Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PP 20
Halisa gyara zamanta ta yi a gaban tvn da remote a hannunta tana kallo tare da saurarar drama da ake yi a gun. Ta dinga ƙyalƙyala dariya ta juya ta kalli Ige “Yanzu fisabilillahi Ige me ye laifin ɗan talikin nan don ya kira ki da kaka? Kin tsufa fa ina ga aƙalla kin kai shekara casa’in da tara a duniya. Kalli ‘ya’yanki nan su Baba Bello da inna Mariya kansu duk furfura…” Ta ci gaba da dariyarta ta juya fuskarta saitin tv don ci gaba da kallo.
Filon da ke ajiye kusa da ita kan gado ta miƙa hannu daga tsayen da take ta ɗauko shi ta bugewa Halisa baki da shi tana faɗar “Casa’in da tara? To wakiliyar Azara’ilu sannu da zuwa, don ke ina ga ba ma za ki jira har ya zo ba ke za ki kashe nin…”
Dariyarta ta ci gaba da yi ba tare da ta tamka ba don ita ma ta san ta taro match ba ta da ‘yan wasa, a dai yadda Ige take tsoron mutuwa duk wanda zai yi mata maganar tsufa ko mutuwa kai tsaye to ba za su taɓa shan inuwa ɗaya da shi ba.
Tana tsaka da ɓaɓɓaka dariya hankalinta na kan kallon da take kawai ta jiyo an warce remote ɗin da ƙarfi.
Ta ɗago tana kallon ƙarfin hali irin na tsohuwar sai ko ta gan ta tana cika da batsewa duk abin sai ya ƙara ba ta dariya, lamarin da ya ƙular da Igen ta isa gun socket ɗin jikin bango ta ɓalla madannin kashewa tun da ba za ta iya sarrafa remote ɗin ba.
Tsayar da dariyar Halisa ta yi ƙoƙarin yi kafin ta ce “Yi haƙuri ‘yar tsohuwa mai ran ƙarfe, ke kin san ina ƙaunarki ba zan so ki tafi yanzu ba sai kin ga jikokina.”
Ige ba ta kula ta ba ta koma kan gadonta cikin damuwa ta zauna ta yi shiru kamar ta zurfafa a tunani. Damar da Halisa ta samu kenan ta je ta sake kunna kayan kallon ta ci gaba da kallon tashar Bollywood saboda mutanen da ta fi ƙauna take amsa sunansu wato Indiyawa.
Ba ita ta ɗaga wa kallon ƙafa ba sai da aka kira sallar magariba nan ma sallar kawai ta yi ko abinci a nan gun rungume da kayan kallo ta ci sai da aka ɗauke wuta kayan kallon suka samu sassauci daga uƙubar da take gana musu. Ba saban ba…
Lura da ta yi cewa kamar Halisan ta ji ciwo a ƙafa saboda yadda take famar yin ƙara duk lokacin da za ta lanƙwasa gwuiwar hakan ya sa ta shiga babban gidan ta nemo Haidar ɗaya daga cikin samarin gidan da ta fi yarda da hankalinsa domin ya raka mata Halisa gidan malam mai kwacciya don ya gyara mata ƙafa.
Ba su wani jima ba suka dawo, Haidar ya shaidawa Igen Malam ɗin ya ce ba wani abu ba ne mai haɗari buguwa ce kawai, ya taɓa gurin kuma ya yi mata addu’a sai kuma umurnin yi mata ga shi da ruwan zafi na kwana biyu da ya bayar.
Tun a daren Ige ta aiwatar mata da gashin ta ba ta maganin rage raɗaɗi ta sha ta kwanta.
Washe gari ta tashi ta ji ta wasai ƙafar ba ciwon komai saboda haka sai kawai ta shirya don zuwa islamiyya duk da kuwa akwai sauran tabo a jikinta da ba ta so a gani, amma kuma zuwa a ranar yana da matuƙar muhimmanci a gare ta ko don ma saboda malam Mubarak da ba ta son yin missing darasinsa, haka kawai yake burge ta duk motsinsa a kan idonta yake yi har ya bar ajin nasu.
7:40am ta fice daga gidan, a ranar ita kaɗai ta tafi saboda Sa’adatu ba lafiya tana fama da zazzaɓi da mura mai zafi. Ita kuwa ba za ta iya haɗa tafiyarta da sauran yaran gidan biyu da suke makarantar tare ba don duk ba su cika shiri da juna ba, ta fi shaƙuwa da Sa’an saboda ita tana iya jurewa da shanye kwarafniyarta.
Da misalin ƙarfe sha biyu na rana daidai aka kaɗa gararrawar tashi daga makaranta duka ɗaliban suka yi ruu suka fito ta sake kamo hanya tinƙis-tinƙis ta yi nisa sosai a tafiyarta ta hango wani tsoho da aƙalla zai mai shekaru saba’in da biyar zuwa tamanin a duniya mai ƙwalƙwali kansa ba alamar gashi ko kaɗan irin mutumin da ake kira shagiri, saboda asali haka Allah ya yi jikinsu ba ya fitar da gashi.
Tun daga nesa walkiyar sanƙonsa da rana ke haskawa ta ja ra’ayinta ta fara dariya kaɗan-kaɗan tana yi tana nufar gefen hanyar inda yake zaune a keken guragu ashe fa a nesa ba ta ga komai ba kallo na kusa.
A gabansa ta ja ta tsaya tana ƙarewa randar cikinsa kallo huguma guda kamar mai cikin wata tara. Hannunsa guda biyu da ƙafarsa duka a shanye suke sun juye haka ma bakinsa ya karkace kaɗan. Fuskarsa kuwa sai ta ga kamar ta gwaggwon biri.
Halisa na yin arba da wannan bawan Allahn ta tuntsire da wata ƙatuwar dariya tana kafe shi da ido. Cike da ƙuruciya ta shafa cikinsa ta ce “Wai! Wannan ciki sai kace randa? Ga kuma ƙwalƙwali masha Allahu! Wannan tsaf za ka duba fuskarka a ciki ba ruwanka da madubi.”
Duk yadda bawan Allahn nan ya so juriya sai da ya kasa ya kalle ta cikin muryarsa da ba ta fita sosai ya ce “In sha Allahu yadda kika mini dariyar nan ke ma sai kin haɗu da jarabawar da ta fi tawa a daidai gaɓa mai matuƙar muhimmanci a cikin rayuwar ki.”
Zancensa ya ɓata mata rai matuƙa ta haɗe fuska ta fara magana cikin ƙarin hausarsu ta sakkwatanci da suke amfani da ita a kodayaushe “Ka ga abin ka can ga ƙwaryat shanka baba, in sha Allahu ni babu abin da zai samu na sai alheri. Haka ɗai!”
Tana gama furtawa ta murguɗa baki ta miƙe hanya samɓal don isa gida, a gaba kaɗan ta haɗu da Sadik ɗan shekara takwas ( yaron maƙotansu) ya biyo ta gun da kekensa ƙarama irin ta yara zai wuce.
“Sadik tsaya!” Ya tsaya kamar yadda ta buƙata sai kawai ta ce da shi “Ɗan ba ni ɗani don Allah.”
Ya gyaɗa kai alamar to ta ba shi umurnin sauka daga keken ita ta haye gaba ta ce ya zauna a baya.
Haka aka yi ta fara waina laulawar tana murna har da fitar da sauti da bakinta “Wee! Ti ti ti! Wee.” Wannan sautin take fitarwa daga bakinta tana danna horn ɗin keken ƙilin-ƙilin.
Haka ta ci gaba da yi ba ko kunya duk yaron da ta haɗu da shi a hanya sai ta yi cikinsa kamar za ta kaɗe shi, wanda ya gudu ya tsira wanda bai gudu ba ya ga ta kansa.
Ta kusa zuwa ƙofar gidansu kenan aka yi rashin sa’a Sadik ya saka ƙafarsa ba daidai ba ta shiga cikin kaca. Ya callara wata ƙara yana faɗar “Wayyo anti kin burge ni tsaya in sauka, wayyo!”
Ba ta lura da me yake son faɗa mata ba ta ɗauka yabo ne don haka ta ci gaba da nuna gwaninta ta hanyar waina keken tana faɗar “Mun kusa zuwa ƙofar gidanmu ai zan ba ka…”
Ba ta ƙarasa zancen ba sakamakon babbar ƙarar da ya saka da ta fi ta farko yana faɗar “Wayyo ƙafata!” Lamarin da ya janyo hankulan jama’ar da ke tsaye a kusa da gun suka yunƙuro don dakatar da ɓarnar da ke faruwa ita kuma a daidai lokacin ta saki hannun keken a gigice ba tare da ta kafe kariyar ba ai kuwa keken ta kifar da su ƙasa.
“Subhanallahi!” Mutanen suka haɗa baki wurin faɗa suna ƙoƙarin ɗauke keken da ta danne yaron, sai kuka yake aka samu dai da dabara aka cire ƙafar tasa daga cikin kacar, sai dai rashin sa’ar da aka yi ya riga da ya ji ciyo babbar yatsarsa ta yanke sosai har kana hango ƙashin yatsar jini sai ɓulɓulowa yake.
Ko da Halisa ta gama miƙewa idanunta suka sauka a kan ɗanyen aikin da ta aikata hankalinta ya tashi sosai jiki na kakkarwa ta kwasa da gudu ta yi hanyar gidansu a firgice.
A daidai ƙofar ɗakin Ige ta ci burki tana riƙe gwuiwoyinta da hannu biyu kamar mai ruku’i sai mayar da numfashi take.
Tana ɗago idonta suka sauka a kan ƙaton kwaɗon da ke ɓame a ƙofar. Idanunwanta suka ƙara fitowa tulu-tulu ta dafe ƙirji tana kallon ƙofar cike da tashin hankali ‘To ina wannan tsohuwar? Me ya same ta na ga ƙofa a rufe.’ Can wata zuciyar ta raya mata cewa ‘Wataƙila ba ta da lafiya ne aka kai ta asibiti.’
Tana yin duk waɗannan tunanukan ne saboda sanin cewa tun da ta yi wayo ba ta tuna lokacin da ta ga ƙofar nan a rufe da kwaɗo ba saboda Ige ba ta fita ko’ina a kodayaushe tana ƙofarta, iyakacin inda take zuwa daga cikin gidan gandun nasu sai kuwa idan ta fita ƙofar gida tarewa jikarta faɗa, ko kuma ta shiga maƙwafta jin ba’asi na taɓa mata jika da aka yi ko yin kiran ta idan ta ga ta jima a can. Duk kuma wannan dalilan ba sa saka ta rufe ƙofa.
Ta juya hankalinta na ruɓanya tashi, za ta fice daga ƙofar don shiga cikin babban gidan ta jiyo ko suna da wata masaniyar inda tsohuwar take.
Ta zo ƙofar fita kenan sai ga Ige ta shigo ranta wasai tana afa gurzajjen goronta a baki, haƙoran nan sun yi jajir.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke ta ruga ta rungume ta “Igena ina kika je ne haka? Kin tayar mini da hankali.”
Shafa kanta ta yi tana murmushi “Daga gidan mamanku nake.”
Ras! Ƙirjinta ya buga da ƙarfi ta ɗago idanunta zuwa ga fuskar Igen yayin da take cire hannunta daga jikinta. “Me kuma kika yi a can?”
Ba ta ba ta amsa ba sai ci gaba da lagumar goronta ta yi tana murmushi , kai tsaye ta wuce zuwa ƙofar ɗakinta ta kunto makulli a haɓar zaninta ta fara ƙoƙarin buɗe ɗakin ba tare da ta ba wa Halisar amsa ba, sai dai da iya yanayin fara’ar fuskarta kawai Halisan ta fahimci lallai koma me ta je ta shuko ba iri ba ne mai kyau.
ƁANGAREN FATIMA
A matuƙar fusace ya shiga kitchen ɗin yana ɗauke ta da wani gigitaccen mari da sai da ta ga taurarin wuya sun wulga ta dafe kunci kawai ta ƙame a gun, tamkar gawa sanye da tufafi haka ta kasance, tsakanin mamaki da kaɗuwa ba za ka bambance wanne ne alamarsa ta fi rinjaye a kan fuskarta ba.
A fusace ya fara sauke zafafan furucinsa. “Ke don iskanci ni za ki yi wa ƙazanta a cikin abinci? To bari ki ji ni dai Musa ba zan ci wannan abincin ba, kuma wallahi ba zan yi hasarar shi ba, sai kin cinye shi tas.”
Wannan karon tsoro ne ya maye gurbin wancan yanayin da ke kan fuskarta domin ba ta hango wasa a cikin idanunsa ba, haɗa hannu biyu ta yi ta durƙusa kan gwuiwoyinta tana roƙonsa.
Murya a raunane ta fara magana “Don girman Allah ka yi haƙuri yaya, wallahi ba da gangan na yi ba, ƙamshin tuwon ne sam ba na so. Idan ka ce sai na ci tuwon nan zan iya mutuwa ko kuma shi ya cutu.” Ta yi maganar tana nuna cikinta duk da ta san ba abin da yake so ba ne.
Ƙara ƙuluwa ya yi ya banke ta ta baje a ƙasa ya wuce abinsa ya buɗe lokokin kitchen carbinet ɗin inda suke ajiye kayan abincinsu ya tattare komai ya haɗa wurin ɗaya ya sanya makulli ya rufe ya cire makullin ya jefa a aljihu ya fice daga madafar ba tare da ya kalli inda take ba.
Jiki a sanyaye ta ja jiki ta miƙe tana goge hawayen da suka sauko mata ta bi bayansa, a tsakar gidan ta tarar da shi tsaye yana daddana wayarsa ta je gabansa ta ƙara durƙusawa a karo na biyu.
“Don Allah yaya ka yi haƙuri ka ba ni ko taliya ce na dafa, wallahi ba na iya cin kowanne abinci a yanzu idan ba ita ba.”
Bai kula ta ba ya ɗora wayarsa a kunne yana faɗar “Hello Hassan kana ji na? Yanzu-yanzun nan ka je Restaurant ma fi kusa da kai ka yo mini take-away na sakwara da miyar egusi da nama, sai ka haɗo mini da lemon kwali mai sanyi, kar ka ɓatan lokaci please yunwa nake ji kuma fita zan yi soon.”
Shiru na wani ɗan lokaci kafin ya sake yin magana cikin ɗaga murya “What’s your point? Is she your wife or mine?”
Ya sake yin shiru bayan sakanni goma ya sake cewa “Kuɗinka ko nawa? Ka ga ni bana son shisshigi da karambani ka je ka inda na aike ka kafin raina ya ɓaci.”
Ƙit ya kashe wayar ya ratsa ta gabanta zai wuce kenan ta riƙe ƙafarsa tana faɗar “Don Allah yaya…” Fisge ƙafar tasa ya yi da ƙarfi ba tare da ya juyo ba ya ce “Wallahi sai kin cinye shi tas kuma kin ji dai na rantse, ina falo ina jiranki je ki ɗauko.”
Kamar wacce aka yi wa turare ta samu kanta da miƙe hanyar kitchen, tun kafin ta shiga ta cire ɗan kwalin rigar yadin da ke jikinta ta ɗaure hancinta da shi sannan ta shiga ta rufe tukunyar tuwon, sai da ta fara gyara wurin ta kawar da kazantar da ta yi ta share kitchen ɗin tas ta goge sannan ta koma ta kunna electric ɗin don ruwan miyar ya sake yin zafi ta burga.
Ta koma kan tuwon ta kwashe shi a ledodi kamar yadda ta saba ta zuba a kula ta rufe, ta sa a ranta komai za a yi ba za ta zubar da abinci a wofi ba sai dai ta yi sadakarsa.
A tarbiyyar da ta samu zubar da abinci almubazzaranci ne ma fi girma, ‘wulaƙanta abinci ba kyau don watarana za ka iya nemansa ka rasa.’ Wannan kalamai ne da inna ke yi musu bitarsu lokaci zuwa lokaci sa’in da babansu ke raye.
Kamar yadda ya ba ta umurni haka ta aika ta cire ɗankwalin daga hancinta ta mayar a kai ta ɗebo kulolin ta dire masa a gabansa cikin rawar murya ta furta “Ya…yaya ga shi.”
A duk lokacin da ta kira shi da yaya sai ya ji gundura, yana jin matuƙar ba daɗi don dai ba yadda ya iya da ita ne, ta kasa wayewa. Sai dai a yau da ta da ambaci sunan ji ya yi kamar ya daka mata wuƙa….
Kallon da ake yi wa ɗanyen kashi ya bi ta da shi kafin ya ce “Oya matso ki fara ci.”
Ta yi rau-rau da ido sai hawaye, ganin tana ɓata masa lokaci ya sa ya daka mata tsawa a karo na barkatai “Kar ki ɓatan lokaci, ke nake jira.”
Ba yadda ta iya haka ta matsa ta zubo rabin malmala, hararar da ya banka mata ta sa ba shiri ta cikeshe malmala ɗayan ta zuba miya ta yi zaman tama-tela ta ɗauke farantin tare da rufe ido ta fara ci tana yatsina fuska.
Tun a lomar farko cikinta ya birkice amma ta daure ta afa ta biyu, ai kuwa tun ba ta gama wuce maƙoshi ba ta biyo ruwan aman da ya taho suka dawo tare.
Kawar da kansa ya yi gefe dama tun za ta fara ci ya naɗe ƙafafuwansa duka a saman kujerar irin ya shiryawa abin da zai biyo baya ɗin nan.
Ba ko ɗigon tausayinta a fuskarsa yana jin ta gama wannan, ya juyo tamke da fuska “Idan kin gama ai sai ki ƙarasa cin abincin ko? Ba ni da lokaci.”
Sosai ta kalli fuskarsa da galabaitattun idanuwanta ba ta iya yin magana ba saboda mamaki na tsantsar rashin imaninsa ya gama mamaye ta.
To amma ta karanto tsantsar gaskiyar a idonsa cewa ba fa da wasa yake yi ba. Ganin irin kallon za ki sani da yake aiki mata ya sa da sauri ta ci gaba da jefawa.
A daddafe ta kai loma ta uku kafin abun ya sake zuwa, sai dai duk abin nan da ake shi ko a jikinsa, tana gama haraswa zai sa ta ci gaba da ci sai da ya rage bai fi loma uku ba ta cinye malmalar da ya ga dai da gaske ta galabaita don faɗuwa ma ta yi kwance ta ɓangaren dama, ta ma kasa miƙewa zaune sai jan numfashi da mayarwa take.
Yana ganin haka ya tsallake ta zai shiga ciki kenan ya jiyo sallama daga ƙofar ya gane muryar sarai Hassan ne don haka ya yi saurin fita ya tare shi a tsakar gida domin ya san Hassan ba shi da kan gado sam, tsaf zai faɗo falon nasu. Shekararsa ashirin da shida amma har yanzu hankalin bai wadace shi ba ma.
A tsakar gidan suka yi kiciɓis ya miƙa hannu ya karɓi ledar saƙonsa ya juya zai koma ciki kenan ya ji Hassan ya biyo bayansa yana faɗar “Bari na gaisa da anti Fatima.”
Ummu Intisar ce




