Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 18

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 18

5
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 18

Tana ganin ɓacewarsa ta miƙe ta tsince kayan da ta yi amfani da su ta mayar kitchen ta ɗauko tsintsiya ta zo ta tattare gun ta share ta gyara gun tsaf kamar ba shi ba ne ya kaca-ce a ɗazu ba. Carpet ɗin ta kwashe ta je ta baza shi a tsakar gida da nufin wanke shi idan ta samu sarari da ƙarfin aiwatar da hakan. Wannan dalilin ya sa ba ta ma lura da lokacin da ya fice daga gidan ba.

Daga can kai tsaye ta wuce kitchen ta ɗora tukunyar tuwo da ta miya a kan electric cooker mai guda biyu ta yi amfani da damar ganin akwai wutar lantarki.

Ba ta koma ɗakin ba a nan ƙofar madafar ta zauna jiran tafasar ruwan yayin da take tankaɗe garin masarar da rariya ta jiyo sallama daga ƙofar gida alamun ana shigowa. “Wa’alaikumus Salam ga ni nan.”

Ta amsa tana ɗaga murya daidai yadda za a jiyo inda take, ba ta yi yunƙurin motsawa daga inda take ba sai dai ta zubawa hanyar da take tsammanin bullowar wacce ta shigo gidan ido.

“Sannu da aiki anti amarya.” Zinat ta faɗa kasancewar sunan da yaran unguwar ke faɗa mata kenan tun lokacin tana amarya.

Ci gaba da tankaɗen ta yi tana faɗar “Yauwa Zinat, kwana biyu ba ki shigo gidan ba na yi miki wani laifin ne?”

‘Yar dariya Zinat ta yi tana ƙoƙarin tsugunnawa a kusa da Fatiman, “Ko ɗaya wallahi anti Amarya. Kwana biyun ne na yi busy kin san muna shirye-shiryen gama sakandire ne shi ya sa kaina ya ɗau caji. Yanzu ma karatun jarabawa nake Inna ta taso ni ta ce na zo na duba ko kina da kanwa ki sam mata za ta saka a miya ne an je neman ta sayarwa babu.”

Da ‘yar fara’arta ta amsa da “Ayyah ba komai, na ga ne da kina shigowa ko ba aiki ki taya ni hira ke da Rafi’a amma yanzu kun jefa mini ƙaton dutse kun bar ni a gida ni kaɗai kamar mayyah.”

Ta miƙe tare da ajiye farantin garin da ke cinyarta ta shige madafar tana faɗar “Bari na dubo miki.”

Can bayan kamar minti biyu ta fito riƙe da ɗan ƙullin farar leda da wata baƙar leda ƙarama da ke ɗauke da wasu ƙulle-ƙullen da ba za ka iya gane miye a ciki ba. Ido huɗu ta yi da farantin nata a hannun Zinat ta ɗauka tana taya ta tankaɗewar.

Murmushi ta sakar mata tana faɗar “Zinat kenan iyayen son aiki, wato ke ba dama ki tarar mutum yana aiki ko yaya ne sai kin taya shi.”

Ita ma Zinat ɗin da fara’a kan fuskarta ta ce “Kai anti amarya! Shaidar da za ki mini kenan?”

Da fara’a ta amsa mata da “Eh mana, ai an ce yabon gwani ya zama dole. Karɓi wannan ki kai ma Inna…”

Ta ƙarashe zancen tana miƙa mata ledojin, Zinat ta miƙe ta karɓa tana ƙare musu kallo, ta gane asalin saƙon da ta zo karɓa na baƙar ledar ne ba ta fahimta ba don haka ta kalli Fatima da alamun buƙatar ƙarin bayani a fuskarta.

Zama Fatiman ta yi a kan kujerar katako ‘yar zaman tsakar gida da ta tashi a kai tana faɗar “Wannan ragowar kuka, daddawa, baƙin yaji da kuɓewa da nake da su ne ki kai wa Inna na san za su mata amfani.”

Daga wannan furucin ba ta ƙara magana ba ta ci gama da aikin gabanta sai Zinat ce ta ce “Kai! Gaskiya anti amarya kirkinki yawa ne da shi, da ke da kyauta kamar 5&6 ne ba a iya raba ku, ke dai komai naki na bayarwa ne.”

Murmushi kawai Fatima ta yi don sai a lokacin ma ta tuna akwai wasu kayan sakawarta da suka matse ta kaɗan ta ware su za ta ba wa Zinat ɗin amma ta rasa me ya ɗauke mata hankali ba ta tuna ba, ko don Zinat ɗin ta kwana biyu ba ta shigo ba ne?

Sai kawai ta ɗago ta kalli Zinat tana faɗar “Ba komai wallahi, ai abin da ka bayar shi ne naka ranar gobe ƙiyama. Kin ga na ma manta akwai tufafin da na ajiye miki amma yanzu sun yi nisa gaskiya ba zan iya ɗaukowa ba, ko zuwa dare ne ki shigo ki karɓa don Allah.”

Cike da murna Zinat ta ƙara yi mata godiya sosai da sosai ta fice gidan ranta fari ƙal tana ji kamar an yi mata bushara mai daɗi.

Fitar Zinat ya yi daidai da lokacin da limamin masallacin bayan layinsu ya rangaɗa kiran sallar azahar don haka ta ajiye rariyar hannunta da ta gama zazzage garin ƙarshe ta ɗauke farantin zuwa kitchen ta ajiye ta buɗe ruwan tuwon ta duba ko ya tafasa sai ta ga saura kaɗan miyar ma haka don haka ta sake rufe komai yadda ya kamata ta fice zuwa ɗaki don sauya suturar jikinta da kuma ganawa da ubangijinta.

Bayan ta idar da sallar ne ta fito ta koma ga girkinta ta tarar ruwan ya riga ya tafasa don haka sai ta fara talgin tuwon nata sai dai me? Ƙamshin talgen ya fara tasar mata da zuciya nan take ta fara yunƙurin amai, kafin ma ta cire muciyar ta rufe tukunyar aman ya riga da ya taho cikin zafin nama ta kautar da kanta gefe ta shiga kelayo shi a kan katakon carbinet ɗin gefen tukunyar tata har wani daga ciki yana yin fallatsi zuwa ƙasan tiles na kitchen ɗin.

Ta shafe mintuna biyu a cikin wannan hali, duk iya ƙoƙarin da take don ta ga ta dakatar da aman hakan ya gagara saboda tukunyar tuwon da take a bude iska yana ɗebo mata ƙamshin talgen zuwa cikin hancinta, hakan na faruwa kuwa sai sabon yunƙuri.

Ta galabaita sosai kafin ta samu ya tsaya ta juya cikin ƙarfin hali ta kashe electric ɗin tana ƙoƙarin rufe tukunyar da murfi ta ji motsi a bayanta, a razane ta juya.

Mijin nata ne tsaye a bayanta yana bin ta da kallon ƙyama mai gauraye da tsana, jikinta ne ya hau ɓari har murfin tukunyar ya suɓuce mata ya faɗi ƙasa domin ta sani yau sai buzunta….

ƁANGAREN SURAYYAH

Kamar kullum maman ce ta tarbe ta tana kai hannu don karɓar ledar da ta shigo da ita, ba ta ma damu da tsayawa lura da yanayin fuskar tata ba.

Ita ma Surayyar da ke hankalinta ba ya gun sai kawai ta sake wa maman tasu ledar ta yi ciki don canza kaya zuwa waɗanda za su yi daɗin bacci, ta fito har za ta wuce maman ta miƙa mata ledar tana faɗar “Ga shi nan na ɗibar mana ni da A’ishatu, to da ke kin san ita daga gidan Sadiya za ta wuce can gidan gwaggwon taku ba za ta dawo nan ba sai safe, zan ajiye mata zuwa safe. Za ki iya tafiya da shi yanzu.”

Da to kawai ta amsa bayan ta karɓi ledar ta sa kai ta fice daga gidan zuciyarta na jin haushin yawan kama sunan Aishatu da mama ke yi. Ranar dai ba ta wahalar da ƙafarta ba a abin hawa ta je.

11:45pm tana zaune gefen katifar Minal ta saka ledarta a gaba tana tsintar alawar madarar da ke cikin pack na candies ɗin da ta zo da shi tana jefawa a baki wayarta da ke ajiye a gefe ta yi ringi.
Tun wancan satin sun riga sun shirya biyo bayan haƙuri da Minal ɗin ta ba ta shi ya sa ma ta ci gaba da kwanciya a kan shimfiɗar tata.

Wayar ta lalubo tare da ɗagawa ta ɗorawa a kunne tana faɗar “Assalamu Alaikum.” Cikin sanyin murya mai sanyaya zuciyar ma’aboci soyayya.
Daga can ɓangaren Ahmad ne ya amsa mata sallamar da zazzaƙar muryarsa mai kama da muryar mata, suka gaisa cikin yanayi mai kyau da a zahirance ya bambanta da na ɗazu kafin ya ce

“Ni ko matar officer na tambaye ki mana?”
Ta gyaɗa kai alamar eh kamar yana ganin ta, kafin ta amsa masa da furuci idonta ya sauka kan Minal da ke zaune tana fuskantarta ta yi mata ƙuri da ido ga fitilar Torchlight ƙarama a hannunta tana haska ledar.

Ta fahimci bin ƙwaƙwafi da kwaɗayi ne ke damun Minal ɗin wanda hakan ya so ya fusata ta sai dai ta yi kamar ba ta ga abin da take yi ba ta ba shi amsa da faɗar “Ina jin ka officerna, Allah ya sa tambayar da zan iya amsawa ce.”

Ya ɗan yi shiru na wani lokaci kamar mai yin nazari kan dacewar tambayar kafin ya furzo ta, can dai ya daure ya ce da ita.

“Ki yi haƙuri kar ki fassara tambayar, ina so ne na ce ko kin taɓa faɗawa matsalar iska a baya?”
Duk da dai ya yi dogon sharhi don son kautar mata da damuwa hakan bai hana ranta sosuwa ba don sai da ta ji ‘yar fargaba ta kamata. Ta buɗe baki za ta ba shi amsa kenan ta ji hannun Minal ya sauka a kan ledar candies ɗinta, ta yi hanzarin watsa mata idanu cike da mamaki. Sai dai yin hakan da ta yi bai dakatar da Minal daga ɗibar alawar madara guda biyu da aka fitar musu da shape mai kyau ba tana faɗar “Don Allah in ɗauka yayata?”

Harara ta banka mata a cikin a ranta tana faɗar ‘Daga baya kenan, wane izini za ki nema bayan aiwatar da abin da kika riga kika yi niyya?’

A zahirin gaskiya Surayyah ta yi wa raini tsanar da ba za ta kwatantu ba musamman a wurin waɗanda take gaba da su a shekaru, shi ya sa a duk lokacin da ta fuskanci an yi mata raini take saurin zafafa har ta ɗauki mataki a take.

Ba ta tamka Minal ɗin ba ta ci gaba da wayar da take yi. “Afwan! Ka ji ni shiru wani ɗan abu ne ya ɗauki hankalina. Iska kamar ya kake nufi? Ban gane ba.”

Sosa ƙeya ya yi kamar tana gabansa ya ce “Am! Ina nufin matsalar aljanu.”

Shiru na ‘yan daƙiƙu ya ratsa kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta buɗe baki cikin sanyin jiki “Me ka gani ne officerna?”

Ya so ya kanne ya nuna kamar ba komai sai kuma ya yi nazarin cewa yin hakan ka iya zama cutarwa gara dai ya sanar mata a ƙalla dai ta nemi magani, sanin cuta rabin waraka don haka ya cije ya ce “Ki yi haƙuri, gaskiya ya kamata mu tashi tsaye da neman magani domin a ɗazun nan na tsorata sosai da yanayin da na ganki a ciki. Batun gaskiya ma har yanzu ban gama daidaituwa ba.”

Ruɗani ya bayyana a fuskarta ta ce “Don Allah a wane yanayi ka gan ni?”

Ga abin bayar da amsa a inda aka san amsar kuma a inda za ta gamsar sai dai ba halin yin hakan, idan ya faɗa mata zai ɗaga mata hankali fiye da ƙima, yana ji a ransa cewa yin hakan ba aikin masoyi ba ne, masoyi da bayar da agaji tare da cikakkiyar kariya aka san shi ba sage gwuiwa ko tsoratar da abin son shi ba.

Don haka sai kawai ya ce da ita “Kina ji na matar officer? Ki kwantar da hankalinki ba wani dogon abu ba ne, amma tabbas kina buƙatar neman magani domin lafiyarki da neman tsari daga sharrin sheɗanu. Kin taɓa kasancewa a cikin wata alaƙar soyayya a baya?”

Ya jefo mata tambayar da ba ta taɓa ratsa tsakaninsu ba sai yau, jijiyoyinta sun gama sagewa a haka ta daure ta ba shi amsa da “Eh na yi sau biyu, har ma sadakina an taɓa biya auren ya watse aka mayar masa.”

Doguwar ajiyar zuciya ya sauke wanda tana iya jiyo hucinsa a wayar da ke daf da kunnenta kafin ya ce “Me ya raba ku?”

Wannan karon ta jima sosai cikin yanayin da ta kasa ba wa suna kafin ta sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta yi ƙoƙari ta tunkuɗe wani dutsen damuwa mai nauyi da ya danne mata zuciya da harshe sannu a hankali ta furta. “Idan za ka tsare ni da bindiga ban san dalilinsa na cewa ya fasa aurena ba. Kwatsam da rana tsaka na ji labarin daga bakin manyana. Abu ɗaya na sani muna yawan samun saɓani da shi don zai yi wahala mu rufe sati ɗaya ba mu yi faɗa ba, yana da wata iriyar hasalalliyar zuciya ne.”

Da yanayin damuwar da ya gauraya da tsoro ya ce “Uhmm! To kin ga wannan jawabin naki ya ƙara tabbatar mini da zargina, ba shakka su ne suke lalata zancen aurenki. Ba mamaki abin da na gani a cikin jikinki su ma sun ga irin shi….”
Tun bai ƙarasa ba ya tabbatar ya yi suɓul da bakan da ba ya fatan a ce ta ji, sai dai bisa ga rashin sa’a sai ya tsinto tambaya daga bakinta a rikice. “Don Allah me ka gani a jikina? Na shiga uku.”

Ganin duk ta firgice ya sa ya lallaɓa ya kwantar mata da hankali tare da kashe wayarsa.
Shi kaɗai ne a ɗakinsa kwance kan lafiyayyiyar katifarsa mai ƙwari ya mirgina yana sauke ajiyar zuciya, da a ce zai faɗa mata abin da ya gani da tabbas sai ta gigita don ba shakka a lokacin da ya kira ta ta fito yana cikin yanayi mai kyau da zumuɗin ganin ta, sai dai tun bayan furta kalmarta ta farko a gare shi da ya ɗago ya kalli fuskarta ya razana.

Ba komai ya razanar da shi ba face ganin idanunta sun ƙara girma fiye da ƙima, dogon hancinta ya ruɓanya asalinsa a tsayi haka bakinta ya yi tsini daga gaba ga wasu zara-zaran gashi kwance a gefen kumatunta tamkar biranya dalili kenan da ya tilasta masa ɗauke maganansa a kanta da ya sake ɗagowa a karo na biyu sai ya ga fuskar ta dawo asalinta na fuskar masoyiyarsa.

Har nutsuwa ta fara kwaranya cikin jikinsa ashe fa tsugunne ba ta ƙare ba, tana yin magana ya ji muryar na yi masa amsa kuwa da amo mai ƙarfi, daga baya kuma ya ji sautin na hawa da sauka, haka lokacin da ya zo miƙa mata kuɗi ya lura da wasu kwantaccin gashi a bayan tafin hannunta da zira’insa. Dalili kenan da ya saka garin kakkarwa kuɗin da yake miƙawar suka faɗi.

Tabbas yana tsananin ƙaunar Surayyah kuma ya ji a ransa zai yi iya ƙoƙarin da zai iya don taimaka mata ta fita daga matsalarta amma idan abin ya ta’azzara zai iya haƙura da ita domin ba amfanin baɗi idan ba rai, a haka ya wanzu yana ta karatun wasiƙar jaki.

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here