Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 11

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 11

17
0

NA

Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)

PP 11

“So nake ki ba ni dama mu daidaita don Allah! Kin san dai ina matuƙar ƙaunarki ƙaddara ce ta raba mu. Ƙaddara kuma a kodayaushe ita take yi wa fata zagi, amma ki yarda da ni wallahi ba na jin ko wacce ‘ya mace a raina kamar yadda nake jinki. Ina ji a jikina ke alherina ce, ki ƙara tunawa da tsohuwar zuma ake magani.” ya yi zancen da yanayin da ke tabbatar da gaskiyar abin da ke ransa yake furtawa.

Wannan karon dogon tsaki ta ja tana ‘yar dariyar rainin hankali “Amir kake ko wa? Don Allah ka bar ni haka in huta, ko kuwa ka dawo ne ka fama raunin zuciyar da ka yi mini ya fara warkewa don ka raunata rayuwata? To ban shirya fuskantar uƙubar gidan aurenka ba, ba zan ba ka dama ka cika munanan alƙawurranka a kaina ba. Kuma da kake maganar cewa da tsohuwar zuma ake magani, ka manta cewa idan ta yi wata jimawar tana sauya ɗanɗano? Ko ka manta cewa sabuwar ma tana magani? Tsaya ma tukunna ba kai da bakinka ka ce ka fasa auren ba?”

Ya sosa ƙeya murya a ƙasa yake faɗar “Eh na faɗa but i don’t mean it, ban ma san me ya shiga kaina ba a lokacin na faɗa wallahi na yi nadamar furta wannan furuci ke ma kin san….” Ba ta jira ya ƙarasa ba ta ja wani kakkauran tsaki ta katse wayar a fusace tana sababi.

“Rainin hankalin banza. In ban da ma ka raina ni har ni za ka tara da maganar mayar da zancen aurenmu? Ina! Never wallahi. Ai duk yadda na matsu da son yin aure don fita wannan jarabawar garan mini na rayu cikinta har ƙarshen rayuwata da na yarda na saka ƙafata a tarko alhali ina sani.” Gyara filonta ta yi ta yi kwanciyar ta.

Kiran shi ne ya sake shigowa a karo na biyu sai dai ko a jikinta sai ma kifar da wayar ta yi a gefen filonta don tabbatar da ba za ta ɗauka ba, haka ya yi ta kira amma ba ta niyyar ɗauka sai tsaki take maimaita ja tamkar jaɓa.

Kwanciyar ta kedawuya ta faɗa tunanin baya a lokutan da suke tsaka da zamantakewar soyayya a wata ranar juma’a da dare washegarin ranar ƙaramar sallah ta 2018 da ya yi convincing ɗinta suka fita outing da misalin ƙarfe 7:30 na dare. Ta caɓa adonta cikin purple Egyptian abaya mai matuƙar kyau wadda ta ji saƙar inji ta farin zare aka cika adon stones masu  bada kaloli a cikin saƙar sai ta yi rolling mayafin abayar wanda ba shi da girma sosai, ta saka veil pin purple ta yi ‘yar kwalliya kaɗan, amma ba ta yi jagira ba iya powder, kwalli da jan baki ta saka. Sai ga ta ta fito tamkar ‘yar tsana sai baza ƙamshi take.

Adon nata ya ƙara fito da kyawunta na ‘ya’yan fulanin asali, kyakkyawar farar fuskarta mai ɗauke da matsakaitan idanu da dogon hanci tare da ƙaramin baki da laɓɓa marasa kauri sosai ta yi fayau da ita. Doguwa ce ba irin tsawon nan na zarta iyaka ba, siririya ce ba kuma cancan ba shi ya sa masu kiranta da sunan kyakkyawa ba su taɓa faɗa don zolaya ba sai dai don iya gaskiyar kenan.

Fararen sneakers ta saka sannan ta fito waje don yi wa mama sallama. Maman ta san da fitar tasu amma ganin cewa shi ne wanda aka yi musu baiko zai aure ta ba ta ɗaga hankalinta a kai ba ta bar ta suka fita don ta yarda da tarbiyyarsa da kuma hankalin ‘yarta.

A Valentino ice cream suka fara tsayawa domin sayan kayan maƙulashe masu sauƙi sannan suka wuce Majeed Garden & Park  ya biya kuɗin suka shiga. Ga masoya nan kala-kala da iyalai kowa yana abin da ya kawo shi.

 Can ɓangaren wani ƙayataccen lambu ya nufa da ita inda ba hayaniya sosai suka zauna ya shimfiɗa musu dardumar mai faɗi da ya ɗauko a cikin babur ɗinsa a kan grass carpet mai laushi da ya mamaye gun. A hankali ya fara buɗe ledojin da suka shigo da su yana fitar da desserts ɗin da suka zo da su, strawberry cake, chocolate cake, sponge cake, yogurt da ice cream kala biyu vanilla and chocolate duka ya baza su a tsakiyar su. Ba ta yi magana ba sai kallon shi take, ya fara buɗe mata robar vanilla ice cream da ta zaɓa ya miƙa mata shi kuma ya fara shan nasa da ƙaramin cokalin robar.

Ba yadda bai yi ba ta saki jiki ta ci sauran kayan ba amma sam ta kasa sakewa ita ba ta saba da irin wannan duniyancin ba, sai shi ne ya yi ta ciye-ciyen abubuwan da ya sayowa kansa nata kuwa ya mayar a leda yana ci suna taɓa hira jefi-jefi.

Ba zato ba tsammani ta ji saukar hannunsa a kan nata yana shafawa. Da hanzari ta fisge hannunta tana ɗagowa a ɗimauce ta kalle shi. Ba ta iya yin magana ba sai kallon tuhuma da take watsa masa tana ƙara ja da baya. 

Sai shi ne ya yi ƙarfin halin fara magana da raunanniyar murya “Kina ji baby kada ki ɗaga hankalinki, wallahi kyaunki ne ya ruɗe ni shauƙi ya sa na aikata hakan. Kuma ma miye a ciki? Ai ni ne wanda zan aure ki kin ga ai ba wata matsala.”

Fara girgiza kai ta yi tana yi masa kallon dodo firgici ya daɗa bayyana a fuskarta ta tattara jakarta ta janyo takalminta ta saka ta miƙe ta fara nufar hanyar fita wajen garden ɗin. Hankali a tashe ya miƙe ya bi bayanta, taku uku zuwa huɗu ya yi ya cafko hannunta ta baya, wannan karon da rawar murya yake magana “Don Allah baby ki..ki.. ki saurare ni, wallahi ba abin da kike tsammani ba ne, kin dai san ni ɗin mutumin kirki ne mai addini.”

Kafin ma ya gama zancensa tuni ta sake fisge hannunta ta yi baya da ƙarfi tana faɗar “Subhanallahi! Sam wannan ba Amir ɗina ba ne, ban san ko kai waye ba amma don Allah kada ka sake kwatanta mini abin da ka aikata yanzu.” Ta haɗa hannuwanta alamar roƙo sannan ta juya zuciya cike da tsoro haɗe da fusata ta ci gaba da nufar hanyar fita.

Bai ji bari ba ya biyo bayanta yana faɗar “Don Allah baby ko ba za ki saurare ni ba ki yi mini allfarmar na maida ki gida ko don su mama kada su zargi wani wani abu, don Allah ki binne wannan sirrin a tsakaninmu.”

Ba ta ce da shi komai ba ya dai ga ta tsaya cak alamar ta amshi roƙon shi don haka jiki na rawa ya juya ya je ya tattare sauran kayan da suka zo da su wuri ɗaya yana kwashe shimfiɗarsa ya same ta suka ƙarasa wurin babur ɗinsa ta hau fuska a haɗe ya tada suka fara tafiya.

 Da ita da shi ba wanda ya ce da wani ci kanka kowa da bikin zuciyarsa, shi yana ta fama da tunanin ya zai gyara kuskuren shi ita kuma tana fama da tunanin ‘Da ma haka Amir ɗin yake? Ashe kura ce lulluɓe da fatar akuya? Me ya sa wasu ustazan suke laɓewa cikin rigar addini suna aikata masha’a?’

Tafiyar minti talatin suka sharara amma har suka ƙarasa ƙofar gidansu ba wanda ya yi magana. Za ta shige ciki kenan ya yi saurin cewa “Don Allah Surayyah ki saurare ko da na minti biyu ne don soyayyarki da manzon Allah.”

Waɗannan kalaman da ya yi amfani da su wurin roƙonta da su ya ɗaure mata jijiyoyin jikinta tamau har ya saka ta ji a ranta dole za ta saurare shin. Sai dai uffan ba ta ce ba ta dai tsaya kiƙam a kansa ta ba shi baya irin ka yi magana da ƙeya ɗin nan.

Duk da hakan ya ji daɗin samun nasarar da ya yi sai ya fara ƙoƙarin yin amfani da duk wasu hikimominsa da zalaƙar harshe da yake da ita don ciyo kanta. “Kina ji baby wannan abu ya faru ne bisa ga tsautsayi. Ƙaddara ce ni da ke duka ba za mu iya kauce mata ba. Don Allah ki bar wannan abu ya zama sirri a tsakanin tsokar zuciyarki da ranki. In sha Allahu abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Yanzu ga wannan ki yi mini alfarmar shiga da shi ciki.” Ya ƙarashe zancen yana miƙo mata ledar kayan ciye-ciyen nasu da ya tattaro.

Ba ta ma juyo ba ballantana ta ga me yake miƙo matan kawai ta yi shigewarta gida don haka ba ta san ya ya ƙare ba.

Sai da ta tsaya a soro ta gayyato  nutsuwa ta yi mata mazauni a cikin jikinta sannan ta shige cikin gidan da sallamarta. Mama kaɗai ta tarar ta baza tabarma a tsakar gidan don A’ishatu ta riga ta wuce wurin kwana, ita ma ta shigo ne don ta shiryawa ta wuce saboda tara na dare ta riga ta gota. “Kun dawo? Yana gan ki a haka jiki ba karsashi?.”

Ɗan sosa kai ta yi tana ‘yar dariyar yaƙe “Eh wallahi mama, da ke ma inda muka je da ɗan nisa shi ya sa. Ba fa komai lafiyata qlau.”

Suna cikin zancen ba ta san yanda aka fara ba ta ji sallamar yaro ya shigo gidan hannunsa riƙe da fararen ledoji guda biyu ya ce “Wai ga shi in ji Amir a ba wa Surayyah.” Har ta yi suɓul da bakan cewa “Mayar masa ka ce ba a so…” Sai kuma ta yi shiru ganin mama na yi mata kallon tuhuma, yaron zai juya kenan maman ta ce “Miƙo mini nan, ka je ka ce masa an gode.”

Ta mayar da dubanta a kan ‘yarta “Me ya faru ne kika ce a mayar ko wani mummunan abun ya miki?” Ta tambaya tana tsare ta da ido.

Dawurwura ta fara “Ba… Ba fa komai mamanmu. Kawai ya ɗan ɓata mini rai ne.” Ta waske da zancen,  maman ta ba ta haƙuri a kan cewa ta ci gaba da haƙuri duka duniyar ma ‘yar haƙuri ce idan ba ka da shi ba za ka rayu cikinta da daɗi ba.

Daidai nan zaren tunaninta ya katse ta dawo duniyar zahiri tana sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi. Ta sani cewa tabbas tana buƙatar aure a wannan matakin da take fuskantar matsin lamba da tambayoyi marasa amfani daga mutane da suke yi mata a kan aure, amma kuma wannan ba shi ne dalilin da zai saka ta yi wa kanta ingiza mai kantu ruwa ba ta hanyar auren wanda ya yi mata alƙawurran tozarci, halaka da matsin lamba a rayuwar aurensu, duk da dai daga baya ya yi togaciya. Lallai tana buƙatar yin dogon nazari domin zaɓen madogara ɗaya da za ta ba ta salama a rayuwa. Ita ce take ta fama da wannan zancen a zuciyarta.

ƁANGAREN HALISA

Ba komai ne ya so ba shi dariya ba sai ganin maiƙo a gefen bakinta nashe-nashe maiƙon ya zagaye gefen bakinta ga powder a ko’ina ta shafu amma a gun babu da alama bayan ta yi kwalliyar ne ya taɓa gun, a kan leɓenta kuwa maiƙon ya saje da rabin janbakin da ke damɓare a laɓɓanta. Da ya yo ƙasa da dubansa kuma sai ya ƙara ganin shi a hannunta na dama hakan ya ba shi tabbacin ta ci wani abu bayan ta kammala shiri.

A hikimance ya kalle ta yana faɗar “Kai! Kin yi matuƙar yin kyau baby…” Sai ya ɗan sauya fuskarsa zuwa na yanayin mamaki kaɗan ya sake cewa “Lah! Baby meye a gefen bakinki na ga kamar maiƙo-maiƙo ko dai wani abun ne ya watsar miki a gun ba ki lura ba?” Ya yi mata hakan ne saboda sanin jaraba irin ta ƙwailaye, da ya yi mata maganar ƙeƙe da ƙeƙe za ta iya hawa kansa da tsiwa har ya rasa damar yin hirar da ita idan bai yi sa’a ba.

Hannu ta kai ta shafa gun ta dawo da hannun saitin fuskarta sai a lokacin ta ga kalar kwafsawar da ta yi, sauri ne ya hana ta tsaida hankali har ta tuna ba ta goge hannu da bakin ba.

Da ‘yar dariya kaɗan ta ce “La, la, la! Ashe fa wai ban goge ba, yi haƙuri ina ujila ne kasan an ce da zafi-zafi ake dukan ƙarfe to daga makaranta na dawo ina jin yunwa shi ne dai…”

Tana zancen tana ɗan kakkamewa wai kar ya fuskanci kamar ta tsargu ya yi mata dariya. Tun daga amsar da ta ba shi bai ƙara ce mata komai game da wannan ba ya shiga yin abin da ya kawo shi. Bayan sun gama hirar ne ya ce ta jira shi ya je mota ya ɗauko kwalin ƙaramar waya ya miƙa mata, da rawar ƙafa ta karɓe tana godiya. Shi kuma ya ba ta ne don ya samu sauƙin zaryar zuwa wurinta don har ga Allah yana ƙaunarta kuma yana da burin aurenta, nan bada jimawa ba yake son ya kai maganar gaban iyayensa amma yana son ya fara samun hankalinta da nutsuwarta kafin yin hakan, don ya lura giyar ƙuruciya tana ɗawainiya da ita, she is not matured enough.

Yana tafiya ta shiga gidan tana tsalle-tsallen murna ta nunawa kakar abin da ya ba ta. Kakar ta so ta hana ta riƙe wayar amma kuma sam ba ta son ɓacin ran jikar tata don haka ba ta yi yunƙurin hanawa ba sai ce mata ta yi “Allah ya sanya alheri ya tsare, amma don Allah ‘yar cakwai ki yi taka-tsantsan da wayar nan ta zamani, ni dai wallahi tsoron lamarinta nake.”

“Kar ki damu ‘yar tsohuwa in sha Allahu ba abin da zai faru sai alheri, waya kawai za mu dinga yi da shi.” Zama ta yi ta janyo kulolin ta tarar da su kamar yanda ta bar su don har a lokacin Ige ba ta ma taɓa ba, ta san cewa tana jiranta ne ta zo ta ɗibi mai isar ta kafin ita ta ci. Ganin haka sai ta yi adalci ta fara sakawa mata a faranti sannan ita ma ta ɗiba cikin ragowar ta fara ci don kuwa tana jin azababbiyar yunwa.

 Da ta kammala ne kakar ta yi mata maganar zuwa islamiyya ita kuwa ta miƙe don yo arwala. “Gaskiya yau ba za ni ba saboda ina fama da tsamin jiki, faɗuwa fa na yi a makaranta gardawa majiya ƙarfi suka yi ƙuli-ƙulin Kubura da ni a ƙasa. Shi ma Hayat ɗin na saurare shi ne saboda ya zo daga nesa. Wulaƙanci ba daɗi kin kuwa ji an ce duk mai wulaƙanta jama’a ya ga iyakarsa.”

Haɓa ige ta kama tana faɗar “To ai shi kenan, Allah ya sauwaƙe, amma su can makarantar ba za su hukunta ki gobe ba saboda rashin zuwa?”

“Zan je na ce da Sa’adatu ta shigar da uzurina na rashin lafiya, na san idan na yi hakan in sha Allahu ba ƙaton malamin da zai hukunta ni.” Daga wannan ba ta ƙara ce da tsohuwar komai ba ta tada sallah, ita kuma ta ja baki ta tsuke ta kawo na gani ta zuba mata. Bayan ta idar ta haye gadonta ta yi kwanciyarta nan take bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita.

Bayan kamar wata biyu ta ji shiru fin sati biyu bai kira ba bai kuma zo ba, iyayensa ma da ya ce zai turo da su tun watan da ya gabata su ma shiru kake ji kamar an shuka dusa. Da fari kafin ya daina amsa wayarta ta tambayi dalilin rashin zuwan magabatan nasa amma fa ba wata ƙwaƙƙwarar amsa  abar dogara sai ce mata da ya yi, za su zo shi ne ya dakatar da su akwai ɗan abin da yake jira kafin nan.

 A lokacin ba ta damu ba ba ta kuma kawo komi a ranta ba, sai dai a hankali ta ga yana ja baya da alaƙarsu. Idan da zai kira ta sau goma a wuni sai ya dawo da ƙyar yake iya kira biyu nan ma tana jin yanayin karaya a cikin muryarsa. Daga baya ma sai ya zamana kwata-kwata ya daina ɓatar daga kuɗin katinsa a kanta. 

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here