Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 19

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 19

14
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

PP 19

Ita kuwa Surayyah bayan ya kashe waya hankalinta kasa kwanciya ya yi ta miƙe riƙe da ledar a hannunta ta je ɗakin kakarta ta adana ta cikin wata tsohuwar adakar ƙarfe da tsohuwar ke zuba tarkacenta saboda ji ta yi komai na duniyar ya fitar mata aka, ba za ta iya ci gaba da cin kayan maƙulashen ba, ta gano hakan ne dalilin jefa ɗan madara ɗaya a bakinta da ta yi bayan ta gama sauraren shi sai dai me? A maimakon zaƙi sai ta ji wani ɗaci-ɗaci wanda take da tabbacin ba a jikin ɗan madarar yake ba damuwar da take ciki ne ta haifar da hakan.

A maimakon ta sake fitowa wajen sai kawai ta karkaɗe shimfiɗar ɗaya daga cikin gadajen ƙarfen da suke ɗakin Innare ta haye tana gyara filon ta kwanta tana ci gaba da tufka da warwara, ta saƙa zaren wancan tunanin ta kwance wannan. ‘Idan hasashen Ahmad ya zama gaskiya ina ta dosa? Shi ma akwai yiwuwar a gaba zai gujewa aurenta kamar yadda Amir ya yi kenan? Hakan na nufin matsalarta ta baya za ta dawo sabuwa fil?’

Shirun da ta ji ba motsin kowa a ɗakin ya saka ta ɗago kanta daga filon ba tare da ta ƙarasa miƙewa zaune ba ta haska fitila saitin shimfiɗar Innare da ke ƙasan gado tana so ta ga fuskarta sai dai baya ta ba ta don haka ba ta da damar yin hakan, to sai dai shirun da ta ji ya ba ta tabbacin cewa tsohuwar ta yi bacci, su ko sauran jikokin ɗakin ta riga da ta san suna kwance a waje.

Komawa ta yi ta kwanta sannu a hankali tana furta “Oh Innare kayan Allah! Duk yawan gadajen da ke ɗakin nan ki rasa wurin kwanciya sai ƙasa?”
Ta ƙara haske saman ragowar gadajen biyu da suke kafe wayam ba kowa a kai, a ranta ta ce ‘Dole aljannu su ga wurin maƙalewa.’

Wannan zancen da ya halarto zuciyarta ne ya sa ƙirjinta bugawa kaɗan saboda ya tuna mata da kalaman Ahmad a kanta. Saurin kawar da zancen ta yi a ranta tana mai addu’ar Allah ya ba ta kariya ta ƙara lafewa a kan gadon a take baccin ya yi awon gaba da ita.

Can wuraren ƙarfe uku na dare ta farka a firgice tana kwarara ihu “Wayyo! Innalillahi wa inna ilahir raji’un!”

Ta furta numfashinta na hawa da sauka ta fara rarraba ido a cikin ɗakin lokaci ɗaya hannunta na laluben inda ta ajiye fitar torch da ke kusa da ita. Hannu na kakkarwa ta janyo ta ta kunna daidai lokacin da Innare ta miƙe zaune ita ma tana ƙoƙarin kunna tata fitilar tana furta “Waye a nan? Me ya faru kike mana ihu cikin dare?”

Da furucin da kunna haske fitilar kusan a tare ta yi su domin ba ƙaramar razana ta yi ba. A yadda ƙasa take a rikice ba tsaro ka ji ihu tsakiyar dare ai duk jarumtarka dole ka kaɗu ballantana kuma ita da ga tsufa, kusan shekaru 80 a duniya.

Cikin muryar tsoron da ya narke a cikin sautinta ta fara ƙoƙarin saukowa ƙasa tana faɗar “Innare ni ce Surayyah. Mafarki na yi mai firgitarwa, wasu shanu ne masu matuƙar girma da ƙiba ta zarta ƙima suka biyo ni…”
Tarar numfashinta Innare ta yi da faɗar “Ba sai kin faɗa ba, ki tashi ki yi sallah ki yi addu’o’i ki nemi tsari daga sheɗanu. Mummunan mafarki daga su ne.”

Shiru ta yi tana gaskata zancen Innare a lokacin ta riga da ta sauko daga gadon don haka a tsorace ta saɗaɗa ta yi waje bayan ta kunna hasken fitilar da yake yi mata jagoranci zuwa ga inda ta nufa.

Ta saba yin ire-iren waɗannan mafarkan amma ba wanda ya kai munin na yau, kuma ta jima sosai rabon da ta yi irin su don haka ta saka a ranta cewa zancen Ahmad ne ya tasirantu a ranta har ya haifar mata da wannan mummunan mafarkin.

Bayan kwana biyu komai ya daidaita tsakanin Ahmad da Surayyah, ya dawo da walwalarsa kamar a baya tuni kuma ya shiga nema mata magani a duk inda ya ji cewa ana samun magani mai kyau na lalurar da yake zargi gare ta. Har ɗaukar ta ya yi ya kai ta islamic chemist aka yi mata tambayoyi aka haɗa mata magunguna na sha, wanka da na hayaƙi, sai da ta kai hatta a cikin abincinta da ruwan shanta magani ne. Maganar soyayya kuwa zance yana ta ƙara yin nisa har ya miƙa maganar ga magabatansa suna shirin zuwa nema masa aurenta. Sai dai akwai wata ɗabi’a ɗaya da Ahmad ya tsira wacce Surayyah ba ta maraba da ita kuma ɗabi’ar ke ƙoƙarin rage armashin soyayyar tasu.

Watarana da dare kamar yadda suka saba yin waya a ranar ma ya kira ta sun fara hirarsu irin ta masoya cike da shauƙin ƙaunar juna, ranar Surayyah ta kashe masa zuciya kamar ya buɗe ido ya ganta a gidansa, a cikin irin wannan yanayin ne ta tsinci Ahmad da sauya layin hirarsu zuwa wacce ba ta dace ba. Tun da ta ji ya fara sauka daga layi ta fara yunƙurin dakatar da shi amma sai ta lura kamar ya gama ficewa daga hayyaccinsa don ba ya ma saurarar nasihar da take ƙoƙarin yi masa wannan dalilin ya sa ta kashe wayarta zuciyarta cunkushe da tsoro.

Shin shi ma Ahmad ɗin haka yake ko kuwa aljannun da yake yi mata iƙirarin tana da ne a kansa?
Ba ta ƙara tsinkewa da lamarin Ahmad ba sai da ya sake maimaita kuskurensa har sau biyar sa’annan ta tabbatar ba kuskure ba ne ɗabi’a ce.

Abin da ma ya fi damunta shi ne duk lokacin da ta yi ƙoƙarin bijirewa kalar hirar sai ransa ya yi matuƙar ɓaci ya kashe wayarsa kuma ya ja fushi da ita sai ya yi kwana uku bai neme ta ba sai dai ita ta neme shi.

ƁANGAREN HALISA

Juyowar da za ta yi haka suka haɗa ido su duka kowa ya ɗan fito da ido waje suka ƙame a gun kamar an dasa su, wani irin kallo suke watsawa juna wanda yake da bambancin ma’ana a duka ɓangare biyun.

“Ke ce a nan?” Ya furta da narkakken mamaki da ya saje da muryarsa.

A maimakon ta amsa masa sai ta ɓige da jefa masa tambaya. “Ni ce wa? Ɗan’uwa ka sanni ne?”

Ba wai don ba ta gane shi ba ne ya sa ta yi masa wannan tambayar kawai dai ta yi ne don kar ya ɗauka gani ɗaya da ta taɓa yi masa ya sama masa muhalli a zuciyarta wanda kuma haka ɗin ne tana dai yaudarar kanta ne ya sa take ƙaryata zuciyarta ta hanyar ƙoƙarin tursasawa kanta yarda da cewa kawai ya burge ta ne.

Murmushi ya sakar mata yana faɗar “Oh! Ba fa za ki gane ni ba ni ma na manta ne. Mu je ko?”

Da “Uhm! Kawai ta bi shi ta ɗale mashin ɗin ya fara tuƙi cikin farinciki da sake yin sa’ar haɗuwa da ita a karo na biyu, yana ta ba wa zuciyarsa ƙarfin gwuiwa da cewa wannan karon ba zai bari ta suɓuce masa ba.

Suna tsakiyar tafiya a kan babban titi ta hango Timaya daga nesa shi ma an goyo shi a bayan mashin ta ware murya iya ƙarfinta tana ƙwala masa kira “Timaya! Timaya nawa!!”

Ba zato ba tsammani Al’amin ya ji tana ƙoƙarin fasa masa dodon kunne, sai da ya ji kamar ya saki matuƙin ya dafe kunnuwansa saboda yadda ƙarar sautin ke barazanar fasa masa dodon kunne, amma ga mamakinsa sai ya fahimci kamar ta ma manta a inda take ballantana ta tuna tare da wanda take sai ci gaba da ihun take har sai da kunnuwan wanda take kiran ya zuƙo masa sautinta ya sa matuƙinsa ya yi hanzarin dawowa daga baya don ya ga mai masa wannan azababben kira.

Ita kuwa ganin sun juyo suna shirin dawowa baya ta fara buga kafaɗar wanda take zaune a bayansa murya cike da shauƙin murna take faɗar “Malam mai mashin ɗan rage sauri don Allah.”

Mamakin kan fuskarsa ya ruɓanya linkuwa a ransa ya ce “Wannan wace irin
Yarinya ce?” Bai ƙara cika da mamaki ba sai da su Timaya suka ƙaraso saitinsu ya ga ta shirge shi da hannu a kafaɗa tana faɗar “Shegen bisa! Da ma rai kan ga rai in ji talaka da ya ga tsire?”

Ya tuntsire da dariya yana furta gani kuwa a arha kamar dankali a faranti.

Al’amin ya kalli fuskar wanda take ta kira da Timaya yanayin sumar kansa da baƙaƙen leɓɓansa sai ya ga ya yi masa kama da tsagerun unguwa ‘yan abusa don haka ya ƙara shan jinin jikinsa, ya ci gaba da tuƙinsa su ko suna bin su kafaɗa da kafaɗa tana ci gaba da hira da Timaya tana kai hannu tana dukansa kamar za ta faɗo daga bayan abin hawan gabaki ɗaya ta ƙi zama kurum.

Ganin tana ƙoƙarin sakawa su yi hatsari ya sa nan da nan ya ji haushi mai haɗe da kishi ya turniƙe shi bai san lokacin da ya buɗi baki da ‘yar fusatacciyar murya ba. “Ki nutsu don Allah ko in sauke ki a nan don na ga alamar kin ji sauƙi.”

Za ta yi magana kenan ta ji yo Timaya yana faɗar “Apsara wutar kyau, wa ya mauje miki fuska haka? Kin ga yadda ta kumbura kuwa? Gaskiya kin daku Allah ya sa ba yayankun nan ba ne…” Ya ƙarashe zancen yana gumtse dariyar da take ciyo shi.

Ba ta bari ya kai aya ba ta fara magana cikin ƙuluwa “A inji aka markaɗa ni.”
Ta mayar da akalar zancen ta ga wanda suke tare “Yi haƙuri malam, na daina ƙara sauri mu je.”

Ba ta sake kula Timaya da ke ƙoƙarin ba ta haƙuri ba a ranta ta ce ‘Wannan gayen ni zai buɗewa aiki? Za mu gamu ne wallahi sai na masa mugun yarfi, da ni yake zancen.’ ta yi ƙyacci.

A daidai ƙofar gidansu Al’amin ya sauke ta ta jima tana yi masa godiya ba don komai ba sai don ta ba shi damar da zai tambayi lambar wayarta ko sunanta ko abun da ya yi kama da haka, domin an ce idan ka ga kare yana sansana takalmi to ɗauka zai yi.

Sai dai abin da ba ta sani ba wannan karen ya sansano wani abu dabam a cikin takalmin da ya sanya shi ya fara shakkar ɗauka. Ganin baya da niyyar cewa wani abu sai ƙoƙarin tayar da mashin ɗinsa da yake yi kuma fuskarsa ba tausayi da fara’a kamar da farko don ko Allah ya ƙara afuwa bai ce mata ba, hakan ya sa jikinta ya yi sanyi qalau ta juya ta tana ɗingisa ƙafa ta shige gida ba tare da ta gano inda ta kwafsa ba.

Tana shiga gidan ta tarar an kawo nepar yamma don shida ta gota a lokacin. A ɗaki ta tarar da Ige tare da wani matashi da ba ta san ko waye ba yana ƙoƙarin saita musu kayan kallo a jikin bangon ƙofa ta ciki.

Farinciki ya bayyana a fuskarta ya lulluɓe damuwar da ta shigo da ita da fara’a sosai ta fara magana “Ige yau TV ake saka mana? Kuma namu ne?”

Tsohuwar ba ta kalli fuskarta ba har a lokacin hankalinta na kan aikin da mai gyaran ke yi ta ba ta amsa “Eh ‘yar cakwaina, saboda ke na saka Belloti ya sayo mana shi ɗazu aka kawo bayan kin fita. Jiya ba kin je kallo ƙofar munafukar matar can ta babanku ba shi ne Shafa ta miki wulaƙanci?”

“Eh wallahi Igena ashe fa ba ki manta ba. Kin gama na huta da yin doguwar tafiya zuwa gidan Ɗan’indiya don kallon fim ɗin mutanena.” Ta yi zancen cike da farinciki tana rungume kakar ta ci gaba da faɗar “Ina sonki Igena. Allah ya bar min ke.”

“To ki cika ni kar ki karya ni. Kallon indiyawa kuma yanzu sai kin gaji su ne nan duk na ce a saita mana tashoshinsu ai….”

Sauran zancen ne ya maƙale a ƙasan maƙogwaronta a lokacin da idanunta suka sauka a kan fuskar Halisa da take a kumbure suntum ga kwanciyar jini a gefe da gefen fuskarta don a lokacin har ta sake ta tana ‘yan raye-rayen murna. Hannu ige ta kai ta cafko hannunta na dama da nufin matso da ita kusa sai ta ji ta buga ihu tana “Ah! Wayyo hannuna zafi.”

Da hanzari ta sake mata hannun rai a ɓace ta ci gaba da dudduba jikinta tana ƙanƙance ƙananun idanunwanta.

Murya da tashin hankali ta furta “‘yar cakwai! Waye ya miki wannan ɗanyen aikin?”

Murmura baki Halisa ta fara yi kamar za ta yi magana sai dai ba ta son yin maganar don ta san abin da faɗar gaskiyar ka iya janyowa. “Don ubanki Halilu ki ban amsa, na ce Murja ce ta miki haka?”

A diririce take kallon tsohuwar da mamakin zagin da ta banka mata, lallai yau ran mata ya ɓaci, ba ta da zaɓi face ta faɗi gaskiyar da take fatan ɓoyewa don a yanayin da ta ga tsohuwar ta tabbatar mata idan ta cika gardama har hannu za ta iya saka mata. Ita ko soyayyarta da lafiyar jikinta ba ƙarama ba ce shi ya sa cikin rawar murya ta kwashe komai da ya faru a can gidan ta faɗa mata sai dai ta ɓoye cewa uwar ta saka ta wankin mai yawa don kuwa tasan faɗar wannan zai iya fin komai muni.

Da fusatacciyar murya ta fara sauke kalamanta “Lallai Murja ta rungumo transformer…”
Sai kuma ta yi shiru kamar wacce aka dakatar da masarrafi, da alama ta ƙume daɗinta ne. Halisa na jira ta ji wanne mataki kakar tata za ta ɗauka a kan mahaifiyarta duk da ba za ta so hakan ba, amma sai ta ji shiru kamar ma Ige ba ta da niyyar sake yin magana. Wani sanyin daɗi ta ji yana ratsa ranta lokacin da ta tsinto muryar Igen na faɗar “Allah ya sawwaƙe, ki sha magani saboda tsamin jiki.”

Da amin kawai ta amsa cikin rashin kula da dabara ta zauna a gaban tvn a ƙasa tana sake yar ƙara kaɗan dalilin ciwon da ta ji a gwuiwarta yayin zaman, a daidai lokacin da mai gyaran ya juyo ya kalli Ige “Kaka an gama, ni zan…”

Ba su yi aune ba suka jiyo sautin Ige cikin alamun rigima da son juye zafin a kansa tana faɗar “Da ni ma aka yankewa ƙasa cibi ƙarewar tsufa, wato kai har ka hango ƙabarina ko?”

Sororo matashin saurayin ya yi yana kallon ta ‘To wai miye aibu a cikin kalamansa? Don ya kira ta da kaka da zimmar girmamawa sai cibi ya zama ƙari?’

Yana nan yana batun zuci ya sake jiyo muryarta tana faɗin “Wallahi ka yi ta kudinka, don ƙwandalata ba zan ba ka ba sai dai ka je can wurin Belloti ka karɓa. Fura mai daɗin da na yi niyyar ba ka ma na fasa.”

Shi dariya ma abin ya so ba shi lokacin da yake kallon fuskarta ta haƙiƙice tana surfa masa faɗa sai kawai ya gyaɗa kai ya fita a ransa yana faɗar “Ba ni nakar zomon ba ko rataya ma ba a ba ni ba.”

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here