Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 12

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 12

14
0

Na 

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 12

Ta tsorata sosai da hakan don ita a tunaninta ko ba shi da lafiya ne, don haka a firgice ta je gun kakarta ta iske ta tana taɓa ƙailula wuraren ƙarfe goma sha ɗaya na safe da ke  ranar ba ta je makaranta ba ta tashi da ɗan zazzabi a jikinta.  Tsayawa ta yi a gefen gadon tana ɗan bubbuga ƙafar kakar. Tsohuwar ta yi firgigit ta buɗe ido tana furta “Muhammadu ya Rasulullahi!”

Ita kuma ta ce “Sallallahu alaihi Wasallam”

Ige ta sauke idonta cikin na Halisa tana yi mata kallon ƙurilla fuskarta na nuna tsantsar takaici. “Me ye haka kuma ‘yar cakwai? Wace irin masifa ce a ce da wayonki ma ɗan baccin nan ba za ki bari na yi ba. Su Affam su yi ke ki yi? Don Allah sai yaushe za ki girma ne?”

Turtso baki ta yi gaba cikin shagwaɓaɓɓiyar murya ta fara magana “Ba maganar yaushe zan girma ake yi ba, sadakar ɗari biyu za ki ba ni in saka kati zan kira Hayat na ji ko lafiya sati biyu bai kira ba.”

“Yanzu don Allah saboda ɗan wannan abun ne za ki tashe ni? Ba ki san inda nake ajiye kuɗi ba ne?” Ta kalle ta da takaicin da ya ninku a fuskarta kamar za ta kai mata duka.

“Ai kin san ni ba na ɗaukar abin da ba a ba ni ba. Salon ma na ɗauka ki ishe ni da mita ki ce na taɓa miki kuɗin goro? Ai gara dai ki ba ni da kanki.”

Girgiza kai Ige ta yi tana miƙewa zuwa wurin komatsanta “Gaskiya ‘yar cakwai kin zama tuwon niƙa mai cika ciki. Ina dalilin wannan fitinar, yana can yana hutawarsa ke kin ɗaga hankalinki a nan kin hana ni sukuni.” Daidai nan ta ɗaga wani kwano daga cikin jeren kwanukan da suke ajiye kan wani dogo faffaɗan jan katako mai ƙwarin gaske da ke manne da bangon da ke fuskantar ƙofar shigowa ɗakin. A cikin kwano na kusa da ƙasan ta ciro cukurkuɗaɗɗiyar ɗari biyu ta miƙa mata tana faɗar “Ga shi sai ki sake mini mara na yi fitsari.” 

Kallon kakar tata ta yi ta kuma kalli tsohuwar ɗari biyun kamar za ta yi magana amma ba ta cikin yanayin son doguwar magana shi ya sa kawai ta karɓa. Sarai kakar ta san cewa ita fa ba ta son mu’amala da tsohon kuɗi irin wannan amma shi ne ta ba ta shi ta fice tana mita a ranta.

Shagon da ke gaban gidansu kaɗan ta je ta sayo katin, mai shagon yana ta tsokanarta da wasa kamar yadda suka saba, ranar ba ta kula shi ba sam hankalinta na can kan sahibinta da ya fara koya mata son shi.

Tana tafe tana loda katin don haka ko da ta iso soro ta gama sakawa ta tsaya nan ta lalubo numbersa ta danna masa kira. Kira biyu ta yi bai ɗaga ba, kamar za ta yi fushi sai wata zuciyar ta ce da ita. “Wataƙila yana banɗaki ne ko wani abu makamancin haka don haka ta sake gwadawa da manufar wannan ne kiran ƙarshe idan bai ɗaga ba sai dai ya biyo kiran.

Ringi biyu ana uku ya ɗaga “Assalamu alaikum, ina kwana Hayatie.”

Murya a sanyaye ya amsa mata da. “Lafiya qlau, ya kike?”

“To da sauƙi, amma ina zan yi lafiya ban jin ka ba kwana da yawa, Allah dai ya sa lafiya, na ga har zuwa ka daina yi ma.”

Muryarsa cike da ƙwarin gwuiwa ya ce “Lafiyata lau ka da ki ɗaga hankalinki, na daina zuwa ne kawai don ba amfanin zuwan a yanzu.” Duk irin taɓara ta Halisa da rashin mayar da hankali sai da ta fahimci akwai matsala don haka da damuwa a cikin muryarta take tambayarsa “Me ya faru Hayatie? Me ya sa ka faɗi hakan, na yi maka wani laifin ne?”

Girgiza kai ya yi tamkar tana kallon shi “Ko ɗaya Halisa, ba abin da kika yi mini yau ranar wanka ce ba a ɓoyon cibi zan sanar miki dalilin da ya sa na ɗauke ƙafata daga gare ki.”

Wannan karon ba ta iya yin magana ba tsabar kaɗuwa da jin sunan da ya kirawo ta da shi, sai shi ne ya ci gaba da faɗar “Maganar aure a tsakaninmu an janye ta…”

Ba ta ma san lokacin da ta furta. “Innalillahi wa inna ilahir raji’un! Wai me na yi?” 

“Ni dai ba abin da kika yi mini, hasalima har gobe da jibi ina sonki zan kuma ci gaba da sonki, iyayena ne ba su aminta da auren ba saboda sun zo unguwarku yin bincike kafin su ƙaraso gidanku kamar dai yadda shari’a ta tanada…” Ya ɗan tsagaita alamar abin da zai faɗa a gaba ya yi masa nauyi a kan harshe, ya dai daure ya ci gaba da faɗar “Duka shaidun da suka samu a kanki ba masu kyau ba ne.”

Sai kuma ya yi shiru ita ce ta yi ƙarfin hali cikin rawar murya mai nuni da kodayaushe za ta iya fashewa da kuka ta ce “Me aka ce musu a kaina? Don Allah kar ka ɓoye mini, yana da kyau na san kallon da ake yi mini a unguwa.”

“Wai ba ki da mutunci, ba ki da tarbiyya taɓararriya ce ke goyon kaka, kuma wai ba ki da… Afwan gaskiya ba zan iya faɗar wannan abun ba, ki bari ko ma miye idan halinsu ne watarana da kunnenki za ki ji sun faɗa, sai dai na yi takaicin jin cewa wai har da ƙanin babanki a cikin ‘yan zuga-zugi. Ni yanzu abu ɗaya zan faɗa miki shi ne ki yi haƙuri, har yanzu ke ƙaramar yarinya ce sosai kina da tarin dama a gaba, ina yi miki fatan alheri Allah ya ba ki miji nagari wanda ya fi ni.” Yana gama faɗa ya tsinke kiran.

Wasu zafafan hawaye suka zubo gangaro daga kwarmin idanu zuwa tudun kumatunta, ba don abin da Hayat ya yi mata ba ne sai dai abin da munafukan maƙota masu fuska biyu aikata a gare ta, ma fi ƙona mata rai ma a ce wai har da ƙanin babanta a ciki. To waye wannan a cikin tarin ‘yan’uwan mahaifin nata? Na cikin nan gidan ne ko na waje? 

A ranta ta ji cewa daɗin abin ma su ma sun haifa kuma duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba tasa ko zafi ba za ta yi ba. Ta shige ciki tana goge hawayenta tare da ƙeƙashe zuciyarta da tunanin za ta saka ido za kuma ta zaƙulo ko su waye munafukan musamman macijin sari ka noƙe da ke maƙale a gidan, duk sai ta yi musu rashin mutuncin da kansu ba zai ɗauka ba, sun taɓo gidan danger.

Ciki ta koma ranta cike da fusata mai gauraye da damuwa ta shiga ɗakin sharaf-sharaf. Ige ta yi saurin ɗagawa daga inda take zaune ta dube ta da tsoro a fuskarta. “Bi a hankali dai kar ki faɗo mini ki ƙarasa ni. Lafiyanki dai? Me ya faru haka kika shigo a fusace.”

Faɗawa ta yi gefen gadon ta fara fesawa kakarta abin da ya faru a tsakanin ta da Hayat tana cikin bayar da labarin ba ta san sa’in da kuka ya zo mata ba sai tsintar kanta ta yi ta fashe da shi. 

Lallashinta Ige ta shiga yi kafin ta ce “Ki kwantar da hankali, aure ne dai in sha Allahu za ki yi shi idan ba su yi wasa ba ma duk sai kin riga ‘ya’yansu, ai abun na Allah ne budurwa da jika matar aure babu.

 Sauƙin sha’anin ma ai maganar neman auren ba ta yaɗu ba tun da ba a faɗawa kowa ba. Kuma ma du-du-du shekarunki nawa ne? Har yanzu ba na jin kin cika sha shida. Da ma ko an yi neman ba zan aurar da ke yanzu ba sai kin gama sakandare.”

Kallon kakar ta yi “Ni haushina ma wai har da ɗaya daga cikin waɗanda nake yi wa kallon ubanni aka kitsa wannan makircin na rasa waye ne?”

Da yanayin fusata kaɗan a cikin muryar Ige ta ajiye furucinta “Ko ma waye lokaci zai tona shi nan ba da jimawa ba, munafunci ai dodo ne yakan ci mai shi. Na dai yi imani ba cikin ‘ya’yan cikina ba ne sai dai ‘yan’uba su kaɗai ne za su iya haka. Ki bar su ai ni dakalin majina ce a hau ni a zame na hau mutum na zauna daram.” 

ƁANGAREN FATIMA

Bayan Sati Uku

Ranar Alhamis 

Wannan ita ce ranar dinner party na auren abokin Musa wato Ammar, tun misalin ƙarfe biyar na yamma da ya dawo aiki ya wuto mata da ɗinkin ankonta ya miƙa mata ledar kayan. “Ga ankonki na anjima ki gwada ɗinkin, duk da ba na jin zai ƙi yin cif a jikinki tun da an ba shi measurement da rigarki, telan kuma ƙwararre ne ya san kan aikinsa.”

Karɓa ta yi hannu bib-biyu tana godiya duk da har cikin ranta ba ta son zuwa wajen dinner  ɗin tun da ta tabbatar wurin haɗakar maza da mata ne, sai dai ba ta so ya zarge ta da rashin yi masa biyayya shi ya sa ba ta masa musu ba.

Buɗe ledar ta yi ta ga an shirya ɗinkin cikin leda mai shara-shara wacce ake iya ganin komai da ke ciki a bayyane. Da alama kayan sun sha kwantacciyar guga ta zaro su a hankali ta ɗaga rigar ɗinkin ya yi matuƙar yin kyau ko a ido saboda ba a cika masa kwalliyar hauka ba. Doguwar riga ce  (straight gown)  mai breast coat, ta saman ciki an saka mata wasu igiyoyi sirara guda biyu, na gefen daman mai tsayi na hagu kuma ɗan gajere da alama a gefen hagun ake ɗaure su don ƙarawa rigar kyau. 

Ita dai a ido da ta ga rigar sai ta ga alamun kamar ko ta shige ta za ta sha matsuwa a ciki, duk da haka ba ta yi masa magana ba ta yi uwar ɗakanta domin ta gwada rigar shi kuma da ma tuni ya wuce ɗakinsa da alama a uzurce yake.

A jikin madubi ta tsaya tana ƙarewa doguwar rigar kallo, ta zauna tsam a jikinta kamar ma a nan aka ɗinka ta, har da ƙyar take numfashi saboda kamatan da ta yi ta ko’ina surar jikinta ta bayyana. Don kyau fa suturar ta yi mata kyau fiye da tsammani tamkar don ita aka buga atamfar, maroon ce a kala sai ratsin fari da aka yi kewayayyen zane ƙarami da shi, ga dai sutura har sutura a ido amma ba ta suturtawa a aikace.

“Mtsw! Wannan wane irin jahilin ɗinki ne?” Ta furta a hankali ‘Lallai da sake an ba wa mai kaza kai.’ Ta faɗi hakan a ranta tana wucewa zuwa ɗakinsa kanta ba ɗankwali rai a jagule  ko sallama ba ta yi ba ta fara magana “Yaya ka ga yadda wannan telan ya ɓata atamfar nan?”

Ɗago da fuskarsa ya yi ya sauke kyawawan idanunsa a kan tufafin jikinta cike da fara’a “Wow! Fatabarakal lahu ahasanal ƙhaliqin. Kin yi matuƙar kyau fa sweetheart.”

Wani irin kallo ta yi masa kafin ta matso kusa da shi da sanyin murya ta furta “Ka ma fahimci me nake cewa kuwa? Yanzu kai hakan ya yi maka na fita da wannan rigar?”

Washe haƙora ya yi fara’a ta gama mamaye fuskarsa ya ce “To meye matsalar? Ai ni na zaɓi style ɗin da kaina kin san sabgar nan ta wayayyi ce kowa zai so a ga matarsa acan-acan.” Yanzu kam ta lura shi ba ya hango girman kuskuren da ke cikin aikata hakan. Sai kawai ta juya ta fara buɗar ƙofa tana faɗar

 “Gaskiya to matarka  ba za ta iya fita da wannan kayan ba kunya take ji. Kawai zan saka wani mai kyaun a cikin waɗanda nake da su.” Ya dakata da tattara sauran kayan da yake zubawa cikin jakar rataya ya zuba mata kamar mai nazartar fuskarta kafin yanayin fuskarsa ya sauya zuwa na takaici kaɗan ya girgiza kai.

“A’a gaskiya ban yarda ba, ba za ki ɓata mana tsari ba. Wannan kalar kayan da ke jikinki shi ne ankon da duka matan abokanmu za su saka. Dubu ashirin ne farashin atamfar ban da na ɗinkin da kika raina da shi ma ya ci kuɗi, hakan nan ban saka miki da lissafin waɗan can fararen takalmi da jaka da mayafi ba dukansu so kike su tashi a banza a dinga mini kallon gazawa da gidana duk da Allah ya rufa mini asiri?” 

Yana kashe doguwar saƙar zaren zancensa ya goya jakar tashi har a lokacin ba ta iya yin magana ba sai bin sa da ido da take yi, shi ne ya sake cewa “Ni yanzu zan tafi, a can hotel ɗin da muka kama za mu yi shirin. Ba zan dawo ba sai an gama dinner. Su Hanifah za su biyo su ɗauke ki a motar Faruk sai ku same mu a can event center ɗin.”

Sauke ajiyar numfashi ta yi tana faɗar “To Allah ya kiyaye hanya, sai mun zo.”

Gaba ya yi ta biyo sawun shi sai dai shi ficewa ya yi daga gidan gaba ɗaya cike da takaicin hali irin na matarsa da yadda kunyarta take ci masa tuwo a ƙwarya.

 Ita kuwa nata ɗakin ta koma ta cire kayan ta linke sosai ta tattara sauran kayan da za ta haɗa wurin tada adon ta ajiye gu ɗaya ta fita waje ta ci gaba da sauran aikace-aikacen gidan da suka rage mata.

Da misalin ƙarfe 8:30 na dare ta jiyo sallamar mata a ƙofar falonta da farincikinta ta fito ta rungume Hanifah da Sadiƙa matar Salim tana yi musu sannu da zuwa ta ja su zuwa cikin ɗakin sauran mata biyun da suke tare da su suka bi bayansu.

A falon suka zaz-zauna suna ƙara gaisawa ta ce “Bari na kawo muku ruwa.” 

Salimah ta yi hanzarin cewa “Da kin bar ruwan ma, mu da muka baro gida yanzu? Je dai ki ƙarasa shiryawa ki zo mu tafi dare na ƙara yi.”

Ta faɗi hakan ne ganin ko da suka shigo ita ma Fatiman ta riga ta saka tufafi da ‘yankunne har da agogon hannunta, takalmi kawai ya rage mata da jaka sai ɗaurin ɗankwali.

Ta ce “Afwan, bari na hanzarta, zafi ne ya hana ni murza ɗaurin.”

Ba ta ɓata musu lokaci ba don ko minti goma ba ta ci ba ta fito tana ɗaukar ido, duk da ita ba farar fata ba ce amma adon ya narke a jikinta har ya fi karɓarta a kan wasu daga cikin matan da suka kasance farare a kalar fata.

Kamar yadda mazajensu suka tsara haka aka yi, don ko da suka ƙarasa cikin compound na event center ɗin ma ba su shiga hall ɗin ba a waje suka tsaya, kowacce ta kira mijinta ta shaida masa daga nan suka watse dukansu kowa ta je motar mijinta suka zauna suna hira kafin ƙarasowar amarya da ango. 

Bayan minti talatin masu gayyar suka ƙaraso. Da ma sun riga sun yi nasu tsarin dabam da yadda aka saba a sauran gama-garin tarukan biki, shi ne aka naɗa Faruk jagoranci ya je ya sanar da M.c  yadda tsarin yake. 

Sai a lokacin Musa da sauran ‘yan tawargu su biyar har Faruk cikon na shida kenan suka fito cikin shiga iri ɗaya. Ɗanyar farar shadda gizner suka sha ta ji aikin na’ura mara hayaniya, suka kafa baƙar hula a kai, sai baƙaƙen takalmi  sawu-ciki da agogo baƙi. 

Ango ya tsaya a gaba su kuma suka laya a bayansa kowanne yana gefen matarsa. Muryar M.c ta karkaɗe ɗakin taron da kewaye cikin taimakawar manyan sifikun da ke ajiye a gefe cikin ɗakin taron.

“Yanzu lokaci ne da za mu yi maraba da ango cikin rakiyar abokansa da matansu. Magana ake ta manyan yara ‘yan jami’a eh mana!. Dangin ango sai ku shirya domin yin kara ga wannan ɗan gatan angon. D.j idan ka shirya ka sako mana waƙar soyayya mai ratsa zuciya.”

Cikin ‘yan daƙiƙu kuwa d.j ya kunno waƙar soyayya ta Umar M Sharif mai tattausan kiɗa a hankali ango ya fara takawa zuwa cikin hall ɗin abokanansa na take masa baya, kowannensu sai ya riƙe hannun matarsa suna ɗan takawa a hankali.

Musa da Fatinsa ne a tsakiya ko da ya miƙa mata hannu don kamawa sai ya ga ta noƙe bai jira komai ba ya janyo hannun nata ya riƙe gagam suka fara shiga hall ɗin cikin takun burgewa, ga hasken gulof kala-kala duk wurin ya mamaye da haske tanyar kamar safiya.

Mahalarta taron a ƙiyasi za su yi mutum ɗari da hamsin da ɗoriya, ciki kuwa har da dattijai duk sai ta ji ta tsargu. Ita fa wannan rashin kunya ne a wurinta, yana ji tana ta ƙoƙarin ƙwace hannunta amma ya riƙe ƙam-ƙam gudun kada ta kunyata shi a tsakiyar dandazon al’umma ga kuma masu vedio covering suna ta faman ɗauka abin ya burge kowa da ke gun. A tunaninsu wannan tsarin shi ne irinsa na farko a gun bikin aure domin su suka ƙirƙiri kayansu ba kwaikwayo suka yi ba.

Daga ƙarshe da ta ga ba zai sake ta ba ta yi shahadar ƙuda ta rufe ido kawai ta ci gaba da bin shi tana ji kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki ta ɓuya. Yana lura da yanayinta ya basar har sai da suka raka ango mazauninsa suka watse zuwa mazaunin da aka tanada musamman domin su.

Ragowar tuzurai da samarin angon su ne suka shigo tare da ‘yanmatan amarya yayin da suka sako amaryar a gaba suna rawa har suka sada ta da mazauninta.

Haka dinner ta ci gaba da gudana an ci an sha an gyatse bayan dawowa daga hutun ciye-ciye aka ƙara ba wa abokanan ango dama su nunawa amarya da ango zallar farincikinsu a wannan ranar mai ɗimbin tarihi a gare su. 

Duka ‘yan tawagar suka miƙe daga mazauninsu a tare suna miƙawa matayensu hannu alamar su ɗora nasu a kai. Sai dai shi Musa ko da ya aikata kamar yadda sauran suka yi sai matarsa ta noƙe tana kallon gefe da gefenta ta ga duk idanun mutane ya dawo kansu. Takaici ya kama shi ya ƙara sunkuyowa ya kama hannunta ɗaya ya ɗora a nasa yana kafe ta da idanunsa da suka ƙara fitowa waje wanda hakan ke alamta mata yana dab da arar ɗabi’ar kwaɗo yayin da ya cika da fushi, gudun kar ya fashe ya saka ta miƙe don ta fuskanci takaicinsa ƙarara.

 Sai dai fa ita ba za ta iya jure aikata wannan duniyancin ba a bainar nasi, a iya su biyu kaɗai ma da yaya ta koyi iya cire kunyarsa a ranta ballantana a idon duniya?

Ɗan rungumo ta ya yi kaɗan ya daidaita kafaɗarsa da tata sannan ya cire hannayensa daga kafaɗar ya mayar da su kan tafin hannunta na dama ya riƙe shi da kyau suka fara takawa. 

Duk da cewa jikinta a sanyaye  take tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki  haka ta ci gaba da bin shi a ranta kuwa tana girmama girman rashin kunyarsa sai dai hakan bai hana ta yunƙurin taɓuka wani abu ba. 

Tana ganin ya shagala da kallon saman dandamalin amarya da ango ta ƙwace hannunta daga riƙon da ya yi mata ta matsa can gefe sosai yadda jikinsu ba zai ci gaba da gogar juna ba. Ya waigo ya kalle ta ya kalli hagu da damar hall ɗin ya lura idanu da yawa na kansu. Ransa ya yi ƙololuwar ɓaci idanunsa suka fara kaɗawa zuwa launin ja. Ta riga da ta gama zubar masa da mutuncin da yake tattalawa don ya ga Salim yana ƙume dariyarsa wanda hakan ya ba shi tabbacin idanunsa sun faɗa kan abin da ke faruwa da su. A haka dai ya daure ya ƙarasa gurin liƙin ba walwala ya yi wa amarya da ango liƙin ɗari bib-biyu, sai dai ita Fatin tasa ko ƙwandala bai saka mata ba tsabar haushi da ta ba shi.

Mc ne ya ƙara yin magana cikin salo irin nasu “To abokanan ango muna godiya, tabbas kun nuna kuna cikin farinciki a wannan rana, yanzu za ku koma mazauninku don ba wa saura dama.”

Duka suka juya zuwa table ɗinsu sai dai shi a maimakon hakan sai ya ja hannun matarsa yana tafiya da sauri-sauri yana nufar waje, suna barin wurin idanun jama’a ya fara jan ta da ƙarfi kamar zai fincike mata hannun tana ɗan ihu kaɗan bai damu ba har sai da ya isa inda yake muradi, ya buɗe motarsa ya watsa ta a baya ya saka lock ya koma ciki yana ƙoƙarin arawa kansa nutsuwa tare da samar mata mazauni a jikinsa.

UMMU INTISAR CE

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here