake yi mata zance irin wannan za ta yaga rigar mutuncinsa sai ta ji ta ɗauke wuta ɗif, domin abu ne da ko kusa ba ta yi tsammanin jin sa a bakin wacce ta furta shi ba. To ita dai ta san ba wata doguwar alaƙa tsakaninsu ballantana ‘yar zama ko wasa ta ratso cikin lamarinsu.
Basira ce ta fara yin magana rai a jagule “Haba dai Halima, wace irin tambaya ce wannan? Gaskiya ba ki kyauta ba.”
Sai a lokacin ne ta samu ƙarfin gwuiwar miƙewa da mayar da martani “Gudun irin hakan ya sa na ce muku ba zan zo ba tun farko.”
Ta mayar da dubanta ga Haliman tana mai ci gaba da faɗar “Wannan tambayar ba ni za ki yi wa ba maƙagin kaɗɗararmu shi ne ma fi sanin amsa, shi ya tsara cewa za ki riga ni shiga gidan aure duk da na riga ki zuwa duniya. Kuma ma ai ko da goma ta lalace ta fi biyar albarka, gara zaman gidan da ƙaddararren aure irin naki, dube ki fa yadda kika koɗe kika lalace, dubi muhallinki. Ke a hakan har kina da bakin yi wa wani gori?”
Ta ɗan tsagaita sannan ta juya ta fuskanci Basira “Ni zan fita daga waje idan kun gama kwa same ni, ba ni da lokacin ɓatawa a nan.”
Halima baki ta sake galala tana kallon Surayyah ‘To ita wannan yaushe ta yi baki haka?’ ta raya a ranta fuskarta na bayyanar da takaicin maganganun da ta ji daga Surayyah.
“Wai ni Surayyah take faɗawa magana? Ban ma fi ta ba tun da ni gani ina zaman ibadar? Ita fa?
Basira ta miƙe tsaye fuskarta da annuri ta ce “Wannan shi ne idan baki ya san me zai furta bai san wanda za a mayar masa ba.”
Bahijja ma miƙewar ta yi tana furta “Ni wallahi burge ni ma ta yi da ba ta bar bashin magana ba, kin ga yanzu an yi one-one ta bakin Turawa, gobe sai ki tattauna magana kafin ki furta.”
Daga haka dukansu suka juyo suka bar mata gidanta saboda ba ƙaramin ɓata musu rai ta yi ba.
Da wannan ɓacin ran Surayyah ta nufo gida nan ma sai mama ta tarbe ta da wani zance daga shigarta gidan.
“Wai ni kam Surayyah sai yaushe ne Ahmad zai turo a yi muku baiko ne? Tun daga gaisuwar iyaye da neman izini da iyayensa suka zo shiru ake jinsa.”
Gyaɗa kai ta yi alamar ba ta da masaniya. Abin na damunta a zuci.
Fuska ba walwala maman ta ci gaba da faɗar “To gaskiya ki yi masa magana a san wacce aka ciki yau wata huɗu kenan da haɗuwarku ba wani labari a ƙasa.”
Da to kawai ta amsa ta yi ciki don sauya tufafin jikinta zuciyarta na yi mata nauyi.
Haƙiƙa ita kanta za ta so a yi neman nan, son samu ma daga neman a ɗaura auren a wuce wajen kowa ya huta don haka ta ƙudurce a ranar za ta yi masa maganar.
Yadda ta tsara haka ce ta kasance da dare ta kira shi da kanta ta yi masa tambayar sai dai ba ta samu gamsasshiyar amsa ba sai ce mata ya yi ta dai ɗan ƙara jira kaɗan akwai shirin da yake yi.
Ahmad?🤔 Wane shiri ne haka yake yi shi da yake iƙirarin ko a wata ɗaya ya shirya aure?
Ummu Intisar ce




